Sashe 2
Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
MIJIN-TA-CE 2 N a xaga ido na kalli Inna da hankalinta in yai dubu duka ya tashi, na ce “A’a Inna, to menene na wannan tashin hankalin? Mu bar mishi gidan mana ina ce shi kenan magana ta qare?” Tayi maza ta riqe baki nuna girman lamarin, ta ce “Magana kuwa bata qare ba, yau in da ni kaxai ya ce in bar mishi gida to da ta kwana gidan sauqi, amma budurwa kamarki ace ta bar gidan ubanta a dalilin shi xin da kan shi ya koreta ai ba qaramin al’amari ba ne, vata suna ne ba kaxan ba. Sai ayi ta nanata zancen har ‘ya’ya da jikoki, don haka ina ganin dai to maimakon ayi haka bari in koma kawai in ce mishi ko shi xin zai baki mijin da yaga ya dace tunda ai Mahaifinki ne uba kuma dama yana da wannan damar.” Da sauri na ce mata, “A’a Inna, a’a ni kam gara kawai ki bar ni in yi tafiyata ban san abinda na yi wa Baba ba ya tsane ni, ya tsani farin cikina.” Tayi maza ta daka min tsawa, ta hanyar faxin “Ke kama bakinki, kiyi shiru baka gaya wa Mahaifinka magana ko da kuwa me yayi maka?” Na ce mata “Haba Inna, in ban gaya wa Baba magana ba me zan yi ba shi ya ja ba? Tayi maza ta wafce min bakina da duka abinda ya yi dalilin dana soma kuka sosai. Tun ina yin kukan tana kallona har ta gaji ta soma rarrashina, daga baya ma ta shiga taya ni kukan, muka yi har muka gaji muka yi shiru don kan mu. Na fito tsakar gida zan yi mana wanke-wanke daga nan in yi wanki sai na ji muryar Anti Kaltume a falon Mama alamar tazo gidan kenan, dama kuma su xin don sun zo wuni gida basa zuwa su gaida Inna sai in ta ji muryarsu ne zata leqa ta ce musu “A’a su Kaltume kun zo ne? su ce mata eh, su gaisa. In kuwa lokacin tafiyarsu yayi to in dai ba tana tsakar gida ba ne sanda za su tafin tayi musu sallama to zata shafa ne kawai bata gansu ba sai ta gane sun tafi. Na wanke kunfan hannuna na nufi xakin Mama da nufin gaida Anti Kaltume, don ita tana cikin ‘yan dama-daman ‘ya’yan Mama, tafi Anti Sha’awa yi min adalci sanda nake qarama, sai kawai na ji ta itama tana cewa. “Uh’uh Mama bar mata ‘yarta, taje can tayi sha’aninta ita da ‘ya’yanta, mu ma a nan muyi namu, ai ba a qwacewa uwa ‘ya’ya, Mama ko an qwace su zasu koma.” “Ko zan bar mata sauran dai wannan kam zan tabbatar na riqe ta a hannuna saboda in har na barta taje ta sake, to ba qaramin iya shege zata yi ba.” Nayi sallama na gaida Anti Kaltume, na xan yi ma xanta da take goyo wasa itama kuma sai kallona take yi, tanfar dai wacce bata gama sanina ba, ‘yar gari wato kenan yanzu kin girma kin daina zuwa wurin mutane ko? Nayi murmushi na ce, “Anti kenan, ban fa daxe sosai ba ai ban kai wata biyu ba.” Ta miqo min hannayenta duka biyu alamar daquwa. “Wata biyun ne ba ki daxe ba? Ki zo kiyi min wanki kayan dattin ‘ya’yanki sun taru.” Na ce, “To Anti.” Na tashi na tafi. Ko kaxan bana jin qyashin zuwa gidan Anti Kaltume in yi mata wanki ko ma wani aikin da yafi wankin wahala, saboda ita akwai hikima cikin lamarinta, tunda ta gane ina jin zafin zagin uwata da ake yi a gabana ta yi maza ta daina sava min, Anti Sha’awa da sauran yaran. Ina fitowa daga xakin naji Anti Kaltume tana sake cewa, “Ba fa zai iya da ita ba Mama, wahala kawai za a sha ki bar mata ita suje can su qarata, in taso uwarta ba laifi tayi ba, mu ma duk muna sonki.” Mama tayi maza ta daka mata tsawa “Tafi can shashasha, duk ‘ya’yana sun goyi bayan abinda na shirya sai ke saboda ke dama dole ce tasa ki ka yarda na haife ki in ban da haka da can wurin su kika faxo wani so ki ke yi min?” Komawa nayi xakinmu wurin Inna don ya zama min dole in zaiyane wa Inna irin maganganun da nake ji tunda ga irin furucin da Babana yayi na in fidda miji cikin kwanaki uku ko kuma mu bar mishi gida. Inna ta kalle ni cikin nutsuwa ta ce min, “Haka ne?” na ce mata “Eh.” Ta ce, “To babu laifi.” Tasa hannu ta xauki wayarta ta soma magana da Mamanta Hajiya Kubra, izini take so ta neman mata wurin Babanta don ta koma gida. “Me ya yi zafi haka?” ta kwashe bayani duka tayi mata, ta ce, “To zan yi mishi bayani in ji abin da zai ce, amma kafin nan sai ki sanar da Mallam Yahaya don kar ayi abin da zai ce ba a sanar da shi ba.” Ta ce, “To.” Suna gama maganar, Inna tayi fulashin xin Baba Yahaya, ya kirata shima tayi mishi bayani, ya ce “To ai ba za’a bar gida akan maganar fitar da miji ba, ta fitar mana.” Inna ta gaya mishi gaskiya ai ni xin bani da kowa ga kuma maganar da Ado ya yi wa abokinshi da kuma waxanda Mama ke ta faxi.” Ya xan yi tsaki ya ce, “Bana son ki da irin waxannan maganganun Fatima, bana so in ace ance-ance yana fitowa daga bakinki.” Ta ce mishi “To.” Rannan da daddare sai ga Jamilu xan Amaryar Hajiya Hairan yazo har cikin xakinmu ya shigo ya durqusa ya gaida Inna, ya ce mata ni da Yaya ne, Inna ta ce wannan yaron?” yayi maza ya ce, eh, ta ce to ina yake, ya shigo mana.” Ya ce, a’a yana waje yace ne wai in shigo in kira mishi Humaira. Daga ni har Inna kallon juna muka yi, don mun gane ma’anar kiran, Baba Yahaya ne ya turo babban xan shi sa’an Ibrahim xan Mama na biyu, don shi manyan ‘ya’yan mata ne Salisu su wanda Hajiya Hairan ke kira yaron nan, har su Inna duk suke taya ta shine xan shi namiji babba yazo neman aure na. Salisu yana xaya daga cikin yaran da kullum Babana ke bada labarin natsuwarsu a duk lokacin da takaicin Baba da Ibrahim ya cika mishi ciki, yana shekarar qarshe ne a karatun da yake yi kan harkokin kasuwanci a Jami’ar Abubakar Tafawa Valewa, wato (A.T.B.U). Sannan babu inda Baba Yahaya baya tura shi kan harkokin shi, sannan shine yake tafiyar da al’amuran gidansu gaba xaya, in dai akan yara ne da yake su gidan su babu ruwansu da ‘ya’yan wannan xakin da na wancan gaba xaya abin da suka sani shi ne ubansu xaya to magana ta qare. Bare-bare sosai muka kama yi ni da Inna muna murna da farin ciki, yau na yi saurayi nima gashi an zo ana kirana. To shirya mana ki tafi yana jiranki kuma, na xan yi murmushi nan take kuma kunya ta kama ni. Hijabin dana cire da nayi sallah kawai na sake maidawa na fita. Yana tsaye a qofar gidanmu daga can gefe tanfar dai wani baqo, na xan matsa kamar zan qarasa kusa dashi na kuma kasa, saboda kunya da kuma jin nauyi. Ya xan zuba min ido kaxan cikin yanayin murmushi, shima dai kunyar yake ji ban fa tava zuwa taxi ba, ‘yammata na gaya min yanda ake yi in an zo. Na taya shi murmushin da yake yi na ce mishi “Ai nima ban tava taxin ba.” Yayi dariya cikin wani yanayi da na san dariyar rinjayarshi tayi, ya ce, “Au to shi kenan ki ce min mu duka sabbi ne, na sake taya shi wani murmushin na ce mishi eh, mu duka sabbin ne. Ya ce, to kin gani Humaira dama can mu ‘yan uwan juna ne, ko da Baba bai turo ni yau ba ma aka xaura mana aure aka kawo min ke ai ina zaman kamar zamanmu lafiya zamu yi, to zamu ce auren dole aka yi mana? Na ce, a’a ai ma ba irin tarbiyar da aka yi mana ba kenan.” Yayi maza ya ce “Yauwa, Humaira to na gode miki da ki ka san hakan, to in je in ce wa Baba dai ba matsala kenan? Nayi murmushi na ce mishi, eh, babu matsala ya ce to shi kenan, yasa hannu a aljihun shi ya miqo kuxi zai bani na ce mishi a’a, ai tsakaninmu babu haka, ba sai ka bani kuxi ba, sai da ya kalli kuxin dake riqe a hannun nashi ya saki wani lallausan murmushi kafin ya ce min. Da dai ace kuxina nayi nufin yi miki kyautar da su ki ka faxi haka to da sai in mayar dasu kawai cikin aljihuna in tafi, to amma kuxin Inna ne addu’a kuma mai yawa tayi musu kafin ta bani su. Na shiga xakinta zan yi mata sallama sanda zan taho nan sai ta xauko su ta bani na ce mata a’a Inna Baba ma ya bani kuxin ya ce in riqe na ce mishi don kuxin da zan yi mata kyauta ina da su ba sai ya bani ba, sai ta ce min sa hannu biyu ka karvi waxannan nawa ne in kaje su nake so ka bata. Don haka sa hannu biyu ki karve su daga hannun surukarki suka fitom hannu biyu na saka na karve su tare kuma da yi mishi godiya mai yawa. Habiba ta zo wucewa zata shiga gida, ga alama itama daga wurin saurayinta ta fito, duk da Salisusu ba baqonta ba ne sun kuma gaisa dashi amma bai hanata waiwayowa bayan ta wuce. A cikin gida Inna ta xaure fuska bata so karvar kuxinshi da nayi ba, don haka nayi mata bayani, tayi murmushi ta ce, to miqo min su nan in adana su don basa cikin ire-iren kuxin da kike sayo sabulun wanka da na wanki.” Rannan kwana muka yi ni da Inna muna qus-qus-qus xin mu cikin farin ciki da jin daxi, hirar abotar Babana da Baba Yahaya Inna ke yi min, tana qara gaya min cewar shi kaxai ne abokin Babana tun suna yara da ya