← Book details Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 22

Sashe 11

Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can cikin zuciyata na sake tunawa da Anti Ramla da irin yanda ta rinqa jaddada min cewar kar in yarda in bar Ado ya tava budurcina tunda dai na riga na ce ba sonshi nake yi ba, ba zan zauna dashi ba sannan suma mun riga mun san ba da manufar suka karvi auren nasu ba, aure ne kawai suka yi da nufin vata suna don kawai a maida budurwa ta zama bazawara. A wannan lokacin ban yi tunanin wani abu ne mai tsanani ba yin hakan, musamman da yake nasan babu wata alaqa dake shiga tsakanina dashi, to ashe wai ba haka ba ne, ban san dalili ba ban san abinda yasa ya matsa ya takura rayuwarshi kan sai lalle ya tava ni ba, don ya cika burin Mama ne ko kuwa dai da gaske son nawa ya soma yi kamar yanda yake yawan nanata min? Na sake zurfafa cikin wani tunani don in tantance tsakanin son da Ado yace yana yi min da kuma sha’awa kamar yanda Anti Ramlah ta tava yi min bayanin su ban iya gane komai ba illa iyaka dai nasan ko ma wanne yake yi min a cikin biyun to ya soma kanshi cikin fitina don kuwa yayi matuqar takura kanshi barci yayi matuqar yin qaranci a gare shi. Kallo xaya zaka yi mishi ka gane walwalarshi ta ragu, gashi kuma rama ta bayyana a fuskarshi. Ina cikin wannan zaman sai ga Sa’adatu ta shigo rungume da wata qatuwar leda, na tabbatar Ado ne ya aiko ta sai da ta shiga xaki ta ajiye sannan ta fito ta gaishe ni ta miqe zata tafi, nayi maza na ce mata zo mana Sa’adatu, ni hayaniyar me jiya na rinqa ji tana tashi a cikin gidanmu? A hankali ta ce min, Anti Zubaida ce suke faxa da Mama, shi ne Anti Suwaiba ta shigan wa Maman da sauri na ce mata Mama kuma? Ta ce min eh, nayi maza na ce mata me ya haxa su Sa’adatu? Ta ce ban sani ba amma dai na ji tana cewa Inna wai Mama macuciya ce tayi qaryar ta bar mata ko menene? Ni ban gane ba, cikin zuciyata na gane da magana bai wuce Zubaida ta gane Mama irin rashin adalcin ta ba. Na yi murmushi kafin na sake kallon Sa’adatu na ce mata, yanzu kuma Zubaidan tana magana da Inna ne? ta ce, eh daga kwana ukun can ne take samun Inna in ta ganta a kicin tayi ta mata magana ita kuwa sai ta ce mata ai zaman aure sai an haxa shi da haquri, nayi dariya na ce Inna kenan ki ce ina gaishe ta in wankin ya haxu ta baki ki kawo min ta ce to ta tafi. Ruwa ya xan fara saukowa sanda Ado ya shigo gida ga dukkan alamu kuma ranshi a vace yake duk da shi xin ba mai yawan fushi ba ne, na kuwa gane hakan ne ta dalilin yawan baqaqen maganganun da nake gaya mishi don wai in tabbatar mishi da qiyayyar da ke tsakanina dashi. Shi kuwa maimakon ya vata rai sai ya ce min ai shi auren namu ba yin shi aka yi a dalilin so ko amincewa ba anyi shi ne kawai bisa qa’ida ta rabo da kuma qaddara, don babu wanda yasan menene a tsakanin, don haka mu baiwa juna lokaci kawai. Tashi nayi na bi bayan Ado, zuwa cikin xakin duk da lokacin da ya shigo bai ma kalle ni ba balle ya yi min wata magana, ina shiga xakin nayi mishi sannu don dai in samu ya saki jiki in tambaye shi abinda nake son sani. Ni me ya haxa Mama ne kuma da wannan yarinyar Zubaida? Yayi maza yayi min wani lalataccen kallo kafin ya tambaye ni, to ina ruwanki? Hakan da yayi, ya yi matuqar vata min rai, amma sai na danne na ce Mama kenan, ai munafurcinta da sharrinta da mugun abin ta da iya…ban kai ga qarshen maganar ba na ji caraf Ado ya cukume ni ya shaqe da hannunshi, za ki zage ta ne a gabana? Kina nufin ke xin rashin kunyarki har ta kai ki kalli idona ki zageta? Ya sake ni ya tsare ni da idanuwanshi wata qila don ganin na shiga mutsu-mutsun qoqarin qwatar kaina saboda wahala, kina nufin don kin zama matata sai ki zagi Mama akan idona ina kallonki?” Duk da ban wastsake daga wahalar shaqar da ya yi min ba, ban yarda nayi shiru ba sai da na ce mishi ai ni ba matarka bace ba kuma zan yarda in zama ba, bai kula ni ba ya wuce ya shiga cikin xaki ya barni a nan ina kuka sai da ya sake fitowa falon na gane wanka yayi. Can gefe ya koma ya zauna kan kujerar dake wurin sannan ya xago ido ya kalle ni cikin natsuwa ya soma cewa ai na riga na roqe ki cewar ko bamu mutunta juna ba a zaman da zamu yi to mu mutunta auren dake tsakaninmu, mu kuma girmama shi, mutunta aure da girmama shi yana nufin mutuntu ta, duk wani abin da ke buqatar mutunci da ke zagaye da shi haka nan a girmama duk wani abinda ke buqatar girmamawan dake tare dashi Mama ai uwa ce a wurinki aurena da ke kuma ya sake maida ita surukarki sannan ni bani da wata wacce ta fita mahaifiyata ta rasu ita ce uwata ba zan iya ba ba kuma zan yarda ba ki rainata ina gani balle har rainin ya kai ga zagi ina ji, na ce eh ai shi yasa nima nace maka ba zan iya zama da kai ba don nafi buqatar auren mutumin da zaiga girma da mutuncin Mahaifiyarta ba. Ai ni ban raina Inna ba ban kuma tava yi mata wani abu wanda yake na raini ko rashin mutunci ba in ke kin xauka a haka to ita Inna na gode bata xauka a hakan ba domin ranar da na fara shiga xakinta na gaishe ta na roqe ta ta yafe min abubuwan da suka faru a baya a tsakanina da ita na kuskure ta ce ban mata komai ba, kuma a tsakanina da ke da ki ke ganin nayi matana kamar yanda nima zuciyata ta qi yarda da cewar ban yi matana ba, sai na roqe ki ki bani dama irin wanda ta bani kiyi min adalci irin wanda ita xin tayi min, ki kuma yarda da yawan ce mikin da nake yi cewar ni xin namiji ne ma’ana zan iya juyawa a kowane lokaci daga wani matsayi in koma wani, ban ce mishi komai ba. Kwanaki biyu a jere harkokinshi kawai yake yi bai kula ni akan wani abu ba, iyaka dai nasan yasa min ido mai yawa kan al’adar da nake yi, ya kuma hana kawo min abincin da ake yi daga cikin gida, wai na riga na fara girkina duk kuma da ba yin girkin nake yi ba. Rannan ya shigo gida bayan sallar Isha’i, tuni nima na riga nayi sallata na hau kan katifa nayi kwanciyata naja bargo na kululluva zuwa zan ya shigo riqe da leda a hannunshi abinda za’aci ya kawo har kin kwanta ne? na ce mishi eh, tashi kici naman nan tunda xuminshi kar yayi sanyi nace ai na qoshi, ya ce to ba laifi, kin yi wanka ne kin yi sallah? Nayi shiru kamar ban jishi ba, ya ce ba kya jina ne? ko ba na ce bana so in yi tayin magana kina jina kina kin amsawa ba? Kinyi wankan al’ada ne?na ce ba yau na ke yi ba, ya ce to ban yarda ba ki tashi kiyi yanzu, na ce ha a nuka ake yi ba sai ta xauke ake yin wanka ba? Ya ce ko ta xauke ko bata xauke ba yanzu za ki yi wankan wacce irin al’ada ce haka har kwana shida? Tashi kiyi wanka kawai ko kuma in ganta da idona kamar yanda rannan na ganta. Rikici mai yawa ne ya faru tsakanina da Ado saboda qoqarin da nayi wajen ganin na hana shi ganin abinda yake son ganin kallona yayi, ya yi murmushi bayan ya tabbatarwa kanshi da abinda yake son tabbatarwar, nayi matuqar tsorata da abinda ke shirin faruwa na takura na maqu re a jikin ban go a daidai lokacin da na xaga ido na kalle shi naga abinda yake yi tsoro ya sake kama ni hawaye suka soma zuba daga idanuna, bai fasa abinda yake yi ba savanin sauran kwanakin da suka gabata da in ya ganni ina kuka yake haqura ya qyale ni, kayi haquri kar ka tava ni. Nayi maganar cikin wata irin murya da ta riga ta tsorata da abinda ke shirin samunta kiyi haquri ki bar ni in tava ki, ya faxi hakan a daidai lokacin da ya miqo hannayenshi a gare ni, kuka sosai na soma yi mishi ina roqonshi yayi min adalci kar ya tilasta ni yin abin da bana so yayi murmushi ya ce babu komai don na tilasta ki tunda na riga na gane ke xin baki da ra’ayi baki da wani abin da ki ke yi don kanki, kina bin umarnin da ake baki ne. Kin kuma san ba zai yiwu ni dake mu haxu muna bin umarnin wani mutum wanda shi a gidan shi yake nashi zaman auren lafiya duk irin nashi mas’alolin amma mu a namu gidan yayi uwa yayi makarviya wajen ganin bamu zauna lafiya ba, tuni na bar kukan da na ke yi na koma sauraron kalaman Ado saboda na qara tsorata da kalaman nashi, ai nayi haquri na kuma tilasta zuciyata yin haquri akan dole saboda na xauka ra’ayinki ne ki qi yarda da ni ki qi bani haxin kai a duk lokacin da na nemi kiyi min hakan. To amma kuma a ‘yan kwanakin nan sai na gane saki ake yi don naji wayar da ki ka amsa kwanci wanda a ciki ake jaddada miki kar ki yarda in tava budurcinki, to ai nawa ne, domin aurena ya bani shi ba zai yiwu ba kuna zuane a xakina a gidana kina bin umarnin wata naki savanin.” Na kawar da kai game da ke don ki fahinci cewar ba dudurcinki nafi nema ba a yanzu abinda nafi
Chapter 11 · 0% Book details