← Book details Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 22

Sashe 3

Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

qi yarda suyi vatawar da zasu rabu ko ya zo gida an yi kaca-kaca bai hana shi kuma gobe ya sake dawowa. Har irin tsayuwar da yayi kan neman auirenta sai da ta gaya min da ta gama kuma sai ta ce to gashi yau daga kai mishi wannan magana ya turo xan shi kan maganar aurenki, yanda ya rufa min asiri shima Ubangiji ya rufa mishi, na ce amin Inna. Abin mamaki gari na wayewa sai ga Alhaji Tijjani makwabcin Alhaji Mai kuxi shi da Limamin unguwar su sun zo wurin Babana wai sun zo ne a madadin Alhaji Mai kuxi don su nemar wa Alhaji Abba izinin aurena wai da Hajiya Kubra ta yi wa Alhaji Mai kuxi bayanin abin da Inna take ciki da wa’adin da Babana ya bayar lokacin uma Alhaji Abban yaje gidan sia ya roqi mahaifinshi ya turo a tambayar mishi izinin auren nawa. Shi yana sona.” Inna tayi dariyar jin daxi, farin ciki mai yawa ya kama ta, ta xaga hannu sama tayi ta addu’a da ta gama sai ta waiwayo ta kalle ni ta ce min “Amma fa ba zaki canza wannan yaron ba don Alhaji Abba yazo ba duk da shi xin xan uwana ne amma kuma akwai mutunci da ganin girma mai yawa tsakaninmu da Mallam Yahaya, da kuma hajiya Hairan don haka kan Salisusu kawai za ki tsaya, na ce mata to Inna. Ba mu san yanda aka yi ba, sai kawai muka jiwo Mama tana sakin manya-manyan ashar a tsakar gida, tare da faxin “Lalle ana munafurci a garin nan, jiya yaron nan Salisusu yazo yau kuma ga waxannan sun zo, to raba musu ita biyu za ayi kenan ko?’ Mama wai fa don ace tayi farin jini ne, in ji Habiba. Mama taja tsaki ta ce, farin jinin gidan uwar wa? A yanzu ko Samari goma aka turo mata rana xaya ai an yi aikin banza tunda dai turo su aka yi, ban da haka kuma shekara nawa aka yi a gidan nan ana hidimar arziki a kanku ina nunawa uwarta bata tava cewa ga nata ba? Magana kamar wasa, Mama ta shiga kai-kawo mai tsanani, kowane lokaci tana tashe da Babana tana gaya mishi abinda take gaya mishi, sai dai kuma babu wanda yasan me take faxan sai su biyun suka san abinda suke yi. Aike akan aike daga gidan Baba Yahaya da kuma Alhaji Mai kuxi, Babana ya qi ya tanka, rannan Baba Yahaya yazo da kanshi a tsakar gida ya samu Babana, don haka shima a tsakar gidan ya zauna sai da ya gaisa da duk mutanen gidan kowacce ta nufi xkainta, sannan ya kalli Babana ya ce mishi. “Wurin ka fa nazo kan maganar yaran nan.” Baba ya gyara zama ya xaure fuska alamar rashin wasa kafin ya ce, “Ina sauraronka.” Baba Yahaya yayi kamar bai gane abinda yayin ba, ya ce mishi an turo mutane wurin ka daga wurina da kuma wurin Alhaji Mai kuxi da fari ka ce a saurare ka don zaka yi shawara tukunna akai, daga baya kuma da aka sake turowa sai ka ce wai saboda ka raba faxa a tsakaninsu duka ka zartar da hukuncin yi mata miji kai da kanka. Wanene mijin da ka zavan matan? Ai mu dukan mu muna da ‘yancin ka gaya mana don mu ma iyayenta ne ba kai kaxai ke da ita ba, kuma kasan zaka iya zar tar da wannan hukuncin a kanta ma Alhaji menene na bata wa’adi har kana cewa in ba haka ba ita da uwarta su bar maka gida?” Maganganu masu yawa Baba Yahaya ya yi ta sakewa Babana, ya kuma ja ya tsaya akan ba zai bar gidan ba, sai Babana ya gaya mishi mijin da zai ba ni, da Babana ya ga da iyakacin gaskiyarshi yake yi, gashi kuma tuni ya riga ya amba ci ranar bikin matsowa kuma take yi, sai yaga to bari kawai ya fexe komai ya ji ya huta da voye-voyen da yake yi. Ina daga xaki nayi kasake ina sauraron in ji ya ce Nasiru ne abokin Ado, na kuma zuba wa Inna ido ina kallon irin sauraron da take yi, daga tsakar gida sai kawai na ji ya ce, wai Ado ne. A daidai lokacin da Baba Yahaya ke tambayar shi Ado? Ita Inna rafka salati tayi yayin da ni kuma na qurma musu ihu ina daga cikin xaki. Baba Yahaya ya ce, “wannan kuwa shi ne zance, me ka ke so ka yi wa Binta ne Alhaji? Ai kuma dai ba zai yiwu ba don ba zan qyale ka ba saboda kowa yasan in da maganar taka ta dosa da kuma abin da yasa kayi ta. Tuntuni Ado yana gidan nan bai ce yana sonta ba, ba ka yi niyyar ba shi ita ba har ka zartar musu da hukuncin bar maka gida, sai da aka ga masu son aurenta sun zo na gaskiya sai kuma a koma a cuno maka shi ace ka bashi ita don a samu a yi ta sa uwarta baqin ciki? To kun yi kaxan. Ya tashi ya fita a fusace, Mama ta bishi da kallo kafin taja wani mummunan tsaki daga baya kuma ta saki wani lallausan murmushi ta ci gaba da abinda take yi. Ni da Inna hankalinmu yayi matuqar tashi, in ban da kuka babu abin da nake yi, Inna kuwa ta shiga tattara kayanta tana kintsa abinda yake buqatar kintsi alamar kenan in har Baba Yahaya bai yin nasarar hana Babana haxa aurena da Ado ba, to zata tasa ni a gaba mu tafi mu bar mishi gidan. Da yamma bayan Sallar La’asar na shirya na fita gidan Mallam mai babban allo, na tafi na gama rattaba mishi komai yana sauraro yana kuma shan furarshi bai fasa ba, babu alamar damuwa ko wani vacin rai a tare dashi. Bai kuma ce min komai ba sia da na gaji na ce mishi to Mallam kana jina ba ka ce min komai ba. Lokacin ne ya xago kan shi ya kalle ni wani irin lalataccen kallo ya yi min sai da ya gama share furar da ta tava lavvan bakinshi sannan ne ya ce min ba kun zartar da abin da zaku yi ba ne ke da uwarki, ga kuma Yahaya yana taimakonku shi ne ku ka zo ku ka gaya min. To ni meye nawa a ciki? Ba sai ku je kuyi abinda zaku yi ba? Na soma yiwa Mallam mai babban allo kuka yayin da shi kuma ya shiga yi min faxa abinda ya yi dalilin da kukan nawa ya qaru. “Kin tava ganin in da mai Doki ya koma kuturi? Ya ce zai ba da ke ga Ado ace bai isa ba to sai waye ya isa? Sai ku da Yahaya? Haka kawai don kun samu mutum mai haquri sai kuma ace iya shegen da za’ayi mishin har da na wulaqanci da rainin hankali? Ita uwarki ita ta ce miki ta zavi mijin da zata aura? Ko shi Yayanta bai kawo nashi gwanin ba? Na ce mishi a’a ni ga nawa gwanin da nake so a ba, ya kuma bada ita a dole duk da a lokacin auren tsinken zabori ban bada ba, amma na gwada iko na cewar ni ne uba mahaifi. Shi kuwa Alhaji Surajo ke da uwarki kun ce bai da irin wannan ikon a gidan shi saboda shi ba uba ba ne ko? Tashi ki bani wuri, ya yi min umarnin ta hanyar tsawa. Ina miqewa yana magana zata zo nan uwar taki ta same ni, sakarya kawai sha-sha-sha, in ban da sakaryar uwa wa ke taimakon ‘ya bijerewa uba ana karo ne tsakanin qwai da dutse? To in ma cutarku ake son yi sai me? Don an cuce ku, kuma sai me? Kafin ayi muku ba a yi wa mutanen kirkin da suka fiku ba? Bai wuce ba? Abin mamaki itama Hajiya ‘Yar dubu rannan taya shi yi mana faxan tayi, har tana faxin shi lamarin aure ma ai ya wuce duk yanda ake zaton shi, sai dai addu’a kawai, in ban da a gidan ku a ina ake yin haka? Uba ya ce ga yanda zai yi ace wai bai isa ba? Ko da yake ba laifinku ba ne ku kaxai, na shi yafi yawa don shi yayi sakacin da mace tasha gabanshi sai abinda taso yake yi.” Mai babban allo ya shiga yi mata faxa kan hakan da ta faxa, ni kuwa nayi gaba na bar su tunda dai na gane ba goyon baya zan samu ba. Kin yi mishi bayanin kuwa? Inna tayi min tambayar a sanyaye saboda ganin yanda nima jikina yayi sanyi, na ce mata eh, amma dai kar kije. Tayi shiru tana kallona, zuwa can ta ce min shi Baba ba zai fahimci yanda abin yake ba, na ce mata eh. Ilai kuwa rannan dare nayi sai ga Suwaiba ta xaga labulen xakinmu babu sallama babu komai ba tare da ta gaida kowa ba ta ce min, wai in ji Kawu Ado wai kije yana kiranki.” Muka yi shiru ni da Inna, ta juya ta tafi na kalli Inna na ce mata, bari in je in ji abin da zai ce min, ta ce min to. A zauren gidanmu na same shi tsaye cikin kwalliya, sai wani qamshi yake yi tanfar wani wanda ya zo taxin gaske, sai dai ba don taxin yayi kwalliyar ba, xabi’arshi ce yin hakan don a yanzu ko Babana bai kai Ado sanya yadi mai tsada ba, muka xan yi shiru kaxan na xan wani lokaci kafin na kawar da shirun ta hanyar tambayarshi. “An ce kana kirana?” ya ce min “Eh” na ce to lafiya? Ya ce, qalau, taxi zamu yi. Na sake kallon shi a sakarce na ce taxi wane iri? Ya ce taxin aure, na ce to muyi in ji, ya ce ai gashi nan muna yi.” Na gane shima irin zuwan da nayi shima shi yayi, don haka sai na ce mishi Ado, ya ce Humaira, na kawar da duk vacin ran da nake ciki don in samu gaya mishi abinda zan gaya mishi, na ce mishi yanzu nan kai idan aka baka ni aka ce ka aura sai ka aura? Cikin natsuwa ya ce min qwarai
Chapter 3 · 0% Book details