Sashe 8
Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta gyara tsayuwarta ta ce"Nazifi kana son kanka da arziƙi? To ka taƙaitawa kanka wahala ka sake ni, zan faɗa maka a taƙaice, wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe, ko uwata za ta taso daga ƙabari ba zan koma gidanka ba, ka ga wannan bayanin da na yi maka? Indai ba ka fahimce shi ba, to ba za ka taɓa fahimta ba, ka ga kenan ba ni da lokacin ɓatawa wajen sauraronka".
Ransa ya ɓaci, a ɗabi'arsa shi mutum ne mai saurin fushi, amma yakan danne zuciyarsa idan yana gaban Maryam, ya ce"Ki yi haƙuri Maryam, indai a kan Gwaggo ne ta amince da wannan sharuɗan da kika kafa da farko, za ta dinga girkinta, kuma ta ce ma za ta kwashe kayanta daga kitchen ɗin".
Ta yi wata shegiyar dariya ta ce"Yanzu da kuka ji uwar bari kenan! To sai ka koma ka faÉ—a mata kun makaro, ita dama sau É—aya take zuwa a rayuwa, da ace ka amince tun a lokacin da an yi hakan, amma ka yi sake yanzu auren duka ya fita daga raina, kuma wallahi babu wanda ya isa ya saka ni na ci gaba da yi, don Allah Nazifi idan ba takarda ka zo kawo mini ba kar ka sake zuwa wajena, ni zan fi so ma ka turo min da sakin ta waya saboda ba na son ganinka".
Ganin ya daskare ya kasa cewa komai, sai ta yi tsaki ta shige gidan, ya rasa ma me yake yi masa daɗi, me kuma zai ce mata ta yarda ta koma? Ya lura ita ma babarta ba son ci gaban auren take yi ba, don haka ya yanke ba sai ya sake tuntuɓarta ba, kawai sai ya zauna a ƙofar gidan yana jiran Babanta ya dawo, ya saƙa wannan ya ware wancen har aka kira magriba, ya shiga masallaci ya yi, ya dawo ya zauna, babu jimawa kuwa sai ga Baban ya dawo.
Ya tashi da sauri, ya rusuna yana gaishe shi, Baba ya amsa yana cewa"Kamar Nazifi ko?"
Yana rusunar da kai ya ce"Ni ne Baba".
Baba ya ce"Sannu da zuwa".
Ya ce"Yawwa".
Ya ce"Wajen Maryam ka zo? Ka shigo daga ciki".
Nazifi ya É—an sosa kai ya ce"Ai wajenka na zo, ita mun yi magana tun É—azu, kai na zauna jira".
Baba ya ce"To shigo daga zaure".
Suka shiga, Baba ya shiga cikin gidan ya É—akko tabarma, ya dawo ya shimfiÉ—a suka zauna, Baba ya ce"Wai mene ne yake faruwa tsakaninku?"
Nazifi ya zayyana masa komai, sai Baba ya ji akwai ragi a maganarsa ba kamar yadda Uwani ta faÉ—a masa har da dukan Maryam mahaifiyarsa ta yi ba, ya ce"Sun sanar da ni, to kai yanzu wane mataki ka É—auka?"
Ya ce"Ita Maryam ɗin tun farko ita ce ta ce ta yarda za su zauna da Gwaggo amma kowa ya yi harkarsa, kowa ya yi girkinsa, to da farko ban amince ba, shi ne abin da ya tada tarzomar, duba da ganin mahaifiyata ce, tana da cikakken iko a gidana, kuma ta cancanci mutuntawa daga matata, amma da na ga hakan ya ƙi kawo maslaha sai na ce na amince da sharaɗin nata, ita ma kuma Gwaggon ta amince, amma dai har yanzu Maryam ɗin ta ƙi ta nuna saki kawai take nema".
Baba ya ce"Saki!? Kai ɗan yau ka haife shi ba ka haifi halinsa ba, ka ga ni fa shiyasa ba na saka baƙincikin ɗan yau a kaina, sai su kashe ka a banza, kuma dama Maryam ta fita da ban da ƴaƴan gidan nan, za ta aikata, auren ma da ya ta yi?"
Nazifi ya ce"Sai haƙuri Baba".
Baba ya tashi ya ce"Jira ni kaÉ—an".
Ya shiga cikin gidan ya ƙwalawa Maryam kira, har ta tashi Uwani ta mayar da ita ta zaunar tana tsuke fuska ta ce"Malam lafiya?"
Ya shigo É—akin yana cewa"Uwani wannan wane irin shirme ne haka? Ya za ki É—aurewa yarinya ta samu saken cewa ba za ta koma É—akin mijinta ba?"
Maryam kamar za ta yi kuka ta ce"Baba ni fa wannan zaman ba zai yiwu ba".
Ya ce"A kan me? Ba matsalar babar shi ba ce? Ai ya karanta mini komai, ya ce zai bi sharaÉ—in da kika kafa da farko, ku zauna da uwar tashi ba ruwan kowa da kowa, sai kace wasu facaloli, kai Allah Ya shirya yaran zamani, maza saka hijjabinki ki wuce ku tafi".
Uwani ta ce"Haba Malam don ka ga ba ni na haifi yarinyar nan ba, shiyasa ba za ka ƙyale ni na ƙwatar mata ƴancinta ba?"
Ya ce"Ko wacce kika haifa ce haka zan yi mata, ni ba na ma taɓa sakawa a raina ba ke kika haifi Maryam ba, tun da ba kya wani abu na nuna bambanci, amma kin san wannan zaman nata ba shi da wata fa'ida".
Ya kalli Maryam ya ce"Ba ki tashi kin saka hijjabin ba?"
Ta tashi a zabure kamar wacce za ta kai wa wani duka, tana turo baki da haÉ—e gira ta saka hijjabin ya fita ta bi bayansa, ya ce"Ina akwatin?"
Ta ce"Gobe a kawo mini".
Uwani takaici ya rufe ta, sai take jin kamar da zuciyarta za ta tafi, sam ba ta so hakan ba, so ta yi a yita ta ƙare, auren nan ya mutu a cikin satin nan, duniya ta shaida.
"Maryam!" Ta ƙwala mata kira murya a shaƙe.
Ta koma ɗakin tana share hawayen da ya zubo mata, idan ta tuna haka za ta tsufa cikin bauta da rayuwar ƙunci sai ta ji har gara mutuwa a kan gidan Nazifin.
Uwani ta ja hannunta har ƙuryar ɗaki ta ce"Ba kuka za ki yi ba, ki koma ɗin amma ki ɗaura ɗamarar yi musu gashin ƙuma shi da uwar tashi, kada ki sake ki saurara musu, musamman ita uwar, saboda idan ta ga abun ba na ƙare ba ne, ita ce za ta saka dole ya sake ki, sannan kada ki sake yarda ku haɗa shimfiɗa, idan kuma kin je kin sakar masa jiki kin samu ciki kin ga kanki kika cuta, ki yi zaman zawarci da ciki".
"Ke Maryam!" Muryar Baba ta katse musu tattaunawar.
Wannan karon tare suka fito Uwani tana cewa"Allah Ya ba da sa'a Maryam".
Suka tarar da Nazifi a zaure, Baba ya ce"Tashi ku tafi Nazifi, Allah Ya rufa asiri".
Ya tashi ya naÉ—e tabarmar yana cewa"To Baba na gode, Allah Ya saka".
Ya yi gaba, Maryam ta bi bayansa, sai da suka ɗan yi nisa da gidan suka kusa kai wa titi sannan ya tsaya har ta ƙaraso, saboda su samu damar jerawa.
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
PAGE 6
Yana ɗan murmushi ya ce"Ki yi haƙuri Maryam komai zai wuce in sha Allah!".
Ta yi banza da shi. Ya ce"Ni fa ba nufina kawowa Baba ƙararki ba, da na san ma zai tilasta miki ki koma da ban zo ba, na fi so ki dawo mini ta daɗin rai ba dole ba".
Nan ma dai ba ta kula shi ba, sai ma ƙara sauri da ta yi, yana biye da ita har suka ƙarasa titi, a ranta tana ayyana zai gane kuskurensa na kafewa sai ya zauna da ita, a cikin adaidaita sahu ma da ya kamo hannunta fizgewa ta yi tana aika masa mugun kallo, ya ce"Kin ce abinci kuwa? Ko na tsaya mu siya?"
Ta yi kamar ba ta ji shi ba, sai ya kama kanshi ya ƙyale ta, ya ciro waya ya kira Gwaggo, ya ce"Gwaggo na siyo miki tuwon ko sai na zo na dafa mana wani abun?"
Ta ce"La ai ni yau na yi tuwona, ina ka tsaya ne?"
Ya ce"Ga ni nan a hanya".
Ya ajiye wayar yana kallon Maryam wacce ta haɗe fuska tamkar ba ta taɓa dariya ba, shi mamaki ya ƙi barinsa yadda soyayya take neman rikaɗa ta zama ƙiyayya, sun sauka a bakin titi, sai ya tsaya don ya siya mata wani abun, ita kuwa ba ta jira shi ba ta wuce gidan, a buɗe ƙofar take ta tura ta shiga ko sallama babu, har tana cin karo da kofin sulba da Yasmin ta bari a tsakar gidan, tana jin Yasmin ta ce"Gwaggo kamar wani ya shigo".
Gwaggo ta É—an É—aga murya ta ce"Wane ne a nan?"
Ta ce"Ƙila tumakai ne, je ki kora su".
Haushi ya kama Maryam, wacce ta ja ta tsaya a ƙofar ɗakinta, saboda mukullin yana wajen Nazifin, Yasmin ta fito ta haskata da fitila ta ce"Au!" Sai ta koma ta ce da Gwaggo"Maryam ce fa ta dawo".
Gwaggo ta ce"Au kuma shi ne babu sallama?"
Daga nan Nazifi ya shigo da sallama, Gwaggo ta amsa daga ɗaki, ya ƙarasa wajenta ya miƙa mata ledar hannunsa guda ɗaya, ta kau da kai gefe ba ta karɓa ba, sai ya ajiye su a ƙasa ya ciro mukulli ya buɗe mata ɗakin, ta shiga, ya ɗakko ledar ya ajiye mata ɗaya, ya ɗauki ɗayar ya shiga ɗakin Gwaggo, ya zauna yana cewa"Sannu da gida".
Ta ce"Yawwa, ashe É—akkota ka yi".
Ya ce"E wallahi, kun gaisa?"
Gwaggo ta ce"Ba ta shigo ba".
Ya ce"Bari na kira ta".
Ta ce"Nazifi ba na son tada zaune tsaye, me gausuwarta za ta yi mini? Tun kafin a haife ta ake ta gaishe ni, kuma har yau ban rasa masu gaishe ni ba".
Ya ce"Ki yi haƙuri Gwaggo".
Ta ce"A'a haƙuri ita ya kama ai, ga tuwonka nan" Ta ƙarasa tana miƙa masa kulolin da suke ajiye a gefe.
Ya ce"Bari na yi sallah tukunna, kin ga har an shiga". Ya fito ya yi alwala ya tafi masallaci.
Kafin ya dawo Maryam ta fito ta yi alwala ta yi sallah, ta rufe ƙofarta, ta saka sakata, ta ɗauki ledar, tsire ne a ciki da lemon jarka, ta cinye tass ta sha lemon ta kwanta, tana ta tsara nau'in wulaƙancin da za ta fara aiwatarwa a gidan har bacci ya ɗauke ta.