← Book details Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 22

Sashe 19

Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

abinda yasa take yi min daxi ai saboda Hajiya tana can ne. Bai sake yin maganar ba, iyaka dai rannan nasan Ado bai wani yi bacci sosai ba duk da ya saba yin bacci mai nauyi dake baiyanar da alamar gajiyarshi a duk lokacin da al’amura suka afru a tsakaninmu, amma a yau har cikin dare da na farka idon shi biyu na ganshi. “Lafiya baka yi bacci ba?” Ya ce, min lafiya, tunaninki ne ya hana ni yin bacci, ya kamata in samar mana wani wuri da zamu zauna cikin ‘yanci da kwanciyar hankali Humaira, bai kamata ace kowane lokaci kina cikin fitina da fargaba ba, musamman a wannan lokacin da kike da juna biyu.” Juyawa nayi naci gaba da baccina na qi kula zancen nashi saboda bana son kirana mai juna biyu da yake yi. Tun washegarin ranar dai na lura Ado yana yin wasu abubuwa da suka fi kama da lissafe-lissafe da kuma kintse-kintse sai dai da yake gaba xaya al’amarin ya tafi ne kan takardu sai ban maida hankalina wajen neman sanin abin da yake ciki ba tunda dai bai ce min ba sai nima ban tambaya ba. Kwana biyu da tafiyar Hajiyar Giyaxe ina zaune a falonmu ni da Ado in har da wata rana da na soma tunanin lalle juna biyu yana nufin wani abu mai girma da muhimmanci da wahalarwa kamar yanda kullum Ado ke gaya min, to ranar ne don kuwa wuni nayi a galabaice saboda amai, ko abincin rana ban iya girkawa ba balle na dare. Ado ya dawo daga kasuwa da yamma ya same ni a kwance nayi mishi bayanin abinda ake ciki ya ce to abin da nake faxin zai tabbata kenan? Ya sake kallona ya ce min to sannu kin ji Humaira? Na ce mishi to ya sake kallona ya ce min amma in na roqe ki ai zaki iya yi min wani alheri guda xaya ko? Na ce mishi eh, ya ce to wanka nake so kiyi ki sanya min wannan rigar a jikinki in ganta, xazu naje na karvo ta daga wurin xinki in kin iya yi min haka shi kenan don ta rashin girki babu komai, sai in fita in je in nemo mana abinda zamu ci na ce mishi to. Muna zaune da Ado bayan nasha kwalliya cikin sabuwar rigar da ya karvo min daga wurin tela ta xinkin kanfala ‘yar asali, sai kallona yake yi yana murmushi ke kin gan ki kuwa? Ban ce mishi komai ba iyaka dai kawai nima nasan nayi kyau, to me dame kike so in je in kawo miki?na xan rage fara’a kaxan na ce mishi ni dama ka bar ni haka kawai tunda lalurar ciki take ai ba a biye mata…zai ci gaba da yi min magana sai ga Suwaiba ta shigo da gudu, murna take yi farin ciki mai yawa ne ya bayyana a fuskarta wai in ji Baba wai ku zo yanzu-yanzun nan kai da ita. Tana faxin hakan ta juya da gudu ta tafi tanfar dai wata yarinya ‘yar qarama, Ado ya waiwayo ya kalle ni, nima kallon nashi nayi ko lafiya? Na ce ba zan iya sani ba sai mun je mun ji. Nasa hannu na xauki gyalena, ya kalle ni cikin sanyin jiki ya ce ko dai za ki bari ne in je in ji tukuna? Na ce to ai cewa tayi muje tare kar ka je kai kaxai xin kuma ya zama maka laifi, ya ce haka ne to muje. Muna shigowa gida Babana muka fara gani a tsakar gida sai Mama da kuma Innata da ke can wajen bakin qofarta ga dukkan alama kuma kiranta aka yi ta fito. Muna shiga gidan muka tafi qasa don gaida Baba, amma maimakon ya amsa gaisuwar da Ado ke yi mishi sai ya kalle ni ya ce min, ke ga xakin uwarki can tafi ki shiga, kaima ga taka uwar nan jeka wurinta shi kenan kowa ya riqe nashi, magana kuma ta qare dama ita ta ce a baka ita na baka yanzu kuma ta ce ta gano munafurci da raba zumunci in raba na raba magana ta qare kar in sake jin wani ya ce wani abu zan sava mishi. Cikin kaxuwa mai yawa Ado ya ce ka raba min aure Baba me nayi maka? Baba bai tanka mishi ba ya wuce ya shiga wurin Zubaida, ga alama a wurinta yake. Inna ta biyo bayana zuwa cikin xaki don ni kam ma ban wani tsaya jin komai ba, tuni na haye kan gadonta na kwanta sai Ado da Mama ne a tsakar gida, “kin sa Baba ya qwace min mata Mama? Ta ce ka kwantar da hankalinka ai dama ni nasa shi ya baka ita yanzu kuma ba ka san wacce zan sa a baka ba nan da kwana tara ma za’ayi komai tunda na riga na gama komai ai ba zan barka ka zauna haka ba, tunda nasan ka riga ka xanxani daxin mace. Ba ke ki ka bani Humaira ba Mama kaddara ce ta bani ita ba kuma zan rabu da ita ba, ba kuma na son kowace iri za ki sake bani in gidan da ki ke cewa zan bari ne akan zama da ita zan bar shi zan fita daga harkokin da kike cewa zan fitan miki, zan fita daga dukiyar tashi abinda ba a tsammani na zan mayar dashi zan riqe Humaira ne kawai Mama don ita kaxai xin nake buqata a yanzu. Kai Ado, tayi mishi tsawa mai qarfi zaka zage ni ne? yayi maza ya ce ba zan zage ki ba don ke uwata ce amma kuma ba zan yarda ki raba ni da matata ba, Mama ban ga abinda tayi miki ba ina kuma sonta. Ni kuwa ina shiga banxakin Inna na kama aman tun daga falonta har bayan gida da sauri Inna ta biyo bayana tana qoqarin taimakona. Ado kuwa ya juya ya fita ya bar gidan ban san inda ya tafi ba sai dai bai xauki lokaci mai tsawo ba sai gashi ya dawo, kayayyakin ciye-ciye yaje ya sayo min har cikin xakin da nake kwance ya shigo bai saurari maganar da Mama ke yi mishi na kar ya shiga xakin nan ba haquri yake ta bani wai in kwantar da hankalina kar in ce zan xaga hankalina. Nayi murmushi na ce babu komai ni kam ai dama a nan nake su suka xauke ni suka baka ni in sun ce in sake dawowa ba zan zarge su ba don haka kaima kayi haquri, ya ce min to me kike so in kawo miki yanzu? Na ce babu komai kar ka damu ai ga Inna in ina son wani abu zata yi min, ya ce to sai da safe. Tunda Ado yasa kai ya bar gida cikin dare a cewar sai da safe bai sake dawowa ba, babu ma wanda ya ce ya ganshi a unguwar don ina jin Mama tana tambayar ‘ya’yanta sun ga Kawunsu kuwa? Su ce mata a’a Inna ma tayi ta neman shi a waya amma babu layinshi, ya rufe. Ina jin ta tana faxin ni Binta wannan yaro ko ina ya shiga haka oho. Ban dai ce mata komai ba amma ni kaina a cikin damuwar nake don kuwa nasan yana cikin vacin rai mai yawa. Cikin zuciyata dai addu’a sosai nake yi mishi don kuwa ina matuqar tausayin halin da ya samu kanshi a ciki wanda kuma a dalilin aurena ne ko da dai na sani a farkon al’amarin ni suka yi nufin cutarwa, amma hakan ba zai rage min komai a tausayinshi da nake ji ba tunda nima a yanzu ba zan iya cewa ba na son shi ko kuma ban damu dashi ba. Rannan da safe muna karyawa ni da Inna na kalle ta cikin natsuwa na ce mata “Yau kam in Ado bai zo gida ba Inna zan fita in neme shi a irin gidajen abokanshi da muka jejje, ta ce to ya yi kyau kam hakan duk dai ke ma ba lafiya ke gare ki ba, amma abin ai yayi tsanani daga sai da safe abu ya tafi har kwana uku? Muna cikin wannan maganar sai muka jiwo Babana a tsakar gida yana cewa Mama, yaron nan fa Ado ko kasuwa ba ya zuwa, ta ce rabu dashi ja’iri mara kunya da butulci wai shi nan yayi fushi ne a dole ga mai zafin rai ya bar gida, aje a nemo shi in yaso ya samu hanyar cewa sai an mayar mishi da ita sannan zai dawo to yaje duk inda za shi an hana shi itan yafi ruwa tafiya. Inna ta ce uh’uhun abin tausayi yana zaman zamanshi dai aka tsoma shi cikin wannan fitinar da ba a sa shi wannan auren ba ai da yana nan yana harkokinshi da ya saba cikin kwanciyar hankali, kema da yanzu kina naki xakin, shiru nayi ban ce mata komai ba. Sa’adatu ce ta shigo gida da gudu rungume da qatuwar Jakar da kayana yake ciki wanda kayana ne na gida da kayan da nayi biki da su a ciki don tun ina gida nake amfani da Jakar. Hajiya Kubra ce ta bani ita, tana ajiye Jakar a tsakar falon Inna ta sake komawa da gudu na jawo Jakar kusa da ni nasa hannu na buxe ta ina dubawa duk wani abu nawa da naje gidan da shi da wanda ya saya min da kanshi ya tattara min ya saka a ciki har da akwatin sarqoqina don dama yasan in da nake voye su, na miqa wa Inna akwatin sarqoqin tare da yi mata bayani gaba xaya kayana ne Ado ya tattara ya aiko min da su. Ta xan yi shiru cikin tunani kafin zuwa can ta ce duk abinda yayi niyyar zartarwa don ya samar wa kanshi kwanciyar hankali da ya rasa muna yi mishi addu’a ta fatan alheri ba kuma zamu ji zafin shi ba. Cikin zuciyata na ce itama Inna ta hango abinda na hango kenan, cewar Ado zai haqura da aurena ne yasa ya tsintsinto kayana ya aiko min dasu. Muna cikin haka sai ga Sa’adatu tana shigo da kayan kallon shi da ya saya bayan auren mu a dalilin Mama ta ci gadon nashi na samartaka, Inna tayi maza
Chapter 19 · 0% Book details