← Book details Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 23

Sashe 20

Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji kuwa ya bi ta da kallon burgewa, wankan ya burge shi, don Sauda babu ruwanta da wani wankan dare ballantana kuma kayan bacci, dogayen riguna ne marasa nauyi kayan baccinta tun da ta fara haihuwa, ya haɗiyi wani yawu muƙut wanda har Sauda ta ji sautin, zuciyarta ta ƙara kumbura, ta kasa shigewa kawai tana tsaye tana ƙarewa Maryam kallo, sai Alhaji ne ya katse shirun nasu da cewar"Na barki ke kaɗai a gida".

Sauda ta yi masa mugun kallo ta ce"E tabbas ita kaÉ—ai, tun da a yanzu ita kaÉ—ai kake kallo a mutum, su Æ´aÆ´an naka ba mutane ba ne, komai ma ya same su ta matarka kake yi! Hmm!" Ta wuce fuuu ta yi cikin gidan.

Ya yi murmushin yaƙe ya ce wa Maryam"Kin ga Sauda ta dawo ko? Don Allah ku zauna lafiya, kin ga ma tun da ta dawo kan yaranta za ki fi kula da ni sosai ko?"

Ta yi farr da ido ta ce"Ƙwarai kuwa, zo ma mu je ka gani".

Ta yi ɗakinta, shi kuwa ya bi bayanta kamar raƙumi da akala, a gaban Sauda suka shige ɗakin nata, wacce ta fito daha ɗakin yaranta za ta shiga nata, ta manta rabon da ya shiga ɗakinta, sai dai ita ta bi shi nashi ɗakin idan ya kira ta, amma shi ne ya zo ya shige ɗakin amarya ko kunya ba ya ji, ta yi ƙwafa tana cewa"Lallai akwai aiki a gabana, tsohuwar kilaki ya kwaso".

Ta gagara zama a ɗaki, ko wanka ta kasa yi, sai leƙe take yi tana jiran fitowarsa amma shiru har ƙarfe sha ɗaya ta yi, ga shi ko sallar isha'i ba ta yi ba, kuma ta kasa yi, saboda tana son tabbatarwa da gaske a nan zai kwana? Shi kuwa Alhaji yana can Maryam ta saka shi a kwana ta kalallame shi, ta kanainaye shi har ya manta ma a ɗakinta yake.

Ƙashe dai sai sha biyu Sauda ta haƙura da leƙen ta yi sallah, ta kwanta, sai ta gagara yin bacci gabaɗaya ya ƙaurace mata, ta fara tunanin yanzu fa yana can tare da ita, lallai namiji ba shi da kunya, can dai ta fara tunanin ya za ta yi ta hana su sukuni, ta tashi ta fito a hankali ta shiga ɗakin yaranta, ta haska su, sai baccinsu suke yi hankali kwance, ta shiga tashinsu bisa shawarar zuciyarta, ta dinga jijjiga su duk suka tashi suna murza ido, ta sakawa fuskarta alamun firgici ta ce"Ku tashi don ubanku, aljanu ne suka shigo gidan! Suna ɗakin nan a ƙarƙashin katifarku!".

Ai kuwa a tare suka fara ihu, ta ce"Ku kwanta ba za su yi muku komai ba".

Suka fara kuka suna rirriƙe ta suna cewa a ɗakinta za su kwana.

Ta fizge tana cewa"Suna can a É—akina sun cika É—akin kowa ya yi ta kansa".

Ta fice a guje suka mara mata baya, amma kafin su shiga ta banke ƙofarta ta saka sakata, gabaɗaya suka ruɗe suka dinga ihu a mugun firgice kamar za su shiɗe.

A tare Maryam da Alhaji suka fito a ruɗe, suka tarar yaran suna ta buga ƙofar ɗakin babarsu, fitowarsu ya sa suka yi wajensu suna shigewa jikinsu cikin matsanancin kuka, Alhaji ya ruɗe ya fara tambayarsu me ya faru?

Suka ce"Aljanu, Abba aljanu a É—akinmu".

Gabansa ya faÉ—i ya ce"Aljanu kuma? Me kuka gani?"

Inaa sun ruÉ—e, sai a lokacin Sauda ta fito tana cewa"Mene ne?"

Suka yi kanta suna kuka.

Alhaji ya ce"Kin ji wai aljanu".

Ta ce"Aljanu kuma?"

Ya wuce É—akin a tsorace yana addu'a, ya haska bai ga komai ba, ya dawo a sanyaye ya ce"Abun ya bani mamaki wallahi".

Sauda ta ce"To kar dai fa ture aka fara yi musu".

Ya ce"Wane irin ture? Waye zai yiwa yaran nan ture?"

Ta ce"Wanda suka tsonewa ido mana, an ga yara sun cika gida tubarkalla ana son haukata su don kar Æ´aÆ´ana su moru".

Alhaji ya ce"Subhanallah! Kar na sake jin magana irin haka!".

Ya janyo yaran yana cewa"Tsorata kawai kuka yi babu komai a É—akinku kun ji? Ku je ku kwanta zan yi muku addu'a".

Sauda ta ce"Au da gaske sai ka kora su, saboda kar kwanan É—akin amarya ya wuce ka? Hmm dama uwa ce ba ta gudun Æ´aÆ´anta duk runtsi, ku shigo nan!".

Ya ce"Ba za su shiga ba! A É—akin nasu nake so su kwana ina son fahimtar wani abu ba ne kafin Allah Ya kaimu gobe na kira malamai a yi addu'a".

Maryam ta ce"Allah Ya rufa asiri". Ta koma É—akinta, ita ma duk sai tsoron gidan ya kama ta.

Ya saka su a gaba suna turjewa suka shiga, ya zauna ya kunna karatun qur'ani a wayarsa, yana addu'a yana tofa musu, amma da bacci ya fara ɗaukarsu sai su zabura su farka suna maƙale shi, a haka suka kwana, ita kuwa Sauda ta yi baccinta ranta fess, tun da dai ta haramta musu wannan daren to ita fa buri ya cika, kuma ta saka a ranta yanzu aka fara wasan, ta ɗau alƙawarin sai ta fitini gidan gabaɗaya, sai kwana a ɗakin shi ya gagari Maryam, kafin ta tankaɗa ƙeyarta waje.

LAST FREE PAGES! A NAN ZAN TSAYA DA FREE PAGE, DAGA WANNAN SHAFIN DUK WANDA KUKA GANI A PAID PAGE NE, ƳAN'UWA KU BIYA KU KARANTA CIKIN AMINCI, YANZU ZA A FARA WASAN NAN, TAFIYA TA KISHI MAI CIKE DA ƘULLA-ƘULLA TURA ƊARI BIYAR ƊINKI TA NAN KI SHA KARATU CIKIN AMINCI.

8028966015
Sadiya Abdulrazak opay

08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee

PAGE 13

Alhaji Haruna har zuciyarsa ya yi niyyar kamanta adalci, saboda haka duk da Sauda tana gidansu da ya tashi siyan kazar amarci haka ya siya da nata kashin, dama a baya kashi biyi yake siya da nata da na Innarsa, yau kuwa sai ya sayi kashi uku, ya tafi gidan don ya yiwa Inna sallama kamar yadda ya saba a kowane dare, lokacin tara saura kwata, ya same su a falo, ya ƙarasa a sanyaye ya zauna yana gaishe da Inna, ta amsa fuska babu walwala, ga yaran can rakuɓe a gefe, sun nuna kamar ba su san shi ba, saɓanin da, da idan ya shigo gida a guje suke rige-rigen zuwa gare shi, yaran su huɗu ne, Momy ita ce babba shekararta goma sha ɗaya, sai mai bi mata Kausar, shekararta takwas, sai Ummi shekararta shida, sannan Nana mai shekara huɗu, daga kan Nana ya ce mata ya kamata ta ɗan yi planing don mahaifarta ta huta, ta biye masa ta saka inplan na shekara uku da ya yi expire ta cire ta sake saka wani, don haka yanzu take ganin dama shi burinsa ta tsaya da haihuwar saboda amaryarsa ta zo ta zazzago masa ƴaƴa, kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kai gefe, saboda mugun haushin shi da take ji, ya ce da babbar ƴar"Momy ko gaisuwa babu?"

Sai ta waiwaya ta kalli mahaifiyarsu, saboda tun da suka yi yajin nan kullum sai ta zaunar da su ta faɗa musu babansu yanzu ya daina son su dukansu, shiyasa zai ƙara aure, kuma shi ya kore su dukansu, sannan amaryar da zai aura muguwa ce, kashe ta za ta yi ta zama ita ce uwarsu, kuma dukansu za ta dinga yi, tana hana su abinci, shi kuma baban nasu ba zai yi komai ba, saboda ya daina son su, haka dai ta tsara musu abubuwa kala-kala daidai da tunaninsu, su kuwa hakan ya sanya musu damuwa da jin tsoron baban nasu.

Sai da ya yi magana sannan suka fara gaishe shi É—aya bayan É—aya, ya amsa yana ce musu"Ya makaranta?"

Sauda ta yi wani huci kamar zakanya ta tashi buguzun-buguzun ta bar falon, kasancewarta mace mai ƙiba kuma doguwa, ya bi ta da kallo, sai ya ajiyewa Inna ledarta ya bi bayan Sauda ɗin, zaune ya tarar da ita ta naɗe hannu a ƙirji, ya yi sallama tana kallon shi yana kallonta ta ƙi amsawa, ya zo ya zauna a gefen katifar da take, sai ta miƙe za ta fita, ya ce"Kin ga Sauda zauna mu yi magana".

Ba ta zauna ba, amma ta fasa fitar,shi ma sai ya tashi tsayen ya ce"Ni fa ban ƙara aure saboda kin gaza mini ba, sai don ina da ra'ayin yin hakan, kuma dama can mata biyu ne a ƙaddarar aurena, idan mai afkuwa ta afkuwa ya kamata ki ajiye komai a gefe, ki koma ɗakinki, ni sai nake ganin ba girmanki ba ne a ce yarinyar nan ta zo ta tarar kin yi yaji, kamar hakan zai janyo miki raini".

Ta yi shiru dai ba ta ce komai ba.

Ya ci gaba da faɗin"Maryam ƙanwarki ce, kuma tana da sauƙin kai, za ku zauna lafiya in sha Allah, ni dai yanzu ki wuce mu tafi gida kawai, wannan abin da kika yi sai ki jawo mini zagi a gari, nan kuwa ba ni na kore ki ba".

Ta ce"Babu inda zan je, ka je ka zauna da wacce ka zaɓa, kuma sannan zan aiko maka da yaranka, tun da ita ka zaɓa kake ganin za ta iya sai ta riƙe maka!".

Ya ce"To shikenan, ni dai ba zan yi miki dole ba, musamman ma da Inna ta goya miki baya, saboda haka ki yi duk yadda kika tsara, amma ki sani ni dai ba zan sake ki ba".

Ta ja dogon tsaki.

Ya ce"Akwai abin da kuke buƙata?"

Sai a nan ta ce"Ba na buƙatar komai daga gareka, kai kanka bana buƙatarka ballantana abun hannunka, ita da kake baƙo a wajenta ka je can ka yi mata komai!".

Ya yi ɗan murmushi ya ce"Sauda kina da kishi, amma ban taɓa zaton za ki bar gidanki saboda kishiya ba, wai har kina barazanar za ki ba ni ƴaƴana, to ki ba ni, zan riƙe su".
Chapter 20 · 0% Book details