← Book details Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 23

Sashe 10

Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa Maryam kamar wata makauniya kuma kurma haka ta koma kitchen ɗin ta fara sharewa, ta gama ta zo ta wuce ɗaki, har lokacin Gwaggo tana tsaye mamaki ya daskarar da ita, ta jinjina ki ta shiga ɗaki ta zauna jaɓar, saboda ba za ta iya ƙarasa sharar ba, a ranta tana ta tunanin wace irin mara kirki Nazifi ya kawo cikin rayuwarsa?

Yasmin ta ce"Ruwa fa ta watsa miki Gwaggo".

Gwaggo da zuciyarta take a kumbure ta ce"Babu komai Yasmin".

Ta shiga haÉ—a kayansu, ta É—auki waya ta kira lambar babban É—anta Shazali, suka gaisa ta ce"Don Allah zan iya samun É—aki a gidanka ko na sati É—aya ne?"

Ya ce"Gwaggo kamar ya? Mai zai hana? Ai ke kika ƙi tun farko".

Ta ce"To ga ni nan zuwa".

Ta ajiye wayar, tun da Shazali ya gina gidansa ya ware ɗaki ɗaya har banɗaki ya yi a ciki ya ce nata ne, amma ta ƙi zama saboda tunanin Nazifi bai yi aure ba ba za ta koma wani gidan ta bar shi ba, kuma ba za ta so ya koma gidan yayan nashi da zama ba, daɗin daɗawa ita ba ta son nisa da Nazifin ta fi son zama a gidansa, saboda shi ya fi kwanta mata a zuciya duk cikin ƴaƴan nata, ashe hatsabibiyar matarsa ba za ta bari burinta ya cika ba. Ƙatuwar akwatin kawai ta ɗauka, ta rufe ɗakin suka tafi, Maryam tana leƙe ta gefen labule ta ga sanda ta ja akwatin suka fice, ta yi wata shegiyar harara tana cewa"Da kika ce za ki jure!".

Bayan sallar magriba Nazifi ya dawo daga kasuwa, da mamaki ta fara cin karo, na ganin ƙofar ɗakin Gwaggo a rufe, ya san ko ba ya nan idan za ta je unguwa tana faɗa masa, ya kalli ƙofar ɗakin Maryam ya gan shi a buɗe, sai ya ƙarasa ya ɗaga labulen, tana zaune tana chart, ya ce"Maryam unguwa Gwaggo ta tafi?"

Ta ce"Dama ajiyarta ka ba ni? Ko ita ƙaramar yarinya ce da zan saka mata ido a kan shige da ficenta?"

Ya ce"Ke dakata! Maryam kin fa fara fusata ni a kan mahaifiyata, wallahi kar ki yarda ki kai ni bango!" Ya yi ƙwafa ya saki labulen.

A tsakar gidan ya tsaya ya kira lambarta, ta É—aga ya gaishe ta kafin ya ce"Gwaggo unguwa kika je ne?"

Ta ce"E Nazifi ina gidan shazali".

Ya ce" Ba ki taho ba? Ba na son kina kaiwa dare a waje".

Ta ce"Ai a can zan kwana, gobe idan Allah Ya kaimu sai ka haÉ—o sauran kayana ka kawo mini nan É—in, don hakan zai fi".

Gabansa ya faÉ—i ya ce"Gwaggo me hakan yake nufi? Me ya faru?"

Ta ce"Idan ka zo goben ka ji".

Ta kashe wayar, ya kasa zama, ya fice daga gidan yana fatan Allah Ya sa ba Maryam ce ta yi mata wani laifin ba.

Ya shiga gidan, suka gaisa da matar yayan nasa, a tsakar gida ya tarar da yara suna cin abinci, Yasmin ta yi farat ta ce"Yaya Nazifi ka dawo? Mun dawo nan da zama, matarka ce ta watsawa Gwaggo ruwan wanke-wanke, ta hiƙewa jagab!"

Wani tashin hankali ya rufto masa, ya ce"Ruwan wanke-wanke!?" Yana zazzare ido kamar yarinyar ce ta yi masa laifin.

Ya shiga É—akin da aka ce masa Gwaggon tana ciki, tun kafin ya zauna ya ce"Gwaggo da gaske ruwa ta watsa miki?"

Ta ce"Zauna Nazifi".

Ya ce"Ina zuwa".

Ya fice daga gidan cikin sauri, a hanya sai ya kasa haƙuri, kawai ya ciro wayarsa ya rubutawa Maryam gajeren saƙo "Na sake ki saki ɗaya".

Tana cikin chart ta ga shigowar saƙon, gabanta ya ba da rass, kafin kuma farin ciki ya biyo baya, ta tashi ta zauna ta ƙara tashi, ta ma rasa me za ta fara yi, ta ina za ta fara haɗa kayan? Sai ta kira lambar babarta a waya, tana ɗagawa ta ce"Albishirinki!" Ba ta jira amsarta ba ta ce"Ya gaji ya sake ni!".

Uwani ta miƙe tsaye cike da farinciki ta ce"Alhamdulillah! Ƴata ta rabu da ƙaya ta samu ƴancinta, maza tashi ki haɗa wata akwatin, dama ga wata a nan, gobe tun safe za a siyar da kayan ɗakin nan".

Maryam ta ce"Ina sha Allah! Wallahi sai na ji kamar an cire mini wata ƙaya".

Uwani ta ce"To ai irin wannan auren sartse ne, idan kika rabu da shi dole ki ji haka".

Ta ajiye wayar ta shiga haÉ—a kaya.

08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 7

A zuciye sosai Nazifi ya ƙarasa gidan, ko sallama bai yi ba ya banka ɗakin Maryam, ba ta ɗago ta kalle shi ba ta ci gaba da aikinta ranta fess, ya ce"Ke Maryam akan wane dalilin kika watsawa babata ruwan ƙazanta?"

Ta ɗago tana hararar shi cike da tsiwa ta ce"Ƙila tare mini hanya ta yi".

Tass! Ya ɗauke ta da wani zazzafan mari, ta tsaya tana mamaki ya ƙara sauke mata wani, yana nunata da yatsa a fusace kamar zai tsokane mata ido ya ce"Wallahi uwata ta fi kowa a wajena, ke ba ki kai wacce za ta wulaƙanta uwata ba, duk duniya ma babu indai ina raye ina kuma da ikon rama mata..."

Ta katse shi da faÉ—in"To ai ba ka rama mata ba, wanke-wanke za ka yi ka watsa mini ruwan na yi tsumu-tsumu kamar an tsoma kaza a ruwa shi ne zan san ka rama mata".

Tana rufe baki ya naushi bakin nata, ya ce"Wallahi ni dai na yi asarar kuÉ—i da lokacina wajen aurenki, maza ki tattara gayyar tsiyarki ki bar mini gidana".

Har ya juya zai tafi, sai kuma zuciya ta ciyo shi, ya tuna yadda ya dinga sintiri a ƙofar gidansu yana yi mata wahala, yana yi mata ladabi kamar uwarsa, ya tuna kuɗin da ya kashe a kayan lefe, da shagalin bikin, da ya san wacce zai aura ai da a kasuwa ya saka kuɗin ya ƙara jari ya ciji leɓe, sannan ya dawo kamar an jeho shi, tana duƙe tana haɗa kaya, ya yi mata wani dundu a bayanta, sannan ya rufe ta da duka ta ƙo'ina yana cewa"Wallahi sai na daki kuɗina, ƴar wahala wacce ba ta san halacci ba!".

Maryam ma ta taso tana kai masa duka daidai iya ƙarfinta, sai dai ƙarfin ba ɗaya ba ne, idan ta dake shi ma ita ce take jiggata hannunta saboda ƙaƙƙarfan ƙashi kawai take duka, don haka cikin ƙanƙanin lokaci Nazifi ya yi mata lilis ya tara mata gajiya, fuskarta kuwa har ta kumbura, dama naushin da ya yi mata bakinta ya fashe, bai bi ta kan ashar ɗin da take ƙundumawa Gwaggo ba, ya fice daga gidan, saboda idan ya biyewa zuciya sai ya kashe ta, tun da ta lura bakinta ba zai yi shiru ba.

Kuka sosai Maryam ta ci kafin ta saka hijjabi ta tafi gida, don fasa haɗa kayan ma ta yi, yana daga runfar maƙotansu a zaune, dama jira yake yi ta fice ya zo ya rufe gidan, sai da ta yi nisa sannan ya shiga, sai ya ga kayan duka a baje ba ta haɗa ba, nan ya yi tozali da tarin kayan lefen da ya haɗa mata, zuciya ta faɗa masa ya ragewa kansa zafi a kansu, ai kuwa ya ɗauki atamfofi guda biyar, leshi guda biyu, ya kwasarwa Yasmin kayan kwalliya, sannan ya rufe ɗakin ya tafi gidan Gwaggo, a hanya ya tsaya ya samu leda ya zuba kayan, ya zauna a gaban Gwaggo cike da kunyar abin da matarsa ta yi mata ya ce"Gwaggo don Allah ki yi haƙuri, na ja miki tozarci, wallahi inda na san haka za ta faru da tun farko ma ban yi auren nan ba".

Gwaggo ta ce"Ba komai Nazifi, kowa da irin halinsa, ba ga shi na bar mata gidan ba? Yanzu sai ku zauna lafiya".

Ya ce"Haba Gwaggo, ai ko ita ta gwal ce wallahi ba za ta yi miki wannan abun na iya ƙara kwana ɗaya da ita ba, na sake ta".

A ranta ta ji daɗin yadda ɗanta ya nuna tana da muhimmanci a wajensa, ta ce"Na gode Nazifi, Allah Ya shi albarka, amma da ba ka rabu da matarka ba, tun da na tafi ƙila ku ci gaba da zaman lafiya, dama fa ba lallai ne sai matarka ta so danginka ba, wata nagartar tata za ka duba sai ka yi haƙuri da wani halin nata".

Ya ce"Haba Gwaggo ina nagarta ga wacce za ta iya wulaƙanta mahaifiyarka? Ba fa zama za ki yi a gidan nan ba, kin ga idan sun gama kwashe kayanta sai ki koma, ba na son su zo wani ya ganki ya zage ne, amma da a yau ɗin za ki koma, gara na haƙura da auren matuƙar za ki zauna lafiya".

Ta yi murmushi ta ce"Ai ba duka aka taru aka zama É—aya ba,nan gaba sai ka ga ka samu wacce za ta bi ra'ayinka".

Ya ce"To Allah Ya sa, ga wannan kayan Gwaggo kya É—inka".

Ta karɓi ledar da ya miƙo mata, tana cewa"To daga ina kuma? Na ga sallah da saura".

Ya ce"Na lefen yarinyar nan ne, na kwaso saboda na rage asara".

Gwaggo ta yi ƴar dariya ganin yadda ya yi maganar bil haƙƙi, ta ce"Nazifi kenan, idan ka yi wani abun sai ka ce yaro ƙarami, yanzu dai ka san wannan wata fitinar ka siyo ko? Lefenta ai haƙƙinta ne ka je ka mayar mata, ni ba yafe".

Zai yi magana ta É—aga masa hannu ta ce"Ka je ka mayar".

Ya ce"To".

Daga nan suka shiga fira, ta ba shi abinci ya ci, sai tara da rabi ya koma gida, washegari da safe ya haɗa kayan shi ya saka a ɗakin Gwaggo ya kulle, ya ɗauki kayan da ta ƙi karɓa ya tafi da su kasuwa, sai ya bawa wani mai kanti dake kusa da su mukullin gidan, ya ce idan wasu sun zo ya ba su.
Chapter 10 · 0% Book details