Sashe 4
Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuwa Maryam da asuba ta yi nata wankan, lokacin ya tafi masallaci, Gwaggo da ta makara yau ta fito don shiga banɗaki ta ji ƙarar ruwa ana yin wanka, ta ce"Waye a ciki? Waye yake wanka da asubar fari?"
Wani ƙululun baƙinciki ya tsayawa Maryam a wuya, sai da ma ta ɓata lokaci sosai sannan ta fito tana haɗe rai. Gwaggo ta ce"Ashe ke ce".
Ba ta kula ta ba, ta shige É—aki.
Da sassafe ta ji motsin an buɗe kitchen, don tun asubar ba ta koma bacci ba, tana dai kwance tana jira gari ya waye ta fita, ta fara tunanin me tsohuwar nan za ta yi a kitchen? Jin shiru ba a rufe ƙofar ba ya tabbatar mata har yanzu ana cikin kitchen ɗin, ta tashi ta fito ranta yana ɓaci, daidai sanda Gwaggo ma ta fito daga ɗakinta, tana cewa"Haka kawai kun ƙule a ɗaki kun bar mutane da yunwa? Yasmin!" Ta doshi kitchen ɗin tana ƙwalawa jikarta kira.
Ko kallon arziƙi ba ta yi wa Maryam ɗin ba, ita ma kuwa ta bi su kitchen ɗin, zaune ta samu Yasmin ɗin a kan turmi ta saka kwanon naman da Maryam ta soya jiya da rana a gaba tana ta ci har ta kusa cinyewa, ranta ya ɓaci don dama ita ba ta cikin jerin mutane masu haƙuri, ta ce"Kutt! Ke uban wane ya ce ki shigo mini kitchen har ma ki ɗauki abu ki ci?"
Gwaggo ta ce"Ke dakata! Kar ki zagar mini ita, don ta ci naman da ba da kuÉ—inki aka siya ba?"
Nazifi da y ƙaraso kitchen ɗin yanzu ya ce"Me yake faruwa ne?"
Takaici ya hana Maryam cewa komai, saboda ba ta son nunawa babar shi halinta tun yanzu, sai kawai ta jinjina kai ta fice daga kitchen É—in.
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
PAGE 3
Ɗakinta ta shiga ta riƙe ƙugu tana huci kamar mai jiran dambe. Nazifi jiki a mace ya ce"Gwaggo ya kamata ki nunawa Yasmin kuskurenta fa, wannan ai ba ɗabi'a ba ce mai kyau ta dinga ɗaukar abin da ba a bata ba".
Gwaggo ta ce"Au! Nazifi kenan dai ka goyi bayan matarka ko? Yanzu ƙarfe nawa? Ƙarfe bakwai da rabi kun ƙule a ɗaki kuna ta bacci ba ta fito ta sallame mu ba? Saboda na dawo gidanka da zama sai karatun yarinya ya ɓalɓalce? Ai shikenan". Ta faɗa tana rausayar da kai kamar abar tausayi.
Sannan ta ja hannun Yasmin tana cewa"Mu je ki shirya sai na ba ki kuÉ—i ki sayi koko a hanya".
Nazifi ya shiga É—aki ya samu Maryam kamar za ta fashe, ya ce"Maryam yarinyar nan ba ta yi daidai ba, amma ke ma bai kamata ki yi magana ba, da sai ki faÉ—a min na tsawatar mata, kin san tana zuwa makaranta to don kar ta yi latti ne ya sa ta nemi abin da za ta ci".
Ta ce"Ka ga dakata Nazifi! Ta ya zan san tana zuwa makaranta alhalin a sharuÉ—an auren ba ka sanar da ni har da kula da wasu ba?"
Ya ce"Gwaggon ce wasu?"
Ta ce"Duk yadda ka É—auka!".
Ya jinjina kai ya ce"To ki yi haƙuri ki je ko shayi ne ki dafa musu tun da akwai biredi, amma daga yau sai ki dinga tashi da wuri, tun da ita Gwaggo ta fi son karyawa da abinci ko kunu da ƙosai, shi ma sai idan babu ɗumamen tuwo, na manta na faɗa miki anjima zan auno gari, ita ta fi son tuwo".
Maryam ta ƙanƙance ido ta ce"Ni Nazifi na tambaye ka mana".
Ya ce"Ina ji".
Ta ce"Ku nawa aka aurawa ni? Kuma sannan zaman wa nake yi?"
Ya ce"Maryam! Kina nufin mahaifiyata ba ta da matsayin da za ki yi mata hidima?"
Ta ce"Ba zancen matsayi ake yi ba, ka ga ba na son abin da za a zo ana jin kanmu, tun wuri gara mu baje ta a faifai kowa ya É—auki rabonsa, kai ka auro ni, zamanka nake yi, wallahi babu wacce za ta mayar da ni baiwa, to tsaya na tambayeka ma, da Gwaggo take gidanta kafin ta dawo nan wace take yi mata girki?"
Nazifi ransa ya ɓaci sosai, amma ya san halin matarsa ba a yi mata hayaniya, kuma ba zai so su fara samun matsala tun yanzu ba, ya ce"Kin ga zauna mu yi magana ta fahimta".
Ta zauna tana É—auke kai.
Ya ce"Gwaggo fa uwata ce, idan kika kyautata mata ni kika yiwa, kuma ladanki yana wajen Allah, sannan ke ma za ki so idan zama ya haÉ—a babarki da surukarta ta kyautata mata..."
Ta katse shi da faÉ—in"To yaushe aka fara rayuwar aure a barzahu? Ni uwata ta gama tata rayuwar kuma babu surukar da ta takurawa".
Ya ce"Kenan uwata takura miki ta yi?"
Ta ce"Za dai ta fara".
Nazifi ya ce"Maryam ina sonki, amma gaskiya son bai kai yadda zan bari wani raini ya shiga tsakaninki da mahaifiyata ba".
Maryam ta ce"Sanin kana sona ne yasa na amince na aureka, amma ai kai ma ka san ka so kanka da yawa, a ce daga zuwana gidan na hau hidima da jama'a? Wai har wani tuwo zan dinga yi ina É—umame?"
Ya ce"To ai ban ce ke za ki ci ba, ita za ki yiwa".
Ta ce"Nazifi idan kana so mu sasanta aurenmu ya yi ƙarko to ka yiwa sharaɗin da zan kafa assam'u wa ɗa'a".
Kallonta kawai yake yi, ta gyara zama ta ce"Ka ga dai a wajen ɗaurin aure ba a ce zan dinga kula da Gwaggo da jikarta ba, cewa ma aka yi za ka kula da ni, ni ban ce ba zan zauna da mahaifiyarka ba, amma sai dai mu rayu kamar ƴan zaman haya, idan gari ya waye ta fito na fito za mu gaisa, ta yi girkinta na yi nawa, zan iya zubawa a roba na bata don zaman tare da fita haƙƙin maƙobtaka, sannan zancen haɗa kitchen ba zai yiwu ba, tun da ga abin da hakan ya fara haifarwa, gaskiya ta haƙura ta mayar da kayanta ɗaki, ko ka ɗan buga mata rumfa a tsakar gidan, sannan wannan yarinyar kar ta ce za ta dinga shigo mini ɗaki, don na lura ba ta da kunya, kowa ya yi harkarsa, ka yiwa Gwaggo cefanenta da ban nawa da ban, ta yi girkinta na yi nawa, idan ka yi haka za mu zauna lafiya".
Nazifi ya ce"A gaskiya Maryam wannan ba tsari ba ne, kuma ni zan ji nauyin faÉ—awa nahaifiyata haka".
Ta ce"To salun-alun ka sallame ni tun tafiya ba ta fara miƙawa ba, sai na tafi gidanmu, don mutuwar aure ba komai ba ce".
Ya ce"Ni ba haka nake nufi ba, zan ji ta bakinta dai, yanzu ki dafa shayin".
Ta tashi tana taɓe baki ta shiga kitchen ta ɗora shayin, a nan ta zauna ta kira lambar babarta, tana ɗagawa ta ce"Babarmu ni fa zan taho gida".
Uwani da take zaune tana shan kunu ta ce"To abun ya ƙi ko?"
Maryam ta kwashe komai ta faɗa mata, Uwani ta ce"Tabɗijan! To shikuwa Nazifi kwana-kwanar me yake yi? Ai gara ma ya fito fili ya sanar da duniya ƴar aiki ya ɗakkowa uwarsa! Maryam da ƙuruciyarki da kyaunki za ki ƙare a gidan da za ki dinga yin bauta? Ga ɗakinki ga na suruka, to wannan uban gwanjon da kike ta siya na ƙananun kaya duk ita za ki yi wa kwalliya ashe? Yanzu ya amince da sharaɗinki ko kuwa?"
Ta ce"Ya dai ce za su tattauna".
Uwani ta ce"To su tauna sa kyau ta yadda za su ji daÉ—in haÉ—iyewa, Maryam idan fa kin ga da takura ki kamo hanya ki taho gida, don ba gajiya muka yi da ke ba, muka ba shi".
Ta ce"Bari dai na ga yadda za su tsara, wallahi ba sai kin ce na taho ba, don indai haka zaman aure yake to gara ma na dawwama a gabanki".
Suka yi sallama, ta juye shayin a flas, ta zuba na Gwaggo a ƙaramin flas ta a ajiye, ta ɗauki nasu ta tafi da shi ɗaki, ba ta same shi a ɗakin ba, sai ta fito ta ga takalmansa a ƙofar ɗakin Gwaggon, hakan ya tabbatar mata yana ciki, ta yi saɗaf-saɗaf ta je ta laɓe a jikin labulen ta kasa kunne, daidai sanda Gwaggo take cewa"Yanzu dai Nazifi kenan ka zo ka faɗa mini na takura muku kai da matarka na bar maka gidanka ne ko?"
Muryarsa cike da damuwa ya ce"Subhanallah! Kar Allah Ya kawo ranar da zan yi wannan tunanin, kin san Maryam yarinya ce..."
Ta ce"Kai dakata, Allah Ya sa a nonon uwarta ka tsigota ka kawi gidan nan, mu sanda muka zauna da surukanmu wace bauta ce ba mu yi ba? Tuwon dawa kwano biyar nake tuƙawa, bayan na yi daka na yi surfe na niƙa, idan ban da lalacewar zamani har yarinyar da aka auro shekaran jiya ce za ta kafawa miji wani sharaɗi kuma akan mahaifiyarsa? Nazifi ka fice min daga nan zan haɗa kayana na tafi kawai".
Maryam ta ja wata ajiyar zuciya a hankali jin Gwaggo za ta tafi, Nazifi ya ce"A'a babu inda za ki je, ni fa ba haka nake nufi ba, shikenan zan fahimtar da ita za ta dinga yi miki komai, ki yi haƙuri, bari na karɓo miki shayin".
Maryam ta yi wuff ta shige É—aki, zuciyarta tana zafi, a ranta tana ayyana ta ga wanda zai sauka a kan bakansa tsakaninsu, ya shigo yana cewa"Ina shayin nata?"
Ba tare da ta kalle shi ba ta ce"Yana kitchen".
Ya ce"Ai da sai ki kai mata, don Allah Maryam ki zauna lafiya da babata, wallahi ba ta da wata matsala".