← Book details Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƴarta Mardiyya da take kwance tana shirin yin bacci ta ce"Haba babarmu! Yanzu Maryam ɗin da aka kai yau kowa yana murnar ta yi aure kike cewa ba ta samu gidan zama ba? Me ta ce miki?"

Uwani ta ce"Maryam ki kwanta kin ji, gobe za mu yi waya, akwai Æ´an sa ido a É—akin" Ta kashe wayar tana tsuke fuska.

Mardiyya ta tashi zaune tana cewa"Wai me ta kira ta ce miki?"

Uwani ta ce"Mardiyya ba na son shiga shara ba shanu, ina ruwanki ne?"

Mardiyya ta ce"Gaskiya da ruwana! Ya za a yi a ce awanni da kai ta ɗaki har ta fara kiranki tana kawo miki ƙorafi? Ke kuma ai bai kamata tun yanzu ki ce mata ba ta samu gidan zama ba, ki duba ki ga fa duk mun yi aure sai ita kaɗai a gidan nan, ana ta murna ita ma ta yi kuma sai ki ƙi ƙarfafarta ta zauna? Me yafu ma wai?"

Uwani ta ce"Mardiyya me kike nufi ne? Na fa fi ku damuwar ganin Maryam ta yi aure ta zauna, gani na yi kamar ba ta yi dace na, wai ashe wannan É—akin da kuka ce ya ce ban da shi a jere babar shi ce za ta dawo ta zauna".

Mardiyya ta ce"To sai me? Ita Naziyya da take zaune da uwar mijinta a gida É—aya mene ne ya same ta?"

Ta ce"Babu komai, amma ita ai kin ga kowa da ɓangaren shi, ita kuwa Maryam ga ɗaki ga ɗaki fa suke, suna shaƙar numfashin juna, a kan idonta fa za su shiga wanka su fito, ko leda ya shigo da ita idonta a kai, to kuwa ina za su more amarci?"

Mardiyya ta yi ƴar dariya ta ce"Ta ina za su shaƙi numfashin juna kamar a ɗaki ɗaya za su kwana?"

Uwani ta ce"Ke dalla can rufe min baki, ku da ba ku san komai ba".

Mardiyya ta koma ta kwanta tana cewa"Allah Ya kyauta".

A ɓangaren Maryam amarya haka suka kwana tana tunanin irin zaman da za su yi da mahaifiyarsa, da yake babu nisa tsakanin gidansu da gidan su Nazifi ta san mahaifiyar tashi, sai dai taƙaimaimai ba za ta ce ga halinta ba, tun da su kaɗai ne a gidansu ballantana wani ya ga wani halin nata mara kyau, ita dai ta saka a ranta babu ruwanta da babar shi tun da ba a kanta za ta zauna ba, kowa ya yi ta kansa, sai dai fa ba za ta ɗauki raini ba, duk abin da ta ga an yi mata ba daidai ba ba za ta yi shiru ba, don gidan aurenta ne tana da cikakken ƴancinta, Gwaggo ta ja girmanta ita ma ta ja ƙanƙantarta. Haka shi ma Nazifi ya kwana da tunanin Allah Ya ba su zaman lafiya da mafimtar juna a zaman su da Gwaggo, yana son Gawaggo yana son Maryam don haka dole zai yi wa kowa adalci don ganin sun zauna lafiya.

Washegari da safe suna cikin karyawa sai ga kiran Gwaggo, ya É—aga suka gaisa ta ce"Nazifi ka manta da mu ka tafi aiki ne?"

Ya ce"A'a ina gida yanzu dai zan fito".

Ta ce"Ikon Allah! Yanzu ƙarfe tara kana gida Nazifi? Daga yin auren jiya za ka watsar da aikinka kenan? To ni dai na shirya ina jiranka".

Ya ce"To ga ni nan zuwa".

Maryam tana jiyo sautin muryar gwaggo da tattaunawarsu, ta jinjina kai kawai tana ayyana lallai wannan tsohuwar a tsaye take, to ai kuwa muddin tare za su zauna dole sai ta zaunar da ita, zaman dirshan ma kuwa.

Bayan ya fita ta wanke kofunan da suka ɓata, ta share gidan ta koma ɗaki ta kwanta, sai ga sallamar Nazifi tare da Gwaggo tana cewa"Gafaranku dai!".

Maryam ta tashi zaune tana taɓe baki, tana ji suna ta shiga da kaya ɗakin nata, ba ta fito ba sai da ta ji an buɗe mata kitchen, ta fito tana ɗaura ɗankwali da rarraba ido, Gwaggon ce ta buɗe har ma ta shige, kamar ta bi ta sai dai ta daure ta koma falo ta zauna, Nazifi ya shigo yana cewa"Maryam ki fito ku gaisa mana".

Ta ce"Ai za mu gaisa ita da ba yau za ta tafi ba, ba gobe ba, gaggawar ta mene ne?"

Ya ce"Hakane".

Ta ce"Na ga an buÉ—e min kitchen? Me ake nema?"

Ya ce"Tukwanenta da kwanuka ta ajiye".

Ta ce"Ok".

Ya daÉ—e da fita sannan ta fito ta shiga É—akin Gwaggon, ta yi sallama Gwaggo ta amsa tana yi mata kallon tsaf, Gwaggon irin uwayen nan ce masu kishin É—ansu haka siddan, kuma haka kawai ta ji Maryam ba ta yi mata ba, saboda rawar jikin da Nazifi yake yi a kanta, Maryam ta gaisheta, ta amsa babu yabo babu fallasa, ga jikar tata a kusa da ita, wacce take ta kallon Maryam É—in ba tare da ta gaishe ta ba, yarinyar za ta kai shekata tara, a ganinta ai ta san gaida manya, ta tashi za ta bar É—akin Gawaggo ta ce"To mu fa ba mu karya ba muka taho".

Maryam a zuciyarta ta ce'To zumuɗin uban me kuke yi?' A fili kuma ta ce"To" A daƙile ta tashi ta fita tana tura baki gaba, saboda ita fa gani take takura ne zaman uwar shi a gidanta, shayi ta dafa dama biredi biyu ya shigo da shi jiya, ta kai mata ta ajiye ta fice, ta same shi yana shirin fita, ya ce"Zan fita, zan aiko da cefane, sai ki dafa da ɗan dama tun da ga Gwaggo kuma na san za a yi baƙi ma ko?"

Ba ta ce komai ba, har ya gama shirinsa ta ce"A dawo lafiya".

Yana fita ta É—auki waya ta kira babarsu, sun gisa ta ce"Ya kuka kwana?"

Maryam ta ce"Lafiya ƙalau, amma fa kin ga tsohuwar nan har ta dawo, ta jera kayanta, wai abun takaici har kitchen ma haɗawa za mu yi, haka ta kwaso jiki don sauri ko karyawa ba ta tsaya ta yi ba".

Uwani ta rafka salati da sallallami kamar wacce ta ji mutuwa ko tashin hankali ta ce"Har ta dawo gidan, kenan amarcin ma a gabanta za ku ci!? Maryam wannan wane irin gidan aure kika faÉ—a, anya ba za ki yi bore ba kuwa?"

Maryam ta ce"Bari dai na ga yadda zaman zai kasance, idan na ga ba zan iya ba wallahi sai dai na bar mata gidan, yanzu ma har yana cewa ba yi girki da yawa, ga baiwa an kawo musu".

Uwani ta ce"To ai shikenan, idan dai kin ga da matsala kar ki yi shuru ki cuci kanki, aure irin wannan da aka fara shi da matsala babu inda yake zuwa, idan kuwa kin ga ya yi nisan zango to tabbas durƙushe matar aka yi, irin matan da suke ɗaukar miji kamar rayuwarsu, ke kuwa daraja da ƙimarki ta fi gaban nan wallahi, ƴata wanke hannu ka taɓa ce ta wuce zaman haƙuri a gidan miji wallahi".

Maryam ta ji daÉ—in maganganun babarta mai sonta, tana murmushi ta ce"Zan dai ga take-takensu tukunna".

Uwani ta ce"Yawwa, kuma kin san su iyayen miji idan kika nuna musu ke mai haƙuri ce da biyayya to fa tamkar kin ce musu ke bola ce a zuba miki kowace ƙazanta, wallahi ke ce ƴar iska a idonsu, don haka idan ta yi miki kallon yamma ki yi mata na arewa, wannan cewata ce".

Maryam ta naÉ—e huÉ—uba tass a kanta, suka yi sallama, ta É—akko kazarta ta jiya da ba ta ci ba ta fara ci. Wajen sha É—aya babarsu ta aiko mata da sauran kayanta, da kuma kula fal da jar miya wacce ta ji nama, shi ma Nazifi ya aiko cefane, sai ta soya naman da ya kawo ta ajiye ta dafa taliya ta É—auki wata kula cikin tarkacen kayan Gwaggon da ta ajiye a kitchen É—in ta zuba mata, ta yi sallama ta kai mata, tana ajiyewa Gwaggo ta buÉ—e ta ce"Kuma kya zuba miyar a kai?"

Maryam ba ta ce komai ba ta fice daga ɗakin, har zuciyarta take jin haushin matar kuma daidai take da zamaninta, dayake tana ta yin baƙi taliya leda uku da ta dafa ta ƙare, dab da magriba ta dafa macaroni leda ɗaya, ta raba gida biyu ta zuba mata rabi ta bar wa Nazifi rabi, don ita ba ta jin yunwar ma, da ta kaiwa Gwaggo ta buɗe ta gani, sai ta tura kular gefe.

Ana idar da sallar isha'i Nazifi ya dawo gidan, da ledojinsa biyu, ya siyo musu balangu da biredi ne, ya fara shiga É—akin mahaifiyarsa da sallama, ta amsa tana yi masa sannu, ya ce"Yawwa sannu Gwaggo, ga wannan".

Ya miƙa mata biredin da balangu, ta buɗe ta ce"Allah Ya amfana, dama ban ci komai ba".

Da mamaki ya ce"Ba ki ci abinci ba Gwaggo?"

Ta taɓe baki ta ce"To ka san ni ba cin kayan basir ɗin nan nake yi ba, da rana ta dafa taliya, da daddare ta dafa macaroni, ni gaskiya ba zan iya wannan rayuwar ba, gara ma tun wuri ka auno garin tuwo, idan ba za ta ci ba ni ta dinga dafa mini, na fi gane na ci tuwona idan zan kwanta, da safe na ci ɗumame".

Jikinsa ya É—an yi sanyi, ya ce"To babu damuwa in sha Allah gobe zan siyo, amma dai yau É—in ki daure ki ci macaronin".

Ta ce"To bari na gani".

Ya fita ya shiga ɗakin Maryam, tana kwance tana kallon hotunan biki a wayarta, ya sakar mata murmushi ya zauna a kusa da ita cike da shauƙin sonta, yau dai ta karɓe shi sun sha amarcinsu, sanda suka fito suna alwala ma sai da Gawaggo ta leƙo ta ce masa"Alwalar me kuke yi? Me kake yi a waje ba ka yi sallar isha'i ba?"

Cike da kunya ya ce"Na yi sallah Gwaggo kawai dai zan kwanta da alwala ne".

Ta taɓe baki ta koma ɗaki, haka da komai ya wakana ya ji kunyar fita yin wanka, sai ya bari sai tsakar dare sosai sannan ya fita ya yi, kuma ya yi taka-tsan-tsan sosai wajen zubar da ruwa ta yadda ba sosai za a jiyo ƙara ba, bai saka a ransa Gwaggo za ta saka musu ido ba, kawai dai shi ne yake jin kunya.
Chapter 3 · 0% Book details