← Book details Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 22

Sashe 4

Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuwa, na sake zuba mishi ido ina kallonshi na ce mishi saboda me zaka yi hakan? Saboda baka jin kunya? Saboda baka jin tausayi? Saboda ba ka damu ba kai kayi ta taimako ana yin cuta? Ko kuwa saboda me? Cikin natsuwar shi ya sake cewa, saboda ni namiji ne, na sake tambayarshi saboda kai namiji? Ya ce min eh, na ce mishi to babu laifi to amma zan aike ka wurin waxanda suke saka kana yi, waxanda suka turo ka kazo ka aureni, don ku qara cutarmu saboda duk abinda ku ka haxu kuka yi mana ni da uwata bai ishe ku ba. Ka gaya musu ni na ce wannan karon ba za ku yi nasara ba, don ba zan qyale ku ku sake sanya uwata cikin wani vacin ran ba. Don haka in har zaka ji shawarar da zan baka to kayi maza ka ce musu ka fasa ba kaso, don kar suyi dalilin faxawar ka cikin wawakeken ramin da ba za su iya fiddo ka ba. A hankali ya ce min, babu komai don an yi hakan na ce to shi kenan, na juya zan shiga gida, ya ce to tsaya ai da sauran bayani, na ja na tsaya ina kallon shi menene bayanin? Kuxi ya ciro ya miqo min dunbus a hannunshi ya miqo min tare da faxin kuxin taxi zan baki. Sai da na kalle shi na kalli kuxin sannan na sake kallonshi na ce mishi ai baka da su, baka da ko kwabon da zaka bani in karva, don duk wani abin da kake dashi kake barazana ka ke wani menene? Na ubana ne, sannan ina so in sanar da kai don nasan komai hatta asara-asarar da kake cewa an yi da kuxin kujerar Innata da aka baka kaje ka biya mata kujerar Hajji kaje ka dawo ka ce kayi sujada an xauke kuxin sai daga baya kai da Mama kuka ce kun je qauye kun sayar da gonakinku na gado ku ka sai gida. Nasan komai.” Ya ce to ai yayi kyau gara da ki ka san komai, ungo kawai ki karva in baso kike kiyi na kenta ba, na ce ai babu komai tunda yanzu dai ka mako na karvi kuxin hannun ka wanke kifi aka yi da ruwan jikinshi cikin dukiyar ubana ka ke fantamawa don haka riqe ka qara ci, na wuce shi nayi tafiyata. Tunda Ado ya kira ni na amsa kiranshi sau xaya ban sake ba, ko a hanya muka gamu wucewa kawai yake yi nima in wuce. Muna cikin haka muka wayi gari Anti Sha’awa da ‘ya’yanta guda uku sun kwana a gida ga dukkan alamu kuma ba lafiya ba ne, yaji ta yiwo don ina jin Mama tana yiwa Babana bayanin dalilin yajin nata, tana faxin wai ka ji min xan iskan mutumin nan mara mutunci Alhaji, Zubaida tana daga kicin ta ce assha surukinne kuma xan iska? Ban kulata ba don har yanzu bana shiga harkarta, gaisuwar safe ce kawai take haxa ni da ita daga nan babu qari, na dai lura kawai na gane ita da Mama sun xan yi tsami sai dai ban san dalilin tsamin nasu ba, kawar da kunnuwana nayi daga sauraron Zubaida na maida su wajen Mama da Babana. Wai ashe aure yake nema ka ji xan iska, ko yaushe ya gama ciyar da na gidan? Oho!. Babana ya xan yi maganar da ban ji ba sia na ji Mama ta soma cewa, ina Alhaji? Ai ma ba zai yiwu ba kar ma ka fara sai ka ce wata mara gata? Ai sai ya zo nan shi da kanshi sai mu ji dalilin qara auren nashi, menene ba a mishi ta ina aka gajiya mishi? Ko kuma dai neman fitina? Ba’a gama kada wata ba ana cewa wata ma ta tuve, ai zamu gamu ni dashi zai gane karon babu daxi in don yaga ina yi mishi lako-lako ne. Haka Babana ya haqura ya qyale Anti Sha’awa a cikin gidan nan yana kallonta ita da ‘ya’yanta har tsaraba yake kawo musu bai kawowa nashi ‘ya’yan ba, tana yiwa kowa kallon uku kwabo sai tayi ta habaici tana faxin maganganu kan aurena da Ado, wai daga rufa mana asiri da aka yi amma muna wani iya shege in ban da Mama ma ai Kawu Ado ba mijina ba ne, don yafi qarfina kamar in ce to aba shi daidai dashi mana nima abar ni da daidai ni sai Inna ta ce min kul, ja bakinki kiyi shiru na ce mata to. Kwanan Anti Sha’awa uku a gida mijinta bai zo ba, bai yi aike ba, hankalinsu gaba xaya ya soma tashi don sun saba in ta yiwo yaji ya yi ta zirga-zirga safe da yamma yana kawo hasafi ana wulaqantawa ana tambayarshi baka bayar a gida ba sai da aka zo nan? Ai ya zama aikin banza. Shi kuma ya yi ta bada haquri yana rantsuwar babu ne amma in akwai ai babu wanda zai fi maigida son ya yi wa iyalinshi alheri. Mama tana faxin ba dai kai ba kam don kai kam ba mai alherin ba ne. Rannan da yamma sai ga Baba Yahaya yazo gidan, sallama xaya ya yi ya shigo cikin gidan bai jira sai an amsa mishi ba yana riqe da wani qunshi na tsohon buhu a hannunshi na fito daga kicin da sauri don in karvi buhun a hannunshi, sai kawai naga Innar Giyaxe tana biye dashi tukuf-tukuf. Tsalle na buga na kuma kurma ihu da qarfina kafin na kankameta ina faxin “Kai ku firfito ga Hajiyar Giyaxe tazo.” Da gudu aka yi ta firfitowa yi mata oyoyo, ni kuma Baba Yahaya ya tsare ni da ido yana yi min daquwa hannu bibiyu don Atika ta riga ta karve buhun da ke hannun nashi. Kaga min ja’irar yarinya kina hauka ne ko kuwa qara sa mana ita za ki yi? Na sake ta cikin sauri a hankali cikinladabi na ce mishi Baba kayi haquri. Na kama tafin hannunta na riqe tana qoqarin qwacewa qyale ni ni kar ki matse ni, na ce haba Hajiyata ai tamu da ke bata vaci, har xakin Mama na kaita don nasan can ne masaukin nata a can muka tattaru gaba xayanmu muna ta hargowar yi mata oyoyo rabonta da gidan anyi matuqar daxewa. Mama ta shiga hidimar yi mata hidima sai ina aka saka da ita take yi, itama dai nasan ta gane Baba Yahaya ne yaje ya xaukota ba kuma kan komai ba sai kan maganar aurena da Ado. Rannan ni da Inna muka kwana muna murna tunda ga Hajiyar Giyaxe tazo ai kuma zance ya qare ana baiyana mata komai zata hana auren. Rannan kwananta biyu a gidan tasha farfesu ta kuma wastsake gajiyar girma, idanuwanta sun buxe sosai ta soma gane kan gidan da kyau, ina cikin wanke-wanke na ji ta tana tambayar Babana ni wannan yarinyar Sha’awa me take yi ne a gidan nan? Ya xan yi ‘yan wasu maganganu da ita da kanta na ji tana cewa, ban fa ji ba to balle kuma ni da nake nesa. Sai ga Baba Yahaya yana sallama ta amsa mishi tare da yi mishi sannu da zuwa, sai albarka take ta sanya mishi tare da tambayarshi iyalin sun je gida lafiya ya ce mata lafiya qalau sun ce a gaishe ta, ta ce to tana amsawa, Allah dai yayi musu albarka ya kuma amfana su, Babana ya ce amin. Sai da aka xan yi hira sosai sannan Baba Yahya ya gyara zama ya ce mata, to Inna ko da naje na xauko ki akan ki zo kiyi mana baqunta saboda kin daxe ba ki zo mana ba, to ba baquntar kaxai ba ce tasa na xauko kin, tayi maza ta gyaxa kai tare da mamula bakinta ta ce, nayi zaton hakan nayi zaton da wani abu wataqila tsakaninka da xan uwan naka ko kuma tsakaninshi da iyalin shi. Baba Yahaya ya sake gyara zama kafin ya ce mata kan maganar auren Humaira ne, Hajiyar giyaxe ta ce Humaira, Humaira ya ce mata Aisha, ta ce af to, tayi shiru tana sauraronshi ya gama rattaba mata ba yanin komai sai dai ya yi qoqarin cire sunan Mama a ciki wataqila don yasan ba wani son Mama take yi ba, wataqila kuma bai son nuna mata gajiyawar xanta kan riqon gidan shi. Sai da ta gama sauraronshi tsaf yayin da ni da Inna da su Atika muke xakinmu muna sauraro cikin murna da farin ciki zata zartar da hukunci na adalci a tsakaninmu suma su Mama da nata iyalin suna wurin su don daga ita sai Babana da kuma Baba Yahaya ne a tsakar gidan. Muna cikin sauraronta sai muka ji ta ce mishi, kan wannan maganar ne kaje ka xauko ni Yahya? Cikin ladabi ya ce mata eh, Inna sai kawai muka ji ta ce to ai kuwa dai baka kyauta min ba, ashe waxannan yara ba ‘ya’yanka ba ne ina dalilin da ba zaka zartar da hukunci a kansu ba? Ina dalilin da za ku zauna kuna kace-nace dashi akan wannan ja’irar yarinyar mai bakin ido? Ba ga sauran ‘yanmata a xakin uwarta ba? Ko su me zaku yi da su? Su masu son auren nan ai duka sun cancanci a basu wa za’a ba wa za’a hana? Yanzu shi wannan yaron na gidan nan in an hana auren nan ba a ji kunya ba? Ai sai yaga kamar don ba ku ku ka haife shi ba gashi kuma a gabanku ya girma yana kuma hidimarku ai shi ne ma gidan tunda bini-bini za ka ji Ado dai, Ado dai, Ado dai. To kuma sai ku hana shi aure Yahya? Ai bai yi ba ni da Inna da su Atika muka zaro ido don jin ba zamu samu goyon baya ba, sai dai dole muka yi shiru muna ci gaba da sauraro, su waxannan ‘yanmata guda biyu da suka saura a xakin Fatsuma tunda su na majadan sun samu nasu mazan ko? Baba Yahya yayi maza ya ce eh, sun samu, ta ce to su sauran na xakin nata Atika da Aliya ko? Ya ce “Eh, sunan su kenan ta ce to ka baiwa Salisu su xaya shima xan wan uwar tasu da ya zo nema ka
Chapter 4 · 0% Book details