← Book details Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 22

Sashe 12

Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nema shi ne fahimtar juna, tsakanina da ke don shi yafi komai a wurina, to amma tunda akwai wasu a bayan fage masu zuga ki to shi kenan na haqura da fahintar zan karvi budurcin in yaso sai fahintar ta biyo baya tunda na gane kin qi yarda mu fahinci junanne don kina ganin in anyi hakan akwai wani abinda zai biyo baya. Gaba xaya na firgita, hankalina kuma yayi matuqar tashi da na gane Ado ya ji wayar da Anti Ramlah tayi min wacce na amsa a kicin ranar da nake yin abincin da aka kaiwa su Hajiyar Giyaxe, jikina yana rawa na ce mishi kayi haquri, bai kalle ni ba ya ce min kema na roqe ki kiyi haquri yau kaxai ai ni kin sha bani haquri ina haqura, don haka nina yau na roqe ki kiyi min haquri. Ganin da nayi Ado bai da shirin haqura nema ma yake yayi amfani da qarfi wajen raba ni da budurcina sai naji gaba xaya hankalina ya tashi, na shiga tunane-tunanen da neme-nemen hanyoyin da zan bi wajen ganin na kuvutar da kaina daga gare shi, ina cikin hakanne wata shawara da Anti Ramla ta bani na kuma yi amfani da ita ta faxo cikin raina. Kar ka taba ni, kashedi mai qarfi nayi mishi cikin tsananin firgita saboda na kai matuqa wajen tsoron abinda zai faru in har bai yarda ya qyale nin ba, bai ji ba baya ma saurarona abinda ya sanya a gaba kawai yake shirin aiwatarwa. A kiqxime cikin tsananin tsoro na shiga miqa hannuna karqashin filo ina lalube kan ka ce meye wannan na jiwo motsin abinda na ke neman wanda na daxe ina voye shi, saboda maganin vacin rana irin wannan na gwada fin qarfi da nuna zalunci da rashin adalci a zahiri. Ado bai ankara ba saboda hankalinshi ya riga ya tafi inda ya tafi, sanda na jawo abin daga qarqashin filo na kuma taqarqare da iyakacin qarfina na kwantara mishi aka. Sai da yayi tsalle kafin ya kai ga faxuwa a qasa cikin wani irin sauti mai tsananin firgitarwa, yana faxuwar ni kuma nakoma na kwanta cikin tsananin gajiya sai haki nake yi, ina maida numfashi a dalilin ya riga ya gajiyar da ni. Ina kwancen ina tunanin in ya tashi me zai faru a tsakaninmu? Ina qarawa gudumar da nayi dukan da ita riqo mai qarfi ta yanda in ya sake tasowa zan sake gunduma mishi ita akan nashi, sai kuma na ji shiru bai motsa ba, shirun yayi min yawa ta yanda har na kasa jurewa, na taso na leqo don ganin wane hali yake ciki. Yana kwance a qasa shame-shame babu alamar numfashi a tare dashi, a firgice sosai na soma qurma ihu da iyakacin qarfina, ina faxin waiyo Ado, waiyo Kawu waiyo ka tashi ka zauna in ganka a zaune ka yafe min wannan muguntar da nayi maka. Nan take wani tunani yazo min da gudu na shiga bayan gida, bokitin ruwan da na fara cin karo da shi, shi na fara jawowa ban yi tunanin yawan ruwan ba na kwara mishi shi gaba xaya cikin tsananin firgitan da ban tava ganin wanda ya yi shi ba. Wani irin firgitaccen motsi yayi da ya qara tsorata ni da gudu na valle qofarnayi waje naje ina dukan qofar su Yaya Ibrahim da kyar suka buxe suka fito. Bayan sun tabbatar ba zan iya hangen abin da ke cikin xakin ba, ke menene haka? Yaya Ibrahim ne ya fara tambayata cikin tsananin kaxuwa na ce musu Ado, ne ku zo ku ganshi Baba ya ce ka ji ‘yar iska wai Ado take ce mishi ko da yake shima maganinshi kenan muje suka taso ni a gaba zuwa xakin, suna ganin halin da yake ciki suka juya da gudu, Mama kawai Mama kawai za ku kashe mata qaninta don kun ga yana ji da ita dama auren haxin baki ne, ni kam na takura wuri xaya in ban da kuka babu abin da nake yi. Suna barin xakin na faxi jikin Ado ina ta faman kuka ina roqonshi gafarar abinda nayi mishi, tsorona kar ya rasa rayuwarshi a sanadin abinda nayi mishi ne ba tsoron abinda Mama zata zo tayi min ba. Ina cikin haka naji kamar an yi min magana, a firgice na ce iye, na’am? A hankali ya buxe baki ya ce min yi maza ki kulle qofa kar Mama ta shigo ta same ki, da gudu naje na kulle qofar na dawo na durqusa a gaban Ado, kuka sosai nake yi yayin da shi kuma yake kwance bai motsa ba lokacin ne na gane tsoratar da nayi ne ya hanani gane ya farfaxo, tun sanda na ji atishawa da hamdala sai nayi zaton ko daga wani wuri ne. Muna cikin haka na ji isowar Mama tana faxin “Lallai yau za’ayi wacce za’ayi, buxe min qofar in ga abin da yake ciki in bai tashi ba ai sai dai in haxa su za’ayi a haxa su gaba xaya in kuma nayi sa’a ya tashi to uwata zata ci gari na wayewa kuma zan tattara ta koma xakin uwarta.” Gwam-gwan-gwan, duka suke yi da iyakacin qarfin su nayi matuqar tsorata don ji nake yi tamfar zasu valla qofar su shigo, don haka na tsallaka can bayan katifar na maqure. Ado ya tashi zaune nayi matuqar qara tsorata saboda ganin da nayi tanfar zai buxe qofar ne saboda yawan kiran da Mama ke mishi “Adamu! Adamu!! In kana nan amsa mana in ji ka.” Cikin qarfin hali ya ce, “Lafiyata qalau Mama, je ki gida kawai sai da safe.” Da kyar ta haqura ta tafi saboda ganin da tayi ya qi yarda da buxe qofar. Har gari ya waye ban tashi daga inda nake takuren ba, yayin da shi kuma Ado ya koma falo ya zauna ban san me yake yi ba sai da na ji an yi kiran Sallar farko ban ga shigowarshi don yin alwala ba, lokacin ne na miqe da kyar na tashi saboda ciwon da jikina nima ke yi min na leqa shi yana zaune ne kan kujera ya kuma kwantar da kanshi akan masagalin kujerar ya kuma xora hannayenshi duka biyu a kan nashi alamar dai ya addabe shi da ciwo. Durqusawa nayi da gwiwoyina duka biyu na ce mishi “kayi haqurin abin da nayi maka.” Da iyakacin gaskiyata haqurin kawai nake bashi ba tare da wani tunani ba, don na riga na tsorata na kuma yi nadamar xaukan wannan mummunan shawara da nayi, na yi amfani da ita da Ado bai farfaxo ba to da wanne hali zan shiga? Ba abinda Mama zata yi ne matsala ta ba, girman laifin ne na tsorata dashi. “Kayi haquri.” Bai amsa ba, bai kuma motsa ba daga yanayin kwanciyar tashi, shiga Masallaci da ya ji anyi shi ne abinda yayi dalilin miqewar shi ya nufi banxaki sai da yayi wanka sannan yayi alwala ya fito yayi raka’atil fijr, sannan yayi sallar Asuba ya idar yana jan carbi nima na idar na shafa fatiha sannan na kalle shi na sake ce mishi “kayi haquri ka ji?” bai kula ni ba. Aka soma buga qofa da qarfi kamar na jiya da daddare, gwan-gwam-gwan. Ya miqe ya buxe, Mama ta shigo da xamarar gyale a qugunta riqe kuma da sharveviyar dorina a hannunta, nayi maza naja can baya na maqure a jikin bango sai faman kaxuwa nake yi, don in ta soma dukana yau ban san wanda zai qwace ni ba, tunda shima Adon bai huce ba daga mummunan abinda nayi mishi. Yau za ki gamu da ni, yau za ki san vakko miya ce in ma uwa ki ce ta turo ki ku kashe min shi to zaku san qarya ku ke yi yau zan yi maganinki ke da iyayenki masu koya miki mugun abu.” Me ya faru Mama? ya yi maganar cikin natsuwa, ta xago ido ta kalle shi kamar zata yi mishi magana sai kuma ta fasa, wataqila don ganin da tayi tanfar vata lokacinta zata yi, don haka ta zabura ta xago bulalar da niyyar sharva min, ni kuma na takure ina sauraron ta inda zan ji saukarta, sai kawai na ji shiru. Mama tayi maza ta waiwaya don ganin abinda ya riqe mata bulalarta ta baya, taga Ado a tsaye da bakin bulalar a hannunshi, sake min bulalata, tayi mishi maganar cikin tsawa, nan da nan yayi hakan tare da faxin na sake Mama, amma kiyi haquri kar ki ce za ki tava ta, ai in mun yi faxa ba rama min zaki yi ba, nima da kaina in kin bar ni zan rama ai ba fin qarfina tayi ba. Ran Mama ya kai matuqa wajen vaci, da ta gane ba zai barta ta buge ni ba, ta shiga zage-zage tana haxawa har da shi a ciki, kiyi haquri Mama, kar ka sake bani haquri, tayi maganar cikin tsawa da fusata, kiyi haquri Mama, ya sake bata haquri. A hankali kuma cikin natsuwa da nuna ladabi har ta xan sassauto tayi kamar zata juya ta fita, muje gida yanzu ina zuwa Mama, kamar ta yarda zata yi hakan sai kawai naga ta juyo da iyakacin qarfinta ta xaga dorina zata sharva min, da sauri ya sake kama dorinar ya riqe, ta sake juyowa tana kallon shi cikin qarin fusata, zaka riqe min bulalar ne kuma? Cikin natsuwa ya sake ce mata, mace a gidan mijinta Mama ya kamata ace tana da ‘yancin walawa, hukuncinta ya zamo a hannun mijinta ne kawai ba wai duk wani wanda ta yyiwa wani abu sai kawai ya zaro bulala ya ce zai buge ta ba, ba tare da ya sanar da mijin ta ba. To ai nan ba gidan ka bane, balle ka ce na mijinta ne, cikin hanzari ya ce haka ne. Mama ta ci gaba da maganganu gidan mijina ne ni naga dama kai da ita ku ke zaune a gidan ita xin kuma ni naga dama ne na ce a baka ita ko nawa ka kashe a cikin hidimar auren? Ya ce, babu, ta ce to babu inda zani yau sai ka rubuta takarda ka sake ta tukunna tunda dama komai akan alqawari muka yi shi da kai, ya ce haka ne to kije gida ina zuwa.
Chapter 12 · 0% Book details