← Book details Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 22

Sashe 22

Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

son wani xa kwatankwacin son da take yi min ba, haka nan zan ci gaba da rayuwa ta a birnin da na sani, birnin da aka haife ni, birnin da na rayu, zan ma iya komawa Makaranta in yi karatuna tunda ina da wannan burin. Mama kuma in babu auren Ado a kaina ba za ta sake takura min ba don kuwa ba zan sake yarda ba saboda a yau kan ungulu ya riga ya waye xan auren nan da nayi na kwanaki tamanin da bakwai ba qaramin buxe min ido yayi ba. Tuni zuciyata ta shiga kai-kawo mai tsanani na kasa gane menene abin yi? Wanne zan yi? Wane zan bari? Hankalina ya yi matuqar tashi na rasa wanda zan zava cikin niyun Inna da sauran dangi tare da Babana mai faxin bin Ado yana nufin na bar gidanshi kenan zan xauka in bar Ado? Tunda shi Ado ai zai tafi da iliminshi ban da haka ma zan haifar mishi abinda yake cikina yazo ya xauka abin shi, ko kuwa Adon zan bi min soyayyar wata uku muje can qauyen nasu cikin danginshi mu yi zamanmu? Duk yawan kirarin da yake yiwa kan shi na cewar shi xin namiji ne, alhali kuma mu mata mun sha jin iyayenmu mata suna jaddada mana cewar shi namijin ba xan goyo ba ne…?

Mu haxu a littafi na uku jama’a don jin kafin nan in ku ne wanne zaku zava cikin biyun?
Godiya mai xinbin yawa a gare ku bisa qaunar da kuke nunawa rubutuna.
Na gode da zumuncinku, Ubangijinmu Allahu ya sada mu cikin Aljannarsa ta Firdausi don rahamarsa, Ubangiji yasa mu dace da samun dukkan alherin da yake cikin wannan wata mai albarka na Ramadan, watan da Manzon Rahama (S.A.W) ya ce watan Alqur’ani ne.
10/9/1433 Hijira
29/7/2012 miladiya
Taku
Hafsat Chindo Sodangi
07035586299
Chapter 22 · 0% Book details