Sashe 16
Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da hannunshi, “Matata ce ai Mama don na tava ta ba wani laifi nayi ba, sannan na fara gajiya Mama, zuciyata ba za ta iya ci gaba da xaukar irin wannan abin ba, kin yi sammakon zuwa dukan yarinyar nan alhalin ba ki san yanayin da ta kwana a ciki ba, ko tana da lafiya ko bata da ita.” “A’a qarya kake yi gaya min dai abin da kake son gaya min xin, ja’iri mara kunya mara mutunci akan wannan ja’irar yarinyar? Ai in ba hanzarin raba ku nayi ba to in ba sa’a nayi ba ina zaune ne kawai zanga ka rufe ni da duka.” Ta sake sharvo bulalar ban san yanda aka yi ba sai kawai na ganta a hannun shi, “Haba Mama, wannan fa bulalar doki ce kike duikanta da ita.” Ban ita nan.” Tayi mishi irin tsawar da bata tava yi mishi ba, a’a Mama ba zan baki wannan bulalar ki buge ta ba. Bayan bata yi miki komai ba, in kuma tayi miki ma ai ni ya kamata ki gaya wa in yi mata nasiha sai in bata ji ba ne zan sake dubawa in ga wani matakin da zan xauka amma ba duka kan wannan ba, ai ba zai yiwu a buge ta tana budurwa sannan yanzu ma tana matar aure tana hidimar mijinta da xaukar xawainiyar shi ace za a buge ta, ko nima da nake matsayin mijinta in tayi min laifi a yanzu haquri zan yi tunda nima akwai abubuwan da nasan haquri zata yi dani a kansu. Ni ban tava ganin ana bin matar aure gidan mijinta a buge ta ba sai ita, gaskiya ni kar a sake yi min haka Mama, na roqe ki don bana so. Kasaqe Maman tayi tana kallon Ado, cikin kaxuwa da mamaki. Ai in bar maka ita ta sangarce ta lalace kenan, tafi qarfinka taje tana rabaka da ‘yan uwanka tunda su abinda suka fi iyawa kenan? Ya ce, a’a ni ban san abinda suka fi iyawa ba, Mama na dai san haqququwana da ke kanta tana qoqarin tsare min su, maganar zumunci kuma ba ita ce ta haxa ni da su Ibrahim ba mata suka kawo Baba kuma ya ce bai yarda a rinqa shigo mishi da matan banza cikin gidan shi ba.” Kasaqe Mama tayi tana sauraron Ado cikin kaxuwa da mamakin kalaman bakinshi, uh yanzu nasan kasan mace, tasa kai ta fita kamar ace tayi fushi zance ya qare amma ina? Da daddare nayi wanka ina zaune gabanshi yana shafa min wani mai a tabon shatan dukan Maman da ke jikina, yana yi yana faxin nan da shekara guda in muna raye ba za ki ga tabo a jikinki ba Humaira, tunda ni me za ki yi min in buge ki? Ai in ma kin yi min laifin dukan to bai wuce in yi kamar zan kaxe miki qura da bakin rigata ba, tunda nasan ba za a xauki wani lokaci mai tsawo ba zan dawo miki da lalurata. Muna cikin haka sai ga Mama ta shigo har can cikin xakin, tana ganinmu ta soma faxin uhun, ni fa nasan ba haka kawai kake yin abinda kake yin nan ba, don haka na yafe maka duk laifuffukan da kayi a sanadin zuwanta gidannan in ma haxin baki suka yi na su vata tsakanina da kai to ba su isa ba, ba za su raba mu ba. Rubuta mata takardarta kawai in tasa ta a gaba in kai wa uwarta ita don in gaya mata gata nan na kashe wannan wutar aniyar kowa kuma ta bishi, kamar dai in ce amin sai na fasa saboda Ado da kuma ita Mamar kanta don haka sai na faxi kawai a zuciyata. Shiru Ado yayi yana jinta bai tanka ba tayi rarrashi da ban baki iri-iri bai motsa ba, da ta tunzura da shirun nashi sai ta ce mishi, amma dai ka san dagewa kan zama da itan yana nufin ne kayi zavi tsakanina da ita. Yin wannan zavin kuma ba qaramin fitina zai zama maka ba, don zaka fita daga gidan nan zaka fita daga cikin harkokina, za kuma ka fita daga cikin dukiyar mijina da ka yi wa kane-kane, sannan ko kayi hakan zan kuma iya bi ta wata hanyar da zan rabaka da ita da qarfi tunda in kai ban gaya maka ka ji ba shi uban ta ai zan gaya mishi ya ji. Ya ce mata haka ne.” Muna cikin haka ne sai kawai ga Suwaiba ta shigo da gudu, “Mama wai ki zo da sauri ga Anti Habiba tazo.” Suna barin xakin, Ado ya kalle ni cikin wani yanayi da yafi kama da na tausayin kai, cikin qarfin hali ya tambaye ni in na ce miki ina sonki za ki gamsu? Da sauri don in kwantar mishi da hankali na ce mishi me zai hana? Ya sake kallona cikin natsuwa ya ce, “Duk abubuwan jin daxin da nake ganin kamar yau ma za ki daure kiyi haquri dani in same su sun rushe ko? Nayi murmushi na ce, sai dai in kai ne baka so.” Ya saki wani lallausan murmushi ya ce, “Humaira in tambaye ki mana?” na ce to, dama dai kayi sa’a in san amsar tambayar, kin tava sanin wani abin da yafi aure daxi? Nayi dariya na ce in dai auren na namiji ne kamar ka to ina ganin kamar babu. Daxi ya kama shi, ya jawo ni jikinsa. Rannan kwana muka yi ni da Ado tanfar dai dama mu xin ba baqin juna ba ne, tanfar kuma ya mance da kasadin da Mama ke yawan yi mishi na cewar tari mai qarfi in kayi a wannan xakin ina jin shi, don haka babu wani abin da ku ke ciki wanda ban sani ba. Harkar gabanshi ya yi, nima kuma ban takura mishi ba, saboda a yanzu nima ba zai yiwu in ce ba na sonshi ba, ban da haka kuma na riga na gane Inna tana son auren namu a yanzu in kuwa haka ne to zan yi komai wajen ganin Mama bata qwacewa Inna mijinta ta kuma sake hana ta jin daxin surukinta ba. Washegari da safe Ado ne ya shiga gida don gaida iyayenmu, ya dawo yake gaya min cewar, kin ji ashe wai zuwan nan da Habiba tayi jiya uwar mijinta ce ta kora ta bayan mijin ya naxa mata dukan tsiya, kuma don wulaqanci baki ga doguwar wasiqar da suka haxo ta da ita ba, wai ta zauna a gida daga nan zuwa watanni uku don ta koyi tarbiyya. Na kalli Ado kawai cikin zuciyata kamar in faxi wata magana sai kuma na tuna ba zai yarda in gayawa Mama wata magana ba, don haka naja bakina nayi shiru na vuge da cewa kai abin bai yi daxi ba, yaushe aka yi auren da har za’ace a dawo gida ayi zaman wata uku? Ya ce, to ai kin san bakinta itama kuma ba kunya ne da su ba, na dia ja bakina nayi shiru. Kiyi abin karyawa da ita na ce to. Tun daga lokacin ya zama min qa’ida inna yi girki bayan abincin da nake zubawa na cikin gidanmu zan kuma zuba na Habiba daban. Ado ne yasa ni yin hakan ga kuma kwanukan su Ibrahim safe, rana da dare, amma duk da haka ban fita ba a wurin Mama, wai ban sa mata nata kwanon daban ba, na sata a haxaka sai kace ni tawa uwar ba a haxakan na sakata ba. Saboda gudun fitina, bayan kuma ni nasan zai yi wuya Inna taje tana wani xiban abincin da na aika dashi a kunya da kara irin nata ma ba za ta je tana yin hakan ba. Tuni dama Mama ta riga ta yaxa rashin jituwar dake tsakaninta da Ado, bata bar shi ya zama sirri ba a tsakaninsu, don haka kowa yasan da maganar, ta xauka hakan zai zamo tozartawa ga shi Adon ko kuma Innata ace ta mallake mata qani ta rabata dashi, ta sani ba kanta ta jawa magana ba, don kuwa mutanen da suka santa suka san komai na sirrin zaman gidanmu da dalilin da ya sata tasa Ado aurena sai albarka suke sawa Adon suna faxin mun gode mishi kaga min jarumin yaro ai gara da yayi mata haka. Wannan magana da ta riga ta bayyana kowa ya san da ita yasa dawowar Habiba gida ya zamo abin gulma abin tattaunawa a tsakanin mutane wasu ma faxi suke yi to ai gashi nan tana qoqarin fidda wata ga tata nan an korota. Baba Yahya da kanshi ya nemi wani abokinshi ya xauki Habiba a motarshi suka je har gidan don maida ita xakinta, daga nan su baiwa uwar mijin haquri, tunda dai an yi sa’a hutu suka bayar basu furta kalmar saki ba. Amma uwar mijin Habiba tayi qememe ta qeqasa qasa ta ce ai tunda da bata hutun nan sai tayi shi in dai ba sun gwammace auren ya mutu ba ne, tunda dai ai sun san ‘yarsu zata gidan wasu, amma basu tsaya suka yi mata tarbiya ba. Shi kuwa uban mijin da suka koma ta wurinshi ko zai yi halin maza ya ce a’a tunda an riga an kawo ta to shi kenan iyaka dai a kwave ta don gaba kar ta qara sai yace tunda hukuncin da Hajiya ta zartar kenan sai dai ayi haquri aje kawai in lokacin yayi a dawo da ita. Wurin Ado naji labarin saboda abinda aka yin yayi matuqar vata mishi rai, ni kam murmushi na xan yi can cikin zuciyata dai cewa nayi ashe dai ba Babana kaxai aka yi wa irin wannan kamun kazar kukun ba. Duk da irin hidima da xawainiyar da nake yi da Habiba saboda tausayinta da nake ji gashi kuma na gane xan qaramin ciki ne da ita koma bata nake yi ko ba ta zo ba in aike mata dashi don nasan tana buqatar kulawa ta musamman amma bata gamsu ba haka Mama gaba xaya jin haushina suke yi tanfar dai ni naje na fito da ita daga gidan mijin nata. Kullum dai ta shigo xakina sai ta zagi xakin sannan shigarshi babu qa’idar sallama a wurinta, sau biyu tana samuna kan shimfixa tare da mijina amma hakan bai hanata