← Book details Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 22

Sashe 14

Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dashi da lalatacciyar shiga sai yayi maza ya kawar da kanshi ko ya haye kan doguwar kujerarshi ya ja abin ruhuwa ya lulluva ya ce, wai bacci yake ji. Da rana kuma yana Azumi. Cikin zuciyata na ce to ko dai ya tsorata da abinda nayi mishi ne yake ganin kamar a yanzu ma in ya matso kusa dani zan sake maimaita mishi? Gashi Mama ta tasa shi a gaba kullum sai ta shigo gida ta tasa shi a gaba kan sai lalle ya sallame ni, ita auren nawa ya riga ya ishe ta gara kawai a yanzu don in ance sai an kai kwana casa’in to bata san me zamu sake yi mishi ba cikin waxannan kwanakin. Yana faxin kiyi haquri Mama, ba yau ba sai ka ji ta soma rattabo mishi maganganu tana tuna mishi sanda ta xauko shi daga qauye da irin wahalar da yake ciki a wancan lokacin da kawo shi gidanmu da tayi ta maida shi abin da ya zama a yau amma yake nema ya butulce mata saboda aurena. Shi kuwa sai ya ce mata ai ban manta ba, Mama na gode miki da wannan taimako da ki ka yi min ina kuma yi miki addu’ar sakaiya ta gari, ban da haka ma tun kafin kiyi min hakan ke xin uwa ce don haka ne ma a yau bani da wata uwar da ta fiki, to in har hakanne me yasa nake cewa ka sake ta kana qi? Sai ya ce ai shi aure ajali ne dashi in wa’adinshi ya cika sai kaga kamar a mafarki. A wannan lokacin tausayin Ado nake ji, don na tabbatar da daxin komai yake ji ba don gaba xaya al’amuranshi sun sauya, yin su kawai yake yi amma can cikin zuciyarshi ina ganin kamar akwai wani abin da yayi matuqar takura mishi gashi kuma yana dawowa gida daga kasuwa zan ganshi yana wasu abubuwa waxanda shi kaxai yasan me yake yi. A wannan lokacin al’amuranshi da yawa sun sauya, mafi yawancin lokaci a yanzu ya koma shigowa gida ne wajen sha xaya da rabi ko sha biyu duk da ba wata jituwa mai yawa ba ne tsakanina dashi, wannan sabuwar xabi’ar tashi ba daxi take yi min ba, amma nayi kamar ban san me yake yi ba, don kar ya xauka na wani damu dashi. Rannan tun bayan Sallar Magriba ruwan sama ya kece kamar da bakin qwarya, amma Ado bai shigo gida ba da ya idar da Sallar Isha’i, har wajen sha biyu saura kwata na dare, kamar in kulle mishi qofa don in hana shi shigowa xakin in ya dawo, sai naga to na menene yin hakan? Ai kulawama yabawa ne. Da safe ma haka daga sallar Asuba bai sake shigowa ba sai da ya shigo don yin shiri ya fita kasuwa ban ce mishi komai ba, zai kawo cefane in yi girki amma ba zai tambayi nashi abincin ba, in na ajiye ma ba zai tava ba, a zuciyata na ce shima dai zaman namu ya ishe shi hanyoyin rabuwa yake bi wataqila jira yake yi Mama ta sake bashi wani umarni mai qarfi kafin yayi sakin don tasan dai saboda ita yayi. Muna cikin wannan zaman da Ado na kowa ta kanshi yake yi, duk rashin mutuncin da yake tatawa kuma kallonshi kawai nake yi, iyaka dai ina yi ina lissafin kwanakin da suka saura casa’in xin su cika. Ina zaune a tsakar gida bayan fitarshi kasuwa sai ga wayar Inna ta shigo, ina vare-vare cikin yanayin rawar jiki na xauki wayar a dalilin na kirata yafi sau talatin bata amsa ba, Hello Inna salamu alaikum.” Duka gaba xaya na haxa mata saboda zumuxi, bata tsaya amsa gaisuwata ba sai ta soma tambayata ni wane irin zama ku ke yi ne ke da wannan yaron? Da sauri na tambaye ta, wane yaron Inna? Ta ce, mijinki mana, cikin zuciyata nace to itama Inna mijina take kiran Adon? Kafin in soma yi mata bayani kan munanan xabi’unshi da nake shirin gaya mata don in roqe ta ta qara tsaya min da addu’a akan rabuwarmu don ta zo cikin sauqi ba tare da ya cutar dani ba, sai na ji ta soma cewa “kin ga ki shiga hankalinki da ni fa.” Cikin hanzari na tambaye ta me nayi Inna?” Maimakon ta bani amsa faxa ta soma yi mu ma fa da ki ke ganinmu ba ma wulaqanta aure mutuntashi muke yi in miji ya zalince mu, kuma mu zuba mishi ido saboda mun san watarana ba zai yi ba, mu wulaqanci ne kawai ba ma yarda da shi ba kuma mayi wa wani, to amma ke na menene yana iyakar qoqarinshi a kanki kullum sai kin wulaqanta shi, kin ci mutuncinshi, da sauri na tambaye ta, me nayi mishi Inna? Tun bayan wannan abinda ya faru na sake yin wani abu ne? ko shi ya kawo karata wurinki don ya haxa ni dake, kiyi ta fushi da ni? Tunda ai dama can Inna kin sani ba, son mu yake yi ba babu kuma abinda bai yi ba wajen ganin ya taimaka an quntata mana sai kawai nayi ta soma faxin kinci gidan ku na ce miki kinci gidanku da wannan bayanin da kika tsaya kina yi min Inna sake ji an ce min anga mijinki a waje bayan qarfe tara na dare yana zaune to ni dake ne sakarya kawai mara hankali zaku hankatashi ne? Tuni na soma yiwa Inna kuka sosai ita kuwa bata kula da kukan nawa ba faxa kawai take yi, nan da gobe kamar yanzu in ban ji kin xauki matakin gyara al’amari a tsakaninku ba to zaki yi mamakin abinda zan yi akanki ta ajiye wayarta. Kuka sosai na zauna nayi saboda na gane itama Inna a yanzu so take in miqawa Ado kaina bata damu da abinda zai biyo bayan hakan ba bata tsaya nayi mata bayanin da zai fahimtar da ita gane shima adon bai da wani kwaxayi mai qarfi a kaina ba tunda ai nayi mishi tayi na saki shi ne bai kula ba, to sai kuma yanzu da zaman namu yayi matuqar yin xaci bama tsami ba sai ta ce ta bani daga nan zuwa gobe da safe to me take so in yi mishi? Na zauna nan wurin zuciyata sai kake sake take yi ta saqa wannan ta kwance ta saqa wancan ko abincin rana rannan ban yi ba saboda zuciyata a quntace take. Wajen qarfe shida na yamma ya dawo gida, alamar dai daga kasuwa yake don dama lokacin dawowarsu kenan. Ban iya xaga ido na kalle shi ba, saboda raina yayi matuqar vaci da abinda yayi min na haxa ni da Mahaifiyata da yayi, ban tava sanin Inna tana iya fushi dani ba in ban da a ‘yan kwanakin nan a kuma sanadin aurenshi, auren da a farkonshi daga ni har ita qin shi muke yi muna neman tsari dashi har ma ni ce mai danne zuciyata in bata haquri akai, to ko kuma menene yayi mata daxi da auren a yanzu oho? Har bayan Sallar Isha’i ni da Ado babu wanda ya ce wa wani ci kanka, kowa sha’anin gabanshi kawai yake yi, ya fito daga wanka ya sanya kayanshi ya fesa turare kamar dai yanda ya saba yi kullum shirin fita yake yi kamar dai kar in ce mishi komai in bar shi yayi tafiyarshi sai kuma na tuna Inna da kalaman kashedin da tayi min na in ta sake jin an ganshi a waje bayan taran dare zan gamu da ita. A zuciyata na ce uhun in ban da Inna mutumin da ya riga ya mallaki haqoranshi talatin da biyu wanda ba wani ganin juna da mutunci dama can muke yi ba xan gara ma a xan zaman wuri xaya da muka yi shi ne ma aka xan yi wa juna xan alheri a ciki shi ne wai zata yi fushi da ni saboda shi na sani nima wani lokaci nakan xan ji tausayin shi, saboda matsin lambar da yake fuskanta a wurin Mama a kaina. Wacce ita xin kuma da gaske madadin uwa take a wurinshi suna kuma son juna yana girmamata babu wanda yayi zaton zai iya bijirewa umarninta a kaina, to amma duk da haka ina ganin ni an takwaran ace dole ni ce zan nemi shiri dashi ba a daidai kuma lokacin da yake fito min da halaye iri-iri. Qirjina sia harbawa yake yi val-val-val saboda tsananin qin yi mishi maganar da nake shirin yi, sakai yayi ya fita ya miqo hannu zai ja qofar ya rufe a daidai lokacin da na buxe baki na ce mishi ina magana, yaja ya tsaya nuna alamar wai ni yake sauraro. Sai da ya ji ban sake cewa komai ba lokacinne ya sake dawo da kanshi cikin xakin, kin ce kina magana? Ban iya cewa komai ba in ban da hawayen da suka soma zubowa daga idona, shar-shar-shar tanfar dai ba kukan na wuni ina yi ba. Maida qofar yayi a hankali ya rufe sannan ya juyo gare ni, me ya faru Humaira? Baki da lafiya ne? ban iya ce mishi komai ba, babu abin da yake cin zuciyata irin tilasta nin da Inna tayi sai na nemi shiri dashi bayan kuma tasan me hakan yake nufi, ta kuma xiban min qanqanin lokaci na na yin hakan, ganin da na yi ya nufe ni da shirin tava ni ya sani kai gwiwoyina qasa na durqusa ban daina kukan da nake yi ba. Hannu biyu ya saka ya jawo ni jikinshi nayi maza na zame, me nayi miki Humaira? In wani laifi nayi miki yasa ki wannan kukan na roqe ki kiyi haquri, ki kuma gaya min shi don gobe kar in sake yi miki shi. Rarrashin da yayi min ne yasa ni gaya mishi cewar yana haxa ni da Mahaifiyata. Da sauri ya ce min ban tava yin hakan ba Humaira, ai nasan tana sonki ba zan vata ki a wurinta ba, ban da haka ma yaushe ne na soma mu’amalla da ita da har zan je ina kai sukarki wajenta? Me ya faru wanda yasa ki ka ce ina haxa ki da ita? Ban kalle shi ba na ce mishi ta ce ni nake saka yawon da ka ke
Chapter 14 · 0% Book details