Sashe 5
Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bashi xaya ai ina ganin ma gaba ta kai su sun zo neman baqa an ba su farare. Aka xan yi dariya saboda rahar da tayi, Baba Yahya ya ce, Inna baqar nan fa gida ta xauko Innar giyaxe tayi shiru cikin yanayin murmushi don kuwa kowa yasan Babana kuma da mahaifiyarshi yake yi. Baba Yahya ya soma magana cikin farin ciki alamar shi kam ya gamsu da hukuncin da ta zartar, ya ce to ba zan ba Alh. Abba ita ba, Inna Ahmad zan baiwa Aliya don shi ne saurayi a cikinsu, ta ce wannan kuma kai ta shafa. Inna ma nasan ta xan samu sassaucin damuwarta, sai dai kuma nasan babu yanda za’ayi taji daxin haxa ni da Ado da za’ayi, don haka sai nayi maza na nuna mata murnata a zahiri na ce ai shi kenan ma Inna tunda gashi daga Salisusun har Ahmad duka naki ne, ka kuma da Aliya za’a ba su, Inna tayi magana cikin natsuwa tana kallona cikin wani yanayi ta ce min, to amma ke fa? Ki auri wannan yaron? Kin ga zan samu natsuwa cikin zuciyata? Ai da Atika ko Aliyan aka ba shi, ai da gangan Mama take yin abin da take yi, baqin ciki take so ta sani na ce uh’uh Inna kar kiyi maganar nan har wani ya ji ni da su Atika da Aliya duk xaya ne a wurinki, kuma gara ni in auri Ado da su su aure shi saboda ni ce babba ban da haka ma kuma nafi su sabuwa da wahalar Mama, don haka gara ni xin kiyi haquri kar kuma ki nuna baki gamsu da abinda tayin ba, dukkanmu naki ne Inna dukkanmu kuma xaya ne sannan waxanda za’a basun suma naki ne. Ta ce, “Haka ne, Allah na gode maka ni da nake ta fatan ko ke kaxai in samu ayi auren ki gashi a sanadin auren naki ‘yan uwanki ma duka sun samu auren, Allah Ubangiji ya yi miki albarka, ya kuma rufa miki asiri, nayi murmushi na ce amin Inna. Na sake maida kunnuwana can tsakar gida inda nake jiwo Hajiyar giyaxe tana sakin maganganu masu zafi, saboda hakan ne yasa ka zubawa ‘yarku mai yaji ido tana zaune a gida? Baba Yahya yai shiru kamar ruwa ya cinye shi. Can anjima ya soma magana saboda yasan shirun da tayi alama ne na wai shi take sauraro, ya ce to Inna in na ce komai na gani sai nayi magana ba fa ba jituwa zamu yi da shi na gaya miki abinda ya faru sanda nazo da maganar yaran nan da aka kawo min labarin abinda suke yi zuwa nayi da qarfina don musan matakin da zamu xauka a kan su tun abin bai yi nisa ba sai uwar su ta ci mutuncina a gabanshi ta ce wai duk tsiyata dole in ga ‘ya’yanta in kuma haqura da su tunda an riga an haife su ba kuma zai yiwu in dunqule su in maida su inda suka fito ba. Hajiyar Giyaxe ta ce, to kayi haquri, ni da kaina na baka haquri in cin mutunci tayi kuwa to ba kai tayi wa ba kanta tayi wa, gyara kayanka kam ai baya zama sauke mu raba, ba ga ta nan gasu ba, ko ni xin nan da ban san shaye-shayensu na zamani ba ina ganinsu na gaya musu kai ba sigari kaxai suke sha ba suka ce shi kaxai ne nace to bai karve su ba, su daina don duk sun rine sun zama wani iri. Sannan ko ba komai waxannan yaran su Salisusu ai sa’o’insu ne shi Baba ma ya girme shi to ba gashi nan ba ya natsu ya zama babba har ga aure zai yi su wake ta tasu? Dama shi mutum in yayi kos xin iya shege ai in ya riqa sai ya koma yiwa kanshi, don haka ba don su taimake ni kasa a mayar da wannan yarinyar xakinta. Ya ce to Inna, yanzu in na tashi daga nan zan tafi can gidan mijin nata in neme shi muyi magana in yaso da daddare sai in turo masu maida ita su maida ita, ta ce mishi to, tayi tasa mishi albarka Babana kuwa tayi mishi tas. Ba akan komai ba sai akan irin mu’amallarshi da Baba Yahaya ta ce shi kaxai ya riqe abotar da don ta Babana da tuni sun rabu. Mama tayi ta kuka tana faxin wai dama can Hajiyar Giyaxe ba sonta take yi ba, ita kuwa Hajiya ko kallonta bata yi ba balle ta damu da kukan da take yi. Mama bata xauki cewar da Hajiyar Giyaxe tayi na a baiwa Ahmad da Salisusu Atika da Aliya da sauqi ba, da farko tayi maganar qanqantarsu da Babana ya gayawa Hajiyar Giyaxe sai ta ce ai ita sanda aka kaita gidansu shekarunta goma sha xaya ne ba gata ba me ya same ta? To balle Aliya mai sha huxu a kaita xakinta kawai ta sake dawowa da maganar hidimar da za’ayin wai an riga anyi nisa babu su a ciki gashi ana matsalar kasuwa tunda kwanannan ma akayi wata asarar. Don haka a xan xaga nasu bikin don a samu a xan tanadan musu wani abu, da Babana ya sake yi mata wannan maganar sai ta ce mishi kira min iyayen yaran in ji ta bakinsu, Mama da Inna suka zo Mama ta sake rattaba mata bayani da dalilan son xagawan da ta waiwayi Inna sai ta ce ita ana ta ayi hidimar ba tare da su an sanya su cikin waxanda za’ayi wa sayayyar ba, tunda ba a faro dasu ba a xaura musu aurensu kawai a kai su xakunan mazansu arzikin gidan miji ai yafi na gidan iyaye, don haka kar ayi musu komai ko da kuwa tabarma ce. Innar Giyaxe ta ce, na gode miki ‘yar nan, Allah dai yayi miki albarka, je ki abinki kin ji Inna ta tashi ta tafi ta kalli Babana ta ce mishi kar kayi sayaiyar da su sun yafe a xaura musu auren a kai su gidajensu tunda uwar suma ta ce bata son sayaiyar, don haka na umarce ka ka aurar mata da ‘ya’yanta in kuma bani ka ke nema da magana ba. An maida Anti Sha’awa gidan mijinta ko kwana bakwai ba ayi ba sai ga goro an kawo wai na tarewar amaryarta rana ita yau. Hajiyar Giyaxe ta ce, uhun ka gani ba? Gajiya yayi da irin qarantarku da kuke mishi, don haka zai yi wa kanshi maganin iya shegen ‘yarku ku kuma kun kama ta kun riqe kuna jira sai yazo, to ba don Yahaya yaje ya bashi haquri yasa an maida ita ba da amarya ta tare ita tana wurin yaji kaga kuma da girma ya faxi. Ko da yake yanzun ma dai sai dai ayi sha’ani. Rannan Mama ta wuni tana zage-zage, tana faxin kaga min ja’iri mara mutunci bai da ko kwabo naja na tsaya na ce sai shi bayan ga mutanen da suka dace a ba su shi ne tun ba a gama fita daga zaman talaucin da ake yi ba zai kwaso wata tsiya ya kawowa mutane? Zubaida ta ce ai sai dai kar a kuma don wannan kam ya riga ya kwaso. Gaba xaya Babana hidimarshi da maganarshi ta zama ta hidimar bikin da ya sanya a gaba na ‘ya’yanshi mata guda biyar, ga kumaxan shi na riqo wato qanin matarshi Ado, wai shima shi ne mai yi mishi komai sadaki da zannuwan aure duka ina jin mama tana cewa wannan kuxi da ka bayar na sayaiyar zannuwan auren Ado ai ba za su yi ba Alhaji, haka fa kayayyakin xakin yarannan da hikima na qarasa yi musu sayaiyar. Inna mai ‘ya’ya uku rus cikin lamarin ba a ko sha’awa da ita hankalinta kuma a kwance hidimarta kawai ta sanya a gaba. Tuni tayi kasafi na abinda zata baiwa kowacce a cikinmu cikin ‘yan kuxinta da cikinmu ya rage mata da suke wurin juyi. Sai dai ni kam ba kayan xaki take shirin saya min ba, don Mama ta riga tayi furuci maganar kuma ta riga ta bayyana har mutane da yawa sunji ta cewar auren nawa da Ado za a yi shi na wata uku ne kawai, watanni ukun suna cika zai sako ni in dawo gida in yaso sai ya nemi wata qalleliyar yarinyar ya aura tunda ma ai kan nawa auren ko me aka yi bai da asara don ko qwandalarshi ba zai kashe ba, Babana ne zai yi mishi komai. Ado ya yarda da wannan qa’ida da Mama ta sanya mishi, ya kuma yi rantsuwar yi mata duk abin da take so akan auren dama kuma kowa yasan shi xin mai yi mata biyayya ne. Bisa wannan dalili ne Inna da ‘yan uwanta suka tsaida shawarar ni kar a saya min komai na kayan xaki ta saya min zinari tunda qadara ce ban da haka kuma zan yi kwalliya. Kwanakin bikinmu sun matso gaba xaya abinda yai saura bai wuce kwana bakwai ba, hidima ta riga ta soma kankama in Mama tayi sammako ta fita tun safe to bata dawowa sai dare, wai tana can wurin hidima. Inna ma dai da bata zuwa ko’ina itama tata hidimar tayi nisa don Hajiya Kubra tana tsaye akan al’amarinta gashi kuma ta tsaya wajen ganin an haxawa Innar gudumowa mai yawa shi kam Alhaji Abba ma shi ta xora wa hidimar gadaje da kujerun su Atika, don haka masu matuqar kyau aka saya. Rannan da hantsi na fita naje gidan Anti Ramla don ita tayi kirana wasu ‘yan dabaru wai take son koya min na yanda zan yi in zauna da Ado, tunda ga abinda ake cewa wai auren na kwana casa’in ne tana gama gaya min abinda zata gaya min xin nayi mata godiya na fito ba wani daxewa nayi ba da barin gida amma abin mamaki da yake an ce wai baya bata kaxan sai nazo na samu yanayin da na bar gidanmu ya canza, ganin mutanen gidan nayi a tsaitsaye kowa sai zare ido yake yi yana rarraba su. Da sauri naja na tsaya ina tambayarsu me ya faru? An yi wani abu ne?ko wani ya rasu ne? shiru sai kallona ake yi na ce ha’a to menene haka? Zan