Sashe 2
Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hawayen da ba ta tsammata ba ne suka sakko mata, Uwani ta dafe ƙirji tana cewa"Yau ga muguwar shekara, inji kwaɗo da ya faɗa ruwan zafi, ke Maryam da gaske mutuwar aure kike yi wa kuka tun daga yanzu?"
Ta ƙarasa maganar tana zama a kusa da ita, ta kamo hannunta ta ce"Maryam, wai ina huɗubata a gare ki? Ko yanzu kin ajiye maganata ta miji goma ba uba goma ba ne? Uwar me Nasiru yake ba ki da har za ki yi kukan rashin shi a rayuwarki?"
Maryam tana danne zuciyarta don ta yi alƙawarin ba za ta bari babarsu ta san ta san manufarta a gare ta ba, ta ce"Babu komai babarmu, wallahi tausayin ɗan da zan haifa kawai nake yi, Al'amin yana can yana rayuwa ba tare da ni ba, wannan ma haka ce za ta faru, a ce na yi ta haɗawa ƴaƴana ƴan uba?"
Uwani ta ce"Au ke wannan ne kaɗai tunaninki? To mene ne da ƴan uba? Ke matsala kuke samu da naki ƴan uban? Ke uwa ce, addu'arki kaɗai ƴaƴanki suke buƙata, matuƙar dai su ma kin ɗora su a tarbiyyar da na ɗora ki ta jajircewa da ƙwatarwa kai ƴancin rayuwa, wallahi ba za su yi kukan rashin uwa ba kamar yadda ke ma ba na fatan ki yi shi ko bayan raina".
Maryam ta ce"Hakane babarmu na gode, bari na je na kwanta".
Ta tashi ta fita, Uwani ta bi ta da kallo tana mamaki da fargabar abin da ya sanyaya mata jiki.
Kwanciya ta je ta yi ta shiga tunanin baya, ta tuna ranar aurenta na farko da huÉ—ubar babarsu a gare ta.
Kowace amarya musamman wacce ta kasance buduruwa da aka yi mata auren fari, takan shiga damuwa da jin kewar rabuwa da gidansu da iyayenta a ranar da za a kai ta ɗakin mijinta, takan yi kuka ko da kuwa tana son wanda za ta aura ɗin, jikinta ya yi sanyi har ma wata takan ji dama ba ta yi auren ba, saɓanin Maryam da har yanzu da ta samu labarin motocin ɗaukarta ita da ƴan rakiyarta sun zo garau take jinta, babu wata fargabar shiga sabuwar rayuwa ko wani ƙalaubalen da za ta iya fuskanta a gidan aurenta, babu ruwanta da kewar iyayenta don ita ba mutum ba ce mai saka abu a rai, sabgar gabanta kawai take yi.
"Don Allah Maryam ki saka mayafinki, ki rufe fuskarki, ga shi nan za a kai ki wajen Baba ya yi miki nasiha" Cewar ƙawarta Aisha tana miƙo mata mayafinta.
Ta ce"Wai ni kam Aisha shi rufe fuskar nan dole ne? Baban zan ji kunya ko shi Nazifin da ya aure ni?"
Ta yafa mata mayafin tana dariya, daidai lokacin da ƴan'uwa suka zo suka ɗagata don kai ta gaban babanta, nasiha sosai Baba ya zage yana yi mata, kanta a sunkuye tana sauraron shi, kalamansa suna shiga ta nan suna fita ta can, domin duk wata nasiha da ta gamsu da ita a rayuwar aure masoyiyar babarsu ta gama yi mata ita, _"Maryam ki riƙe wannan kalmar da zan sanar da ke ruƙo ba na wasa ba, miji goma ba uba goma ba ne! Ita rayuwar aure ba a yi ta don ƙunci ko tauye hakki ba, ba a yi ta don haihuwa da rainon ƴaƴa kaɗai ba, sai don samun ƴancin kai da soyayya daga wajen miji, duk macen da mijinta ya yi wani abu dake nuna ba ta isa ba a wajen shi, ko kuma ya kalli wata macen bayan ita to tabbas sunanta bora! Da a kira ki da bora gara a kira ki da bazawara, saboda haka ina ba ki shawarar kar ki sake ki ɗauki raini daga wajen miji ko danginsa, ko da hakan zai yi silar mutuwar auren, ni fa da a ce kin yi wuni ɗaya a gidan aurenki cikin baƙinciki gara a ce kin yi auren wuni ɗaya mijin ya sake ki! Don haka ki ɗaura ɗamarar samarwa kanki aji da ƴanci daga wajen mijinki, zawarci ba komai ba ne"_.
"Maryam! Ba dai kuka kike yi ba?" Muryar yayana Sunusi ta ziyarci kunnenta, yana tambayar da mamaki da kuma izgili.
Ta ɗago ta buɗe fuska da soyayyun idanunta fess ta ce"Kukan me zan yi Sunusi? Kawai dai na rufe fuskar ne". Ta ƙarasa maganar da gadara tana juya masa kai gefe.
Ya ce"Ai na yi zaton kuka kike yi, in ce uban wa za ki yi wa? Hmm wannan aure Allah dai ya ba da zaman lafiya kawai, amma Nazifi ya É—akko Dala da gammo".
Baba ya ce"Sunusi ka faÉ—i alkhairi ko ka yi shiru, Maryam tashi ki je, Allah Ya kai ki a sa'a".
Suka tashi aka yi ɗakin babarsu da ita, tana zaune cikin ƙawayenta, ta zauna kusa da ita, ta kama hannunta ta ce"Babarmu zan tafi".
Ta yi murmushi ta ce"Maryam duk wata nasiha da zan yi miki ai na gama ta, kar dai ki zubar da karatuna kawai shi ne fatana". Ta kawo bakinta saitin kunnenta ta ce"Miji goma ba uba goma ba ne!".
Ta gyaɗa mata kai cike da gamsuwa tana murmushi, yayin da matan ɗakin suke binsu da kallon burgewa, na ƙaunar dake tsakaninsu da babarsu wacce ba ta ɓoyewa har kullum ƴaƴanta ƙawayenta ne, ita ta ja mayafinta ta rufe mata fuska aka fitar da ita waje.
Aka saka ta a mota lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar magriba aka tafi da ita gidan mijinta wanda ya kasance zaɓinta, domin duk cikin samarin da suka nuna mata so Nazifi ne yake daidai da ra'ayinta, ba don komai ba sai don shi ne mai sauka a kan ra'ayinsa ya bin ra'ayinta ko da ba ya so, shi ne mai yi mata biyayya da kwantar da kai tamkar uwarsa, sakamakon sonta da ya zame masa tamkar wata jarabawar rayuwarsa.
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
PAGE 2
Ƴan kai amarya da rakiyar ƴan ango kowa ya watse, wannan washe bakin da wasu kalaman soyayya bai damu Maryam ba, burinta kawai ta ji dalilin da ya sa ya rufe wani ɗaki guda ɗaya a cikin gidan, wanda tun da aka je jeri ya ce musu ban da ɗakin nan, ta sakko daga gadon da take a zaune, ta fice, ya bi bayanta yana cewa"Alwala za ki yi?"
Tana ƙarewa gidan kallo ta ce"A'a ina ganin yanayin gidan ne".
Ɗakuna uku ne sai kitchen da banɗaki a tsakar gida, ɗaya aka saka mata gado, ɗaya kujerunta, ta ce"Ni kam Nazifi wannan ɗakin da ka cewa ma su jeri ban da shi mene ne a cikinsa? Ko aure za ka ƙara?"
Ya yi ƴar dariya ya ce"A haba dai aure! Ko auren zan ƙara ai dai kin san ba yanzu ba, kuma idan hakane me zai hana ki saka kayanki sai auren ya kusa sannan ki kwashe?"
Ya yi wata dariya ya ce"To ballantana ma ban da ra'ayin ƙara aure, ai ba irinki ake yi wa kishiya ba my Love".
Maryam ta taɓe baki ta ce"Ni dai ba ka ba ni amsar tambayata ba, me yasa ka kulle? Ko turakarka ce ai dai ka buɗe ko labule na saka maka".
Ya ce"'A'a ma wallahi ba turaka ba ce, ki yi haƙuri ban faɗa miki ba, dama Gwaggo ce za ta dawo nan da zama, don ma ba a gama ginin da wuri ba, da sai ta riga mu tarewa, yanzu kuma da ta ga abun ya zo dab sai ta ce idan an gama bikin kin tare sai ta dawo".
Wani abu ya daki zuciyar Maryam, wai ita yake nufi ta zauna gida É—aya da uwar miji, tun tana amarya? Ta ce"Wai kana nufin da Gwaggo za mu zauna? To inda take a da me ya same shi?"
Ya ce"Ai kin san dama gidan haya ne, ina da burin gina mata gida, to da na ci rabin ginin nan na ce mata nata ne, sai ta ce sam ita dai na yi aurena na tare idan ya so sai na ba ta É—aki É—aya ta zauna, gobe za ta dawo in sha Allah".
Kamar wacce aka fizgi zancen daga bakinta ta ce"Kuma tun gobe?"
Ya ji tambayar ba ta yi masa daɗi ba, da alama dai Maryam ba ta maraba da mahaifiyarsa, ya ce"To ai dayake ita kaɗai ce dama a gidan, sai wata jikarta ƴar yayana ita kuma yarinya ce, kin ga tare muke kwana a gidan, yanzu kuma ba na nan, akwai dai ƙanwata wacce take makarantar kwana, kin ga yanzu sai ita kaɗai, ba na son barinta ita kaɗai a gidan, shiyasa na ce gobe sai ta taho".
Maryam ta jinjina kai ta ce"To Allah Ya kaimu".
Ya amsa da"Amin my Love, ki yi alwala, ni ma bari na yi".
Ta ce"A'a ni na yi sallar isha'i yanzun nan".
Ya ce"To ai ta godiya ga Allah za mu yi".
Ta ce"Ka bari dai gobe ma yi".
Ya ce"Da dai kin daure mun yi yau É—in, don ina cike da É—okin kasancewa da amaryata, kin ga ya kamata mu fara gabatar da sallar tun da sunna ce".
Maryam ta kyaɓe fuska kamar mai ƙyamar wani abu ta ce"Wallahi kar ma ka saka rai, don yau a gajiye nake, sai dai mu bar wa gobe".
Ransa bai so ba, amma ba ya son takura mata, don haka ya ce"Yau da gobe ai duk É—aya, ni bari na yi nafila".
Ya É—auki buta ya shiga banÉ—aki, ita kuma ta koma É—aki da sauri, ta É—auki wayarta ta kira babarsu, ta É—aga tana cewa"Maryam lafiya kuwa da daren nan?"
Maryam ta ce"Babarmu kin ji wata sabuwa? Wai ashe wannan É—aki da ya kulle na babar shi ne a nan gidan za ta dawo ta zauna".
Uwani ta dafe ƙirji ta ce"Na shiga uku! Me kika ce Maryam? Hauka ake yi? To wallahi ba ki samu gidan zama ba, kada ma ki miƙe ƙafa!".