Sashe 14
Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta tashi a fusace ta ce"Hamza idan ka yi haƙuri zan bar maka gidanka har abada, amma sai na haihu, kuma dalilin ƙin tafiyata ai na faɗa maka sai ka yi mini siyayya, sannan ka sayi kayan jarirai".
Ya ce"Amma ai ce miki na yi zan aiko ko?"
Ta ce"Don ka yi magana dole ne na amince? Idan ji ya zama dole ai babu inda yarda take zama dole".
Ta juya ta kwanata.
Ya fice daga É—akin yana tsaki.
Da ya ga dai har ta ƙara kwana uku ba ta da niyyar tafiyar, sai ya same ta suka zauna ya ce"Wai me da me kike buƙata?"
Ta ce"Za ka siyo kayan shayi na gwangwani fa ba irin wanda kake kawo mini ba, sannanza ka siyo kwalin indomi, da golden morn, sannan kayan jariran wanda mace da namiji za su iya sakawa kala uku, ka ga kenan shida za ka siya tun da su biyu ne".
Kalmar biyun nan ta saka gabansa faÉ—uwa, saboda har yanzu kuÉ—in abun yanka ma É—aya ya tanada, shi ma lissafinsa tunkiya zai siya haka Æ´ar madaidaiciya.
Ta ci gaba"Ka ga za ka siyo tawul masu kyau kowa biyu, sai saitin kayan sanyi da saitin man shafawarsu, wannan su za ka siya kafin na haihu, idan na haihu aka ga me aka samu sai a san yadda za a haÉ—a kayan barka".
Ya ce"Wannan lissafin nawa ya kama?"
Ta ce"Oho! Ka ba da dubu É—ari sai a je a ji".
Ya yi mata wani mugun kallo mai É—auke da manufar ba ki da hankali, ya ce"Dubu É—ari?"
Ta ce"To ka je ka siyo mana".
Ya tashi ya fice, a ranar ya siyo komai da ta lissafa, amma duk masu sauƙin kuɗi ya zaɓo, ya kawo mata ya lallaɓata ta tafi.
Uwani da ta ga kayan ta rafka tagumi har sai da Maryam ta tsargu, kafin ta ce"Maryam wane irin miji ne wannan da kike son rayuwa da shi? Wannan kayan tsohon ya yi masu mugun arha ya siyowa Æ´aÆ´ansa na fari? To sai dai mu ce Allah Ya kyauta".
Maryam dai ba ta ce komai ba.
Daga nan kuma sai Uwani ta tsiri saka ta ta cewa Hamza ya siyo mata nama, ko kayan marmari haka, idan ta kira shi ta faɗa masa sai ya fara masifa yana cewa shi fa ba shi da kuɗi, wataran zai kawo, wataran kuma ya ƙi kawowa, Uwani kuwa ta samu abun mita, ta yi ta masifa tana tsinewa auren, a haka dai har aka cika sati biyu, ranar tsakar dare Maryam ta fara naƙuda, Baba ya ce ga maƙotansu wani matashi yana da adaidaita sahu a kira shi su tafi asibitin, amma fir ta ƙi ta dinga kiran Hamza a waya, shi kuwa yana ganin kiran jikinsa ya ba shi ba lafiya ba, ya san dai ƙarshen zance cewa za a yi Maryam za ta haihu ko kuma ta haihu, don haka ya ƙi ɗagawa, sai ma ya saka wayar a silent ya ci gaba da baccinsa, dole dai aka bi maganar Baba, suka tafi asibitin a hanya tana ta zagin Hamza Baba yana kwaɓarta.
Sai da asuba Maryam ta haihu, Æ´aÆ´anta mace da namiji, sai dai macen ta zo babu rai, sai namijin ga shi nan ma sha Allah, sai da gari ya waye ta kira lambar babar Hamza ta bawa Uwani, ta faÉ—a mata an sauka lafiya, ta ce"Ki sake kiran shi shi ma".
Uwani ta ce"Kin san kira nawa na yi masa jiya? Yanzu da ya tashi sallah ai zai ga miss call idan shi mutumin kirki ne ai sai ya kira!".
Bakwai da rabi Hamza ya zo asibitin tare da babar shi, suka kawo musu abun karyawa, a gaban babar shi Uwani ta caccake masa tass na rashin ɗaga wayar, ita kuma tana ta ba ta haƙuri, aka tafi da gawar yarinyar aka binne, sai da yamma aka sallami Maryam ta koma gida.
Sun ga tijara kafin ranar suna ta zo, don yanzu Uwani karɓar lambar shi ta yi, abu kaɗan ta kira shi ta ce ana buƙatar abu kaza, ranar da bai kawo ba ta yi ta tsine masa ƴaƴanta suna yi mata nasiha, amma kamar suna zugata.
Ranar sunan ma sai da ta raina abun yankan, kayan fitar suna ma kala ɗaya ya yi mata, wata atamfa ce aka sako ta a cikin kayan barka, don haka ita Maryam a ranta ta ƙudure wannan zuwa gidan da ta yi, ta zo kenan babu zancen komawa, don wannan idan ta ci gaba da zama da shi gorin Uwani ma kawai ya ishe ta.
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
PAGE 10
https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee
Hamza sai ya bushi iskarsa yake leƙowa gidan har aka yi arba'in ɗin Al'ameen, ga wani raini da ya yiwa Uwani, saboda yawan roƙon shi da take yi, da yadda take raina ƙoƙarin shi, har wani kallon gani-gani yake yi mata idan ya je gidan. Uwani tana sane ta ce Maryam arba'in biyu za ta yi, saboda ta dinga ja masa rai har ya gaji auren ya sire masa, ba ta san kamar an zuga zugagge ba ne, don shi ma ba son ci gaba da zaman yake yi ba, Baba da ya yunƙuro a kan sai ta koma ɗakinta Uwani ta sanar masa ba ta da lafiya fa, ɗinkin da aka yi mata sanadin haihuwar nan bai warke ba, kuma likitocin sun yi gargaɗi da kakkaurar murya a kan kar ta koma sai bayan wata uku, su kuwa yaran zamani masu do a tsakar ka idan ta koma sai dai komai ya faru, don haka Baban ya ƙyale su ya zuba ido.
Watanta biyu a gida Hamza ya zo da daddare, sun gaisa yake cewa"Maryam yaushe za ki koma ne? Sannan ina ga fa sai dai ki koma gidanmu da zama..."
Ta katse shi da faÉ—in"Ban gane ba!".
Ya ce"Ai ganar da ke nake yi".
Ya ce"Kin ga dama kuɗin hayar ya ƙare, kuma ni ba ni da kuɗin da zan sake biya, sannan ma ina son tafiya wata ƙasar neman kuɗi, ana kan yi mini hanya, kuma ko ba wannan ba ni dama fa a zamanmu haƙuri kawai nake yi da ke, saboda tsakani da Allah ba ki da kunya, ba ki da tarbiyya ba ki san girmana ba a matsayina na mijinki".
Maryam ta yi mamaki sosai, don ko da wasa ba ta taɓa tunanin gidan nan ba na shi ba ne, sanda yana neman aurenta ya ce mata na shi ne ya gina tun da jimawa sai ya saka ƴan haya a ciki, yanzu ya tashe su tun da ya yi aure, ta ce"Hamza idan za ka kore ni ba sai ka yi mini ƙarya da gida ba naka ba ne, idan ka yi haƙuri dama ni ma wannan zaman da nake yi ba ni da niyyar komawa, saboda haka ka sallame ni kafin ka tafi inda za ka je".
Ya ce"Wallahi ba gidana ba ne, ki tambaya ki ji, kuma sannan ni fa ba ni da manufar rabuwa da ke, sai dai idan ke ce kika zaɓi hakan".
Ta ce"E ni ce na zaɓa ɗin, ka sake ni".
Ya ce"To gobe zan aiko miki saƙo".
Ya tashi ya fice, a tsakar gida ya samu Uwani zaune, ta ce"Ka fito?"
Ko kallonta bai yi ba ya yi dogon tsaki ya fice.
Ta shiga ɗakin dafe da ƙirji tana cewa"Na shiga uku ni Uwani, Maryam me zan gani? Mijinki ne yau ya yi mini tsaki, a gobe kuma sai duka, wallahi saura zagi da duka, Maryam wa kika kwaso mana ne haka?"
Jin shigowar saƙo wayarta ya sa ba ta kula Uwani ba, tana dubawa ta ga daga shi ne, ya rubuto mata ya sake ta saki ɗaya, ta nunawa Uwani wayar ba ta ce komai ba, ta ce"To rubutu nake gani, kuma kin san ni ba iya karatu na yi ba, na mene ne?"
Ta ce"Shi ne ya turo mini saƙo wai ya sake ni saki ɗaya".
Uwani ta sauke ajiyar zuciya ta ce"To Alhamdulillah! Tsaki da ya yi mini kuma ya je don kansa, tun da dai ya sallame ki ni ya biya ni!"
Ta zauna tana cewa"Maryam ki kwantar da hankalinki, wannan ba komai ba ne, in sha Allah nan gaba za ki samu miji na kere sa'a, wanda za mu yi alfahari da aurenki".
Maryam ta ce"Allah Ya sa".
Bayan kwana uku da sakin sai ga babar shi ta zo gidan, Uwani ta yi kicin-kicin ta tarbe ta a tsiyace, saboda kar ma ta yi zancen kome, irin yadda take amsa mata gaisuwa a daƙile kamar mai gyambo a maƙoshi har Maryam ɗin sai da ta ji babu daɗi, saboda ta zauna da matar lafiya ba ta da wata matsala, babar Hamza ta ce"Ashe haka abu ya faru, ɗan yau dai ka haife shi ba ka haifi halinsa ba, wallahi Hamza bai yi shawara da ni ba ya yanke hukunci, don Allah ku yi haƙuri".
Uwani ta ce"Ai ba komai ba ne a wajenmu, duk wanda ya rasa Maryam shi ke da asara, don haka shi za ki bawa haƙuri".
Ta ce"Ai kuwa ba a ce ba komai ba ne, aure irin wannan da albarkarsa har an fara samun rabo..."
Uwani ta katse ta da faɗin"Cewa za ki yi har an samu rabo, idan kika ce an fara da saura kenan za a ci gaba, kin ga mun gode amma don girman Allah ki ƙyale yaron nan sa hukunci shi, don ba a yi wa yaran zamani dole".
Ta ce"Haka ne, to Allah Ya rufa asiri".
Uwani ta gyara zama ta ce"Dama ai jira nake a cika sati na ga ƙarshen abun, da ba ki zo ba dama zan zo".
Babar Hamza ta ce"To lafiya dai ko?"