← Book details Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 23

Sashe 7

Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce"Ban ga alama ba! Uwarka ce fa, ba za ka taɓa canzata ba, don haka ita ya kamata ka zaɓa ba matarka ba, yanzu idan ta kwashe maka albarka kana ganin zan bar ƴata ta ci gaba da zama da kai da rashin albarkar uwa? A'a ba zai yiwu ba, ka rabu da ita kawai shi ne maslaha".

Nazifi ya ce"A yi haƙuri don Allah, indai babata ce ta ce ma gobe za ta bar gidan, shikenan babu wani abu da zai sake tasowa kuma in sha Allah".

Uwani ta ce"To ai gata nan, idan za ta koma shikenan!" Ta tashi ta shiga É—aki.

Ya kalli Maryam ya ce"Haba Maryam, yanzu wannan har ya kai ki taho gida? Wannan Æ´ar matsalar da za mu daidaita a tsakaninmu?"

Ta ce"Kai kake mata kallon ƙaramar matsala, ni kam babba ce a wajena".

Ya ce"Wannan ma ai abun kunya ne a ce har kin yi yaji, ki rufa mini asiri ki zo mu koma".

Ta ce"Abun kunya ya wuce na zuwan uwa ta zaune a gidan yara?"

Maganar ta dake shi sosai, ya ji haushi amma ya dake ya ce"To ki tashi dai mu tafi".

Ta ce"Nazifi wai da wane yaren ake yi maka bayani? Aka ce maka wannan auren ba mai yiwuwa ba ne ba fa! Don haka ka sallame ni kawai".

Ya ce"Ba dai Gwaggo ba ce? Za ta tafi ai na faÉ—a miki".

Ta ce"Ni ko ta tafi na fasa auren, ka sallame ni idan kana son zaman lafiya".

Nazifi ya ce"Shikenan bari na tafi, zuwa gobe idan kika huce na dawo mu yi magana".

Ta ce"Nu babu wata hucewa da zan yi, za dai ka ɓatawa kanka lokaci".

Ya fice daga gidan yana jin ransa babu daÉ—i.

08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 5

A hanya ya tsaya ya siyawa Gwaggo tuwo ya tafi da shi gidan, ya miƙa mata ya zauna ya yi shiru, ta ce"Nazifi, ko daga gidan nasu kake?"

Ya ce"Daga can nake".

Ta ce"Ya kuka yi?"

Ya ce"Wallahi ita da babar tata sun ƙi fahimtata, wai zancen ma na sake ta suke yi".

Gwaggo ta ce"La ila ha illallahu! Saki kuma? Duk saboda ni? Ka ga taya ni haɗa kayan nan na bar maka gidanka yau, ba ka ba ta haƙuri ba ka faɗa mata ni ba baƙuwar zafi ba ce?"

Nazifi ya ce"Na faɗa mata za ki tafi tun da haka ta zaɓa, amma duk da haka zancen rabuwa take yi".

Ta ce"To Allah Ya kyauta".

Ganin ta janyo tsohuwar akwatinta ta fara haɗa kaya jikinsa ya yi sanyi kamar an zare masa laka, zuciyarsa kuma ta fara kumbura, sai a yanzu ne ma yake ganin Maryam da uwarta fa sun ci mutuncinsa, ya tuna ƙima sa daraja irin ta uwa, ya tuna goyon ciki, haihuwa har zuwa shayarwa da raino, ga kula da tarbiyya da karatunsa Gwaggo ba ta gajiya ba, anya kuwa idan ya zaɓi ra'ayin wata mace wacce suka haɗu rana tsaka ya wofantar da mahaifiyarsa zai gama da duniya lafiya? Sai ya ji tausayinta ya kama shi, har ya ji gara ya zaɓi rayuwa babu aure a kan ya zama silar ɓacin ranta, ya matsa kusa da ita, ya mayar da kayan ya zuge akwatin ya matsar gefe, sai ya sunkuyar da kai, Gwaggo ta kafe shi da kallo, ya ce"Gwaggo babu inda za ki je fa, ke uwata ce ba a canza uwa, amma ana canza mata, babu macen da za ta raba ni da ke dare ɗaya, zan iya rayuwa babu auren ma gabaɗaya matuƙar ina tare da albarkarki".

Ita ma sai jikinta ya yi sanyi, ta ce"Nazifi ba zai yiwu ka ƙi aure saboda ni ba, wallahi so ne yasa na zaɓi zama a kusa da kai, ka sani duk cikinku na fi sonka, ba zan so abin da zai takura rayuwarka ba, saboda haka gara na tafi ɗin kawai tun da haka ta zaɓa".

Ya ce"Gwaggo wallahi ba za ki tafi ba, indai ba za ta zauna da ke ba a gidan nan, to tabbas zan haƙura na sake ta kamar yadda ta ce".

Gwaggo ta ce"A'a kar ma ka fara, ba zai faru ba ma, tun da ka ce sai na zauna to zan kwashe kayana daga kitchen É—inta, sannan zan dinga girkina a murhuna, idan ta ga dama ma ko gaishe ni kar ta yi, tun da ba zamana take yi ba, indai hakan ya yi mata shikenan".

Ya ce"Wallahi da na san haka Maryam take da ba zan fara aurenta ba"

Gwaggo ta ce"Ka daina yiwa kanka baki, ai idan ka lura har da ƙuruciya da rawar kai irin ra yaran zamani, Allah dai Ya kyauta".

Ya ce"Amin, bari na siyo miki tuwon".

Ta ce"To kai me ka ci?"

Ya ce"Tun kunu da na sha a kasuwa".

Da sigar tsokana ta ce"Kai dai sunanka angogu ba ango ba, to ko Æ´ar taliya za ka dafa mana? Ka ga Yasmin tuwon rana da ka siyo ma ba ta ci ba, ka ganta ta yi lakur ko motsin kirki ba ta iyawa saboda yunwa, ba mu iya kunna gas É—in ba, kuma matarka ta ce za mu babbake, na ce to mu bar shi tun da ba mu san kalar kaifin bakinta ba".

Ransa a ɓace ya ce"Kamar ya za ku babbake?"

Ta kwashe labarin yadda aka yi da Yasmin ta zo kunna gas É—in ta faÉ—a masa, ya ce"Tabb ai kuwa da kun babbake É—in, gaskiya kar yarinyar nan ta sake gwada irin wannan tsautsayin, nawa take da za ta ce za ta yi girki?"

Ya tashi ya shiga kitchen É—in, sai bai ga kayan abincin ba, ya koma É—aki nan ma bai gani ba, saboda Maryam a cikin sif ta loda su ta kuma rufe ta zare mukullin ta tafi da shi, abun ya ba shi mamaki, kamar ya kira ta ya tambaye ta, sai kuma ya ga ai ba shi ya siyo ba dama gararta ce, don haka ya fita ya siyo taliyar ya dafa musu, suna ci suna fira cike da nishaÉ—i kamar suna gidansu na da.

Ƙarfe tara ya yi mata sallama ya tafi ya kwanta, sai dai ya kasa baccin, ya shiga tunanin yadda rayuwar aurensa ta fara da ƙalubale, yana son Maryam sosai, har zuciyarsa yake son ƙare rayuwarsa da ita, sai dai ya fara tunanin ita ba son shi take yi ba, tun da har wannan ƴar matsalar za ta saka ta ce ya sake ta, wajen goma da rabi ya kira ta a waya, har sau uku ba ta ɗaga ba, ya kunna data ya ganta a online, kamar ya yi mata magana sai ya fasa, ta ajiye wayar yana jira gobe ta yi, ya je ya ji yadda za su kaya da ita, don shi dai bai shirya rabuwa da ita ba.

A ɓangaren Maryam kuwa bayan tafiyar Nazifi, Uwani ta saka ta a gaba da zuga, tana nuna mata ya zama dole ta haƙura da auren nan indai tana son kanta da arziƙi, ta na ta nuna mata mutuwar aure ba komai ba ce, ballantana ita da ba ta haihu ba ma, nan da nan wani da ya fi shi zai fito ya aure ta, ta nuna mata da ka yi rayuwar aure cikin ƙunci da rashin ƴanci gara a ce ka ƙi zaman auren ma, ai dai ka san kana da cikakken ƴancinka.

Shi kuwa Baba bai sake bi ta kanta ba, ya zuba ido ta ga gudun ruwansu.

Tsaf ta kwashe karatun da aka biya mata, don haka har ta fara jin tsanar Nazifi shi da auren nasa duka, ta kuma saka a ranta ba za ta koma ba, dole ya sake ta, shiyasa tana kallon kiransa ma ta ƙi ɗagawa, lafiya ƙalau ta shari baccinta sai ta ji kamar dama ba aure ta yi ba, unguwa kawai ta je ta kwana biyu ta dawo gidan babarta mai ƙaunarta.

Washegari Nazifi tun safe ya kira ta a waya ba ta ɗauka ba, haka dai ya tafi kasuwa, sai la'asar ya tashi ya dawo gida ya yi wanka ya canza kaya ya tafi gidan nasu, da ita ya fara cin karo bayan ya shawo kwanar kayin nasu, tana tsaye a ƙofar gidan kusa da su, ta yaye hijjabinta ta baya gabaɗaya bayanta a waje, ga shi riga da siket ɗin jikinta sun ɗame ta sosai, tsaye take a kan yarinyar da take soya awarar siyarwa a ƙofar gidan, ta ɗauki ɗaya a cikin ɗan kwandon, ta kai bakinta kenan suka haɗa ido da Nazifi wanda ya tsaya yana kallonta ransa a ɓace cike da takaici.

Wani haushinsa ya kamata, ta tsaya tana ƙare masa kallo kamar yadda yake kallonta, Nazifi dogo ne siriri, baƙi ba wani kyakkyawa ba ne, shi ba kuɗi ba, sai yau ma ta ji haushin kanta, ta fara tunanin me yasa ma ta aure shi? Kamar wacce aka yiwa asiri, idonta ya rufe saboda ganin son da yake yi mata.

Ta yi tsaki bayan ta karɓi awarar da yarinyar ta miƙo mata, ta juya ta fara tafiya, kamar ba ta san wajenta ya zo ba.

Ya bi bayanta yana kiran sunanta, ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya ƙarasa ya tsaya a gabanta yana kallonta zuciyarsa cike da sonta, ya ce"Amma Maryam kar ki manta yanzu ke matar aure ce fa, bai kamata ki ɗage hijjabinki haka a titi ba, duk wanda ya kallar mini ke a haka wallahi ya cuce ni".

Ta yi masa wata kafirar harara ta ce"Malam me yake tafe da kai?"

Ya daure ya yi murmushin yaƙe ya ce"Ango ya zo wajen amaryarsa a tambaye shi dalili? Zuwa na yi mu tafi mana".
Chapter 7 · 0% Book details