← Book details Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 23

Sashe 19

Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tashi ta je ta ɗakko shi a yadda suka bar shi, ta ajiye, ya saka su a gaba sai ga shi sun cinye tass, har da ƙari, ya yi mamakin dalilin da ya sa suka yi mata haka, ya zaunar da su ya yi musu nasiha sosai, ya nuna musu ita ma Maryam babarsu ce, duk abin da suka san ba za su yiwa babarsu ba to kar su yi mata, suka ce to, sannan ya saki jiki da su suka yi fira, Maryam ta ce su je ta yi musu wanka, ba su yi musu ba suka wuce, sai a lokacin ma ta sa suka yi home work, ƙarfe takwas Abba ya ce su je su kwanta, ita kuma Maryam ta kwashi unifom ɗinsu ta tafi wankewa, sai ga shi sun yi wankin a tare da Alhaji suna yi suna fira.

Ita kuwa Momy suna shiga ɗaki ta ɗauki wayar ta sanarwa Sauda duk yadda aka yi, Sauda ranta ya ɓaci matuƙa ta ji kamar ta taso ta taho gidan yanzu, ta fara tunanin wato daga zuwanta za ta sa ya tsani ƴaƴansa har yana yi musu faɗa? Nan gaba ai sai duka, kenan ya goyi bayanta nan gaba ko ita ce da laifi tana kallo za a tauyewa ƴaƴanta haƙƙi, ai kuwa ba zai yiwu ba, ta fara tunanin hanyar da za ta bi don ta hana su cin amarci, sai dai yaran sun yi ƙanƙantar da za ta saka su yi wata kissar, don haka kawai ta yanke gara ta dawo su fara gabza yaƙin, ta ce wa yarinyar ta yi haƙuri su kwanta, amma kar su sake bari ta yi musu wanka, ita ta yi da kanta sannan ta yiwa ƙannenta.

Washegari haka Maryam ta yi sammakon tashi saboda yaran, don tun a daren ya faɗa mata girki biyu ake yi da wanda za su ci, da wanda za su tafi da shi, ta dafa shayi ta soya doya da ƙwai ta saka musu a lunch box ɗin, sannan ta tafi ɗakinsu, ta tarar Momy ta yi wanka za ta fara yiwa sauran, Kausar tana cewa ita ba za ta yi mata, ta ce"Ya za a yi ki yi musu? Ke ma ai ba wuce wankan kika yi ba, ku wuce na yi muku".

Momy ta ce"Mu fa Ummanmu ce kawai take yi mana wanka".

Maryam ta ce"Tun da yanzu ba ta nan ai dole ku bari na yi muku".

Ta ce"Mu dai a'a".

Maryam ta juya ta fita, ta sanarwa da mahaifinsu, da mamaki ya ce"Ha'a, wai me yasa yaran nan suke haka ne?"

Ya fito ya zo É—akin, ya ce"Ke Momy! A kan me ba za ta yi muku wanka ba?"

Ta ce"Ummanmu ta ce kar mu yarda da ita".

Maryam ranta ya ɓaci ta ce"Ai shikenan". Ta juya ta bar ɗakin.

Ya ce"Ummanku? Au haka ta tsara muku? Abin da ta turo ku ku yi kenan? To zan haÉ—u da ita! Ku saka kayan naku a haka ku tafi, idan ta damu sai ta dawo ta dinga yi muku wankan".

"Maza ku saka ku fito, mintu uku na baku". Ya ƙarasa a tsawace yana jin dole ya takawa Sauda burki don ba za ta lalata masa tarbiyyar yaransa ba.

Yana fita Momy ta shiga banÉ—aki ta kira Sauda ta sake faÉ—a mata, ai kuwa ta hasala tana ta zage-zage.

Suka fito kowaccensu babu sakewa, sai a lokacin suka gaishe shi, ya amsa kafin ya ce"Kun gaishe da Antinku?"

Duk suka yi shiru, sannan suka gaishe ta É—aya bayan É—aya, suka karya mai adaidaitansu ya zo suka tafi makaranta.

Sun gama karyawa ya ce da Maryam"Don Allah ki yi haƙuri, yara ne kin san duk yadda aka tsara musu ba za su yi nazari ba, amma zan same ta na yi mata magana, idan ba za ta barki ki yi yadda ya dace da su ba, to ta zo ta zauna da su".

Maryam ta ce"Allah Ya kyauta".

Kafin ya tafi kasuwa ya tsaya a gidan nasu, ya gaida Inna, ya samu Sauda tana karyawa, ko kallon shi ba ta yi ba, ya ce"Yawwa Sauda na ga kin aiko mini yarana, ina son ki sani Maryam za ta iya riƙe su fiye da yadda kike kula da su, sai dai ki sani indai kin bar mata su to fa sai dai ki koma gefe ki yi kallo, ba zai yiwu tana tufka kina warwarewa ba, saboda shirme kin zauna kina tsarawa yara shirmen banza, to matata uwa ce a gare su, ya zama dole su yi mata biyayya tun da ni na haife su!".

A hasale Sauda ta ce"Ita ta haifar mini su? Wallahi babu shegiyar da ta isa ta tsarawa Æ´aÆ´ana yadda za su yi, yarinyar da ba ta samu tarbiyya ba tun daga tushe, har kana kallona kana faÉ—a mini kalmar matarka?"

Sai kuma ta saki wata dariya mai kama da ta tsantsar baƙinciki ta ce"Heee masu mata manya! To a yi mu gani idan tusa za ta hura wuta, yarinyar da ba ta zaman aure har wata abar alfahari ce? To sai ka jira ka ga zaman ya yiwu kafin ka fara wulaƙanta ni ka watsar da ƴaƴanka!".

Ya ce"Ni dai na faɗa miki, idan kuma kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba!". Ya fice ya barta tana ta bambami.

Inna duk a gabanta a ka yi komai, ba ta ce wani abu ba, dama idan da sabo ta saba da faɗan nasu, sai da ya fita ta ce"Sauda a nan fa ba ki da hujjar da za ki saka yara su raina matarsa, idan har ba kya son ta shiga sabgar yaranki to ya zama dole ki koma kansu ki ci gaba da kula da su, kin ga dai yadda ya gigice a kan yarinyar nan yake rawar kai, kina nan a zaune za ta gama mallake shi da kissarsu ta zawarawa, irin wannan gogaggun yaran da suke yin aure-aure wallahi ki kiyaye su,sai kin tashi a tsaye kin ɗaura ɗamara, saboda haka ni yanzu umarni nake ba ki ba shawara ba, ki kama hanya ki koma ɗakinki a yau, ki kula da ƴaƴanki, sannan ki yi iya yinki na ganin ba ta mayar da ke bora ba, kar ki yarda ta ƙwace miki mijinki da gidanki".

Sauda ta ce"Shi kenan Inna an jima zan koma".

Inna ta ce"Ko ke fa, wannan ai kina nuna mata ta fi ƙarfinki ne ba za ki iya da ita ba, saboda haka ki koma ki nuna mata gida naki ne, kuma miji da ƴan'uwan shi ma naki ne!".

Sauda ta jinjina kai cike da gamsuwa, ta tashi ta shige É—aki.

Zama ta yi ta kira ƙawarta a waya ta sanar da ita za ta koma, ta ɗora da faɗin"Don Allah ya za a yi ki haɗa ni da wannan mai maganin? Na san shegiyar tana nan ta gigita shi, bazawara ana marari za a samu miji".

Aliya ta sheƙe da dariya ta ce"Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka nuna mini ranar da Sauda za ta nemi maganin gyara zama".

Sauda ta ce"Au shaƙiyanci za ki yi mini kenan".

Ta ce"To ai ke ce kullum cikin kuri kike kina da ni'imarki ba sai kin sha komai ba, yanzu kika dawo hanya Hajiyata, zan turo miki lambarta".

Sauda ta ce"Malama yanzu fa nake so, zai yiwu ta aiko mini kayan a yau?"

Aliya ta ce"In sha Allah!".

Tana turo mata, ta kira ta a waya, suka yi ciniki gabaÉ—aya irin wanda ake cewa ban da me kishiya su ta siya na dubu É—ari, kuÉ—in gudunmawa ne dangi suka haÉ—a mata don ta yi gyaran dama, da yamma aka aiko mata da kayan, ta gama shirinta tsaf jira kawai take yi ya zo yi wa Inna sai da safe ta bi shi su tafi.

Yau ɗin Maryam shinkafa da miya ta yi, da alama yaran ba ma su taurin kai ba ne, don kuwa yau babu wanda ya yi magana a kan abinci, kowa ya ci, sannan sun tsaya ta yi musu wanka, ban da babbar da ta ce ita ce take yi da kanta dama, sai ta rabu da ita, amma dai sam sun ƙi yin fira da ita, don haka ita ma ta ke ta harkar gabanta.

Da yamma da ya dawo sai da ya tambaye ta yaran, ta ce babu wata matsala, ya yi wanka ya ci abinci, ya fita sallah ya dawo, dama idan zai fita sallar isha'i da mota yake fita saboda daga can yake wucewa gidan Inna ya yi mata sai da safe, don haka yau ma ya wuce, ya ɗan zauna bayan sun gaisa, hat yanzu ta ƙi dawo masa kamar baya, babu wata fira haka dai babu yabo babu fallasa, ya tashi zai tafi ta ce"Ka zauna".

Ya zauna yana sauraronta.

Ta ce"Sauda za ta bi ka ta koma kan ƴaƴanta, saboda haka kar na ji kar na gani, ka zama mai adalci a tsakaninsu, kar sabo ya sa a watsar da tsoho, ta farkon dai ita ce dahir ɗinka, ba zan ɗauki wulaƙanta mini ƴa ba wallahi, don haka ka ja kunnen yarinyar nan, ta kula ta kiyaye, tun da zuwa ta yi ta tarar da ita da ƴaƴanta, ba ta san faɗi-tashin da aka yi kafin ka kai matakin da kake a yanzu ba".

Ya ce"To Inna za a kiyaye in sha Allah!".

Ya tashi ya fita yana yi mata sai da safe, ya ɗan jima a motar kafin Saudar ta fito da akwatinta, ta buɗe motar ta shiga ya ja suka tafi, babu wanda ya ce wa wani ƙala har suka ƙarasa gidan, lokacin yaran suna ɗaki, Maryam kuwa tana hakimce a babban falo cikin wata fitinanniyar rigar bacci, suka shigo da sallama, niyyarta idan ya shigo ta je yin oyoyo amma sai ta yi turus ganin shi tare da wata wacce ba sai an faɗa ba ta san matarsa ce, sai da gabanta ya faɗi, ta daure ta ce"Sannunku da zuwa".
Chapter 19 · 0% Book details