← Book details Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 23

Sashe 5

Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ta ce komai ba, ta fara haɗawa kanta shayin, sai da suka gama karyawa ya shirya fita aiki, amma ya kasa yiwa Maryam bayanin Gwaggo ba ta amince ba, saboda yadda ya ga ta yi kicin-kicin da fuska, sai janta yake da wasa ta ƙi sauraronsa, ganin sai kame-kame yake yi yasa ta cewa"Wai ni kam ba fita za ka yi ba?"

Ya yi murmushi ya ce"Au korata ma kike yi?"

Ba ta ce komai ba. Ya ce"Maryam kin san dai ina sonki, ina son zama da ke, dalilin da yasa na zaɓi aurenki kenan, to kin kafa sharuɗa na samu Gwaggo amma ita ba ta amince ba, ni sai nake ganin ta fi mu gaskiya, don Allah ki yi haƙuri ki yi yadda ta tsara ɗin, wallahi kamar kin yiwa mahaifiyarki ne lada za ki samu, kuma ni ma za ki samu ƙima da mutunci a idona".

Ta ce"Wato da ba ni da mutunci ko?"

Ya ce"A'a ina nufin za ƙaru".

Ta ce"Nazifi ina ga zan tafi gidanmu sai hakan ya fi kawo masalaha, sai ka auro wata ta zo ta yi mata hidima, matsalar da aka samu fa duk kai ka ja, ka ga ba ka faÉ—a min zaman mutum biyu zan yi ba, dama da ba zan ma fara aurenka ba, don abin da zai yiwu shi ake yi".

Ransa ya ɓaci ya ce"Maryam ina lallaɓa ki ne saboda a zauna lafiya fa, amma na ga abun naki sai gaba yake yi, kin san dai yanzu ni mijinki ne ina da ikon saka ki da hana ki, don haka umarni zan ba ki yanzu, ya zama dole ki kula da mahaifiyata, ki yi mata biyayya, indai kin yarda aljannarki tana ƙarƙashin ƙafata, na ji ita ba ta isa da ke ba, amma ni ai na isa da ke, to ni za ki yiwa ba ita ba".

Maryam kallon shi kawai take yi da maɗaukakin mamaki, don bai taɓa faɗa mata maganganu kai tsaye haka ba, wato yanzu yana ganin tun da ya aure ta zai iya taka ta yadda ya so, bai ma tsaya jiran amsarta ba ya fice, a ransa yana jin babu daɗi, amma dole ya nuna mata muhimmancin mahaifiyarsa.

Ita kuwa yana fita ta kira babarta, ta zayyana mata komai, ta ƙara da faɗin"Ni zan haɗa kayana na taho".

Uwani ta ce"Kul! Kar ki taho yanzu, ƴan gulma sun tashi daga bacci, ki yi haƙuri sai dare, ana sallace sallar magriba ki taho, ba ki ga wajen zama ba Maryam".

Ta tashi ta haɗa kayanta cif a kwati ƴar tsakiya, ta gyara ɗakin ta fito tana wanke-wanke tana jin waƙoƙi a wayarta, tana bin waƙar cikin nuna ko ajikinta, wani jinta take a sama ta yadda take jin tana da gatan da ba za ta ɗauki raini daga wajen kowa ba, ta gama ta shiga kitchen ta tattaro kayan gararta danginsu cincin da dubulan ta kawo su ɗaki, tana ci tana chart har sha ɗaya ta yi, sai ga ɗan aike da ledoji wai ga shi inji Nazifi, ta buɗe ta ga ledar farko kayan miya ne da nama, sai kuma garin masara da na alkama, ta yi wani murmushi na takaici ta ɗauki ta kayan miyan ta kai kitchen ta garin kuma ta je ajiye a ƙofar ɗakin Gwaggo, ta koma ɗaki ta ci gaba da harkokinta, sai sha biyu da rabi da Yasmin ta dawo daga makaranta, ta ci karo da kedar, tana buɗewa take cewa"Gwaggo wannan ledar fa?"

Gwaggo ta ce"Leda kuma?"

Yasmin ta ce"Ai garin tuwo ne ma, kuma kika ajiye a waje?"

Gwaggo ta fito tana cewa"Garin tuwo kuma? Sai ta ƙwalawa Maryam kira, ta fito tana ɗaura ɗan kwali, Gwaggo ta ce"Wnnan fa na ga an ajiye a ƙofar ɗaki?"

Maryam ta ce"Ƙila ɗan aike ne ya kawo".

Ba ta jira cewarta ba ta koma É—aki, tana jin Yasmin tana tambayar me aka dafa?

Gwaggo ta ce"Shiga kitchen É—in ki duba" Ta koma É—aki tana mamakin kalal surukar da Allah Ya haÉ—ata da ita.

Maryam tana jin ƙarar buɗe kitchen ta fita, ta samu Yasmin tana buɗe-buɗe, ta haɗe rai sosai ta ce"Ke ƙalau kuwa? Uwar me kika ajiye da za ki ɗauka?"

Yasmin ta ce"Ba dai uwata ba".

Mamaki ya kama Maryam ta ce"Zaginki na yi? To na zage ki É—in uwarki da ubanki! Na fi ki iya rashin kuya, a fagen nan ke jikata ce ba Æ´ata ba, fice ko na kikkifa miki mari!".

Yasmin ta fita tana kwarara ihu kamar wacce aka cirewa ido, Maryam ta fara kwashe kayan abinci na gararta tana kaiwa É—aki, har ta gama Yasmin ba ta fasa ihu ba, Gawaggo kuma ba ta fito ta ce komai ba, tana zaune sai ga kiran Nazifi, tana É—agawa ya ce"Amma Maryam sai da na faÉ—a miki babu ruwanki da yarinyar nan, akan me za ki dakar musu Æ´a?"

Ta yi tsaki ta kashe wayar, saboda ba ta da lokacin tsayawa faɗa musu ba ta kai ga dukanta ba, abu ɗaya da ta sani dai shi ne auren nan ba mai yiwuwa ba ne, dole a kira ta da ƙaramar bazawara, don ko miji bai isa ya saka ta ciwon kai ba, ballantana kuma uwarsa da wata ƴar tsakuwar jikarta.

Ya yi ta kira ba ta É—aga ba, hakan ya sa ya taho gidan don kukan da ya ji Yasmin tana kurmawa ta waya da yadda Gwaggo take ta masifa ya tada hankalinsa.

08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 4

Yana shigowa gidan ya shiga ɗakin Gwaggo, da yake Maryam ta ji sallamarsa sai ta tashi ta fito, ta je ta laɓe tana sauraron su, Gwaggo tana ta tsara masa son ranta kamar a gabanta aka yi, sai da ta ji ya ce"Ki yi haƙuri don Allah Gwaggo bari na je na same ta". Sannan ta yi wuff ta shige ɗakinta, ta haɗe rai tana jiran ta ga ta inda zai fara, ya shigo da sallama, ransa a ɓace yake da abin da ta yi, amma sai ya kasa karaɓus saboda yana son Maryam, ya zauna a sanyaye ya ce"Maryam don Allah ki rufa mini asiri ki fita daga harkar yarinyar nan".

Ta ce"Na fita daga harkarta fa ka ce, kamar dai wata sa'ata, yarinyar da a haihuwar kaji na haife ta amma ta yi yunƙurin zagina..."

Ya katse ta da faɗin"To kin ji ke ma yunƙuri kika ce, ba ta zage ki ba, a kan me za ki dakar musu ƴa?"

Ta ce"To shi yunƙurin ba raini ba ne? Ai wallahi inda ta zage ni sai bakinta ya yi jini, kuma ni fa ban dake ta ba, sharri ne kawai ta so ƙullawa, kuma sai dai ya ƙare a kanku don yau zan bar muku gidan".

Ya yi murmushi ya ce"A haba, da wasa kike yi, babu inda za ki tafi ki bar ni".

Ta ce"Wallahi Nazifi da gaske nake, ba zan iya ba, bari na faɗa maka gaskiya inda na san haka zan samu gidanka da ban aureka ba, a ce daga aure sai saka ni ɓacin rai ake yi?"

Ya ce"Ki yi haƙuri don Allah! Komai zai daidaita in sha Allah, kuma ke ma fa har da laifinki, kin ƙi kwantar da hankalinki, yau da wuri zan shigo mu sha shagalinmu amaryata".

Ta taɓe baki, don ba ta da lokacin ɓatawa wajen nuna masa dole yau za ta tafi gida.

Ya ce"Kin yi girki? Na aiko cefane za ki iya yi mata tuwon yau ko sai gobe? Kin ga cikinta ita kaÉ—ai ne ko kaÉ—an ne kin ji Sweety".

Takaici ya kamata, ta kwanta tana cewa"Don Allah ka tafi harkarka".

Shi ma ya kwanta kusa da ita yana cewa"Ba zan tafi ba, kin ga yi haƙuri tashi mu shiga kitchen ɗin tare sai na taya ki".

Ta ce"Wallahi Nazifi ba zan yi tuwon nan ba".

Zai yi magana suka ji Gwaggo tana ƙwala masa kira, ya tashi ya fita jiki a mace.

Gwaggo ta ce"Nazifi tun da ka zaɓi matarka ta huta ni na wahala to mu je ka koya min yadda ake kunna gas ɗin, sai na ɗora".

Ya ce"Haba Gwaggo za ta yi, duk fa ba yadda kike tunani ba ne, kin san Maryam tana da aljanu shiyasa wani abun sai an yi mata uzuri".

Gwaggo ta ce"Allah Ya sa tsamiya ce a kanta, wa za ta faÉ—awa aljanu? Ni da nake da guda saba'in a kaina na gado, zaman gidan nan fa idan ba zai yiwu ba tun wuri ka faÉ—a min na koma inda na fito".

Inda za ta koma ɗin tabbas da zai ji daɗin hakan, amma ba zai iya nuna mata yana so ta tafi ba, don haka ya ce"Ki yi haƙuri Gwaggo, bari na samo miki tuwon, gobe sai ta dafa miki".

Bai jira cewarta ba ya fita daga gidan. Ya siyo mata tuwon ya kawo ya koma kasuwarsa, ba tare da ya sake shiga É—akin Maryam ba.

Can da magriba Maryam tana sallayar da ta idar da sallah ta jiyo hayaniyar Gwaggo tana cewa"Wallahi Yasmin idan fitina za ki yi sai ki bar gidan nan, ga tuwo ki ce sai kin yi girki, alhalin ba iya kunna gas É—in kika yi ba?"

Yasmin ta ce"Wallahi na ga yadda ake kunnawa, idan na kunna sai ki dafa min indomin don Allah, idan kuma so kike na kwana da yunwa shikenan".

Gwaggo ta ce"Rufa min asiri na mutu babu hakkin kowa a kaina, ungo siyo ashanar, don wannan matar ƙila ɓoyeta ta yi".

Maryam ra ƙufula, sanda ta fito Yasmin har ta fice, tana dosar kitchen ɗin ta fara jiyo ƙarar gas ɗin shuuuu alamar ta kunna shi, kuma wai ta tafi siyo ashana, a ranta ta ayyana lallai dole dai ta bar gidan nan, don ba ta shirya mutuwa ba, ta kashe gas ɗin ta fito ta ja ta tsaya a ƙofar kitchen ɗin.
Chapter 5 · 0% Book details