← Book details Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ga Yasmin ra dawo da saurinta, ta yi turus ganin Maryam a ƙofar kitchen, ta haɗe rai ta shiga ɗaki, sai ga Gwaggo ta fito tana gyara ɗaurin zani, Maryam ta ɗauke kai kamar ba ta ganta ba, Gwaggo ta ce"Baiwar Allah za ki iya ba mu waje ko?"

Ta ce"Gwaggo ba zai yiwu a kunna gas yanzu ba, ya kamata ku fara sanin yadda abun yake kafin ku fara amfani da shi, wallahi yanzu idan aka kunna gas É—in nan gobara ce za ra tashi gagaruma ku mutu, don haka ko za a kunna shi a yau dole sai warin iskar nan da ya fita ya baje".

Ta ce"Ke Yasmin daga yau kar ki sake gwada kunna gas ko a wani wajen, ba haka ake yi ba".

Gwaggo ta tafi É—aki tana cewa"Oh! Ni kam Nazifi wa ya auro ne? Yau ni za a faÉ—awa zamani? An hana ni abinci kuma an hana ni dafawa? Ba laifinki ba ne".

Maryam ta ce"A'a Gwaggo ku zo ku kunna, sai dai na ce Allah Ya ji ƙanku, don ni yanzu zan bar muku gidanku ma".

Daga haka ta shige É—aki, ta É—auki akwatinta ta saka wayarta a jakar hannu ta fice, Gwaggo ta bi ta da kallon mamaki, sai kuma jikinta ya yi sanyi, ita dai ba ta ga abin da aka yi da zai saka ta yi yaji ba, "Daga kunna gas? Allah Ya kyauta" Ta faÉ—a tana shigewa É—akinta.

A ɓangaren Maryam ranta fess ta ƙarasa gida, duk da tana ɗan fargabar abin da Baba zai ce, faɗa ne ta saba da shi musamman ta wajen shi, kuma shi Baba yana da wani hali wanda yake burge ta, idan ya yi maka faɗa da nasiha a kan abu, ka ƙi yarda ko ka ƙi dainawa, shikenan sai ya ce ka fi ƙarfinsa ya zare hannu a tafiyarka, sam ba zai takura maka ka yi dole ba, shiyasa take ganin ba zai takura sai ta koma gidan Nazifi ba.

Ai kuwa da Baban ta fara cin karo, a ƙofar gida ta same shi, suna tattaunawa da wani maƙocinsu, dama gaida manyan unguwa ba ɗabi'arta ba ce, don haka kanta tsaye ta wuce su ta shiga gidan, Baba da ya gane ta sai da gabansa ya faɗi, ya bita da kallo.

Tana shiga da sallama Uwani ta tare ta ta rungume tana cewa"Sannu da zuwa, maza shige É—aki, ai ba neman kai muke yi da ke ba" Ta yi maganar tana jan akwatin zuwa É—aki.

Maryam ta shiga ta ajiye hijjabinta, ta kwanta a gado, Uwani ta shigo tana cewa"Kuma Nazifin yana kallo kika taho?"

Ta ce"A'a ba ya nan, sai dai ya dawo ya ga wayam".

Uwani za ta yi magana suka ji sallamar Baba, ya É—aga labulen É—akin yana cewa"Wace ta shigo yanzu kamar Maryam?"

Uwani ta ce"Ita ce, zama ya ƙi daɗi, tun a daren da aka kaita suke ƙunsa mata baƙinciki ba ta huta ba".

Baba ya ce"Ban gane zama ya ƙi daɗi ba, amma dai kin manta kwana biyu da kaita gidan miji ko? Da har za ta kwaso ƙafa ta dawo ta shimfiɗa miki ƙarairayi ki yarda. Ke ta shi ki fice ki koma gidanki".

Uwani ta rafka salati har da tafa hannu kafin ta ce"Wallahi Malam irinku ne masu siyar da ƴarsu a gidan auren, ta yi ta bauta da sunan zaman aure, ai aƙalla ka tsaya ka ji me ya dawo da ita tukunna kafin ka kore ta".

Ya ce"Wane irin rashin haƙuri ne zai sa ta dawo gida kwana biyu da aure?"

Ta shiga tsara masa ƙarya da kashi-kashi, har da cewa yau ɗin Gwaggon har marinta ta yi a gaban shi bai ce komai ba, ga shi kullum sai ta yi mata tuwo, ga jikarta tana zaginta. Baba ya yi shiru yana nazari kafin ya ce"Uwani duk da hakan wannan bai kai ta taho gida, ko waya ce sai ta yi wani ya je a sasanta yanzu idan aka fahimci har ta zo gida me duniya za ta ce?"

Uwani ta ce"Ita fa rayuwa indai za ka biyewa duniya za ka ƙare a wahala ne, ina ruwanka da duniya ko mutanen cikinta, yadda za su yi suka don ta dawo haka za su yi idan miji da uwarsa sun kassara ta".

Tsaki Baba kawai ya yi, don ba ya iya doguwar ja in ja, ya fice daga gidan.

Uwani ta ce"Maryam dole fa ki buɗe baki ki ƙwatarwa kanki ƴancinki, idan ba haka ba wallahi kwasarki zai yi ya maida ki, ƙarama da ke da ƙuruciya ki ƙare a wahala da uwar miji? Duk yadda za a yi ki ce ba za ki koma ba, kar ki sake ki sare, don auren kwana biyu mene ne marabarki da buduruwa? Yanzu wani saurayin zai aure ki wanda ya fi shi komai, Allah Ya sa dai bai ɗora miki idda ba".

Ta tsare ta da ido tana jiran amsarta, Maryam ta ce"Sai dai kar a kuma".

Uwani ta ce"Ya cuce ki! Allah Ya saka miki".

Nazifi yana komawa gida ya tarar an karo ƙofar ɗakin Maryam, ga shi dai ba lokacin sanyi ba ballantana ya ce shiyasa ta rufe, sai ya raya a ransa ko bacci ta yi da wuri, duk da sai yanzu ake kiraye-kirayen sallar isha'i, ya fara shiga ɗakin Gwaggo da sallama, ta amsa ya shiga ya zauna yana yi mata sannu, ta ce"Ni kam Nazifi matarka wace iri ce? Daga magana a kan kunna gas shikenan ta haɗa kaya ta bar gidan?"

Gabansa ya faÉ—i ya ce"Ta bar gidan kuma?"

Gwaggo ta ce"Ka ga Nazifi ni kam zan bar gidan nan, na tabbata Auduwa bai saka Æ´an haya a gidanmu ba, ka taimaka ka yi masa magana na koma, idan na mutu ni kaÉ—ai shikenan, ko na kumbura babu wanda ya sani duk tsiya dai kafin na fashe na ishi duniya da wari wani zai shigo ya gan ni".

Nazifi ya ce"Haba Gwaggo wannan wace irin magana ce kike yi?"

Ta ce"Ka ga ka je ka dawo da matarka, gobe zan bar gidan nan, yanzun ma don dare ya yi ne, ka faɗa mata ta yi haƙuri ni ba baƙuwar zafi ba ce".

Nazifi ya tashi ya fita jiki a mace, a ƙofar gida ya tsaya ya kira lambar Maryam, ta ɗaga ya ce"Maryam kina ina?"

Ta ce"Gidanmu".

Ya ce"Don Allah me yasa za ki yi mini haka? Me ya yi zafi?"

Tsaki kawai ta yi ta kashe wayar, ya bi wayar da kallon mamaki, bai taɓa zaton da gaske za ta iya yin yaji a kwana biyu da aurensu ba, ya mayar da wayar aljihu ya kama hanyar gidansu.

Yana ƙarasawa yayanta Sunusi ya zo shiga gidan, suka gaisa yana ce masa"Ya Maryam ɗin? Ko wani abun za ka karɓar mata?"

Nazifi ya yi yaƙe ya ce"Ai tana ciki ma, zuwa na yi mu tafi".

Sunusi ya zaro ido ya ce"Kamar ya tana ciki? Uban me ta zo yi?"

Nazifi ya fara kame-kame kafin ya ce"Ba wata matsala ba ce, za mu sasanta".

Sunusi ya shiga gidan ransa a ɓace, ya fara ƙwalawa Maryam kira, ta tashi zaune tana harare-harare, Uwani da ta fito daga banɗaki ta ajiye buta a fusace ta ce"To Allah Ya dawo da kai! Lafiya kake yi mata kiran mafarauta? Uwar me ta kashe maka?"

Ya ce"Yanzu na ga mijinta a ƙofar gida, wai babarmu uban me ya dawo da ita tun yau?"

Ta yi masa daƙuwa ta ce"Ubanka ne! Kuma wa ya sako ka a wannan rigimar?"

Da mamaki ya ce"Rigima fa kika ce? Lallai, kenan nufinki waje za ki ba ta ta zauna? Ke Maryam!"

Ya ƙarasa yana shiga ɗakin, kamar zai dake ta ya ce"Uban me ya haɗa ku da shi, da har kika kwaso jiki kika dawo?"

Ta yi banza da shi, tana turo baki, ya ce"Ai dama na san zai yi wuya ki zauna wallahi, idan na ce da motsi a kanki sai a ce ba haka ba, to ga shi dai an fara gani, sai ki wuce ga shi can yana jiranki a ƙofar gida".

Uwani ta ce"Kai Sunusi ka kiyaye ni fa! Ka fita daga idona na rufe, ina ruwanka da zancen nan wai?"

Ya ce"Allah Ya kyauta". Ya shiga É—akinsa.

Uwani ta saka hijjabi ta fita, ta samu Nazifi tsaye yana jira, ya tsuguna ya gaishe ta, sannan ta ce"Ka shigo daga ciki, magana ai ta wuce ƙofar gida".

Ya bi bayanta yana sunne kai ƙasa irin na surukai.

A tsakar gida ta shimfiɗa tabarma, ya zauna sannan ta shiga ɗaki ta ce da Maryam"Ki fito, kuma saura ya yi miki kallon soyayya ki haƙura, shi fa aure irin wannan da ya fara da matsala wallahi matsalar nan ba ta taɓa ƙarewa, sai dai ta yi ta girmama, ki tsufa a haka kina shaƙar baƙinciki, idan kuma kin ji kin gani to sai ki bi shi ki koma".

Maryam ta tashi ta fito, suka zauna aka ƙara gaisawa, Uwani ta fara magana"Nazifi ka ba ni mamaki, ka yi mana bazata! Ashe kai uwarka ka aurowa ƴata ba ka yi bayani ba? Ta ya za ku rufar mata da bauta ba ta da hutu ta ko'ina? Ka ga a gidan nan ma da na saka Maryam aiki gara na yi, saboda ba na so ta wahala, a gaskiya wannan zama naku ba mai yiwuwa ba ne, tun da abun har ya kai ta fara dukanta to kawai ka sake ta kowa ya huta tun ba ku fara tara zuri'a ba".

Gabansa ya faÉ—i ya ce"Duka kuma? Maryam Gwaggon ce ta dake ki?"

Ta ɓata rai ta kau da kai gefe.

Uwani ta ce"To ƙarya za ta yi mata kenan?"

Ya ce"A'a kawai dai na yi mamaki ne, saboda ita Gwaggon ba ta ce mini an yi haka ba".

Ta taɓe baki ta ce"Dama mutum zai yi ya ce ya yi ne? Nazifi don Allah salun-alun ka furta mata kalmar saki, ba sai ka wahalar da shari'a ba".

Ya ce"Haba Umma wannan ai ƙaramar matsala ce wacce za a magance ta, abun bai kai na rabuwa ba".
Chapter 6 · 0% Book details