← Book details Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 23

Sashe 18

Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar ya zo zance yake cewa"Maryam a gaskiya ba zan ɓoye miki ba, matata ba tana da kishi sosai, tun tuni nake son ƙara aure ta hana ni, dama kuma dai lokaci bai yi ba, amma a yanzu ina ji a jikina ke ɗin ce ta aure in sha Allah! Saboda na shirya fito na fito da ita a wannan karon".

Maryam ta ce"A'a don Allah ka lallaɓata, kar ka rabu da matarka saboda ni".

Ya ce"Ba zan rabu da ita, amma aure dai babu fashi, ke kuma sai ki shirya zama da ita, kar ki ce za ki rabu da ita ta ci tuwo a kanki, ku zauna lafiya dai kawai saboda ni ma hankalina ya kwanta, tun da kin ga gida É—aya za ku zauna".

Maryam ta ce"Ni idan da hali ka raba mana gida mana".

Ya ce"Wallahi haka na tsara tun farko, ginina na mata biyu ne ita ma ta sani kuma tun da na gama ginawa na sanar mata zan ƙara aure".

Ta ce"To shi kenan, Allah Ya sassauta zuciyarta".

Ya amsa da amin, sannan ya nuna mata vedion gidan a waya, gida ne babba mai kyau, daga farfajiyar tsakar gida babba sai a shiga babban falo, mai ɗauke da manyan kujeru, kayan kallo da firji komai dai an saka falo ya haɗu, akwai dining a ciki, sai kitchen da banɗaki, sannan a shiga cikin gidan, ɗakin da zai saka Maryam ɗin ne a farko, ciki da falo da banɗaki a ciki, ita ma na uwar gidan haka yake, sai ɗakin shi da kuma ɗakunan yara guda biyu, sannan wani banɗakin a tsakar gida, ga bantileson mai ɗauke da shuke-shuke da famfuna, gidan ya burge ta, ta miƙa masa wayar tana cewa"Ma sha Allah ya yi kyau".

Ya ce"Zuwa gobe jibi za a gama kayan É—akinki, sai a saka, zan ba ki kuÉ—i sai ki sayi kayan kitchen ko? Gobe muka yi da Æ´an gidan namu za su kawo kayan lefe".

Ta ce"Allah Ya kaimu".

Ya ɗan yi jim kafin ya ce"Don Allah ku yi haƙuri da abin da ƙila ƴan'uwana za su iya yi a yayin kawo lefen, kin san da yake Sauda ƴar'uwata ce, auren gida aka yi mana, kuma ita Innar tawa ita ta riƙe ta tun tana ƙarama, da ta isa aure ta aura min, to yanzu haka tana nan tana taya ta kishi, don ban faɗa miki ba ne ba ma, amma Sauda ta yi yaji tana can gidanmu, kuma Innar ta goya mata baya ta ƙyale ta, sannan akwai wasu ƙananun maganganu da suke yi, wai ai ba zaman aure kike yi ba, ko na aure ki za ki fita, sai dai kin toshe kunnuwanki gaskiya".

Jikin Maryam ya É—an yi sanyi ta kasa cewa komai ta tafi duniyar tunanin kalar zaman da za su yi.

Alhaji ya ce"Maryam kin yi shiru, ina son ki, kuma sannan zan kwatanta adalci daidai gwargwadon iyawata a tsakaninku, ba zan ga wata ɓaraka na ƙyale ba, amma kin san komai sai kin yi haƙuri kafin ki ci riba".

Ta ce"To Allah Ya ba mu zaman lafiya bakiÉ—aya".

Suka yi sallama Maryam ta shiga gida a sanyaye, da a da ne da tuni ta juyewa Uwani komai, amma a yanzu sai ta yi shiru ta bar abun a cikinta tana fatan Allah Ya ba su zaman lafiya.

Washegari ƴan kawo lefe suka zo, mata ne su biyar, suka kawo akwati guda huɗu, kuma babu laifi ya saka mata kaya sosai, duk da sun rage a cewarsu ai wannan kayan bai cancanci bazawara ba, ƴan'uwa da aka gayyato karɓar lefe da ƙawayen Uwani suna ta ɗaga kaya suna cewa"Ma sha Allah! Kaya sun ce".

Wata cikin masu kawo kayan ta taɓe baki ta ce"Iyyi kaya sun yi fa! Sai fatan Allah Ya sa kunun banza ya ƙare a farau-faru ɗin banza".

Wata ta ce"A to, tun da dai amaryar an ce ba mazauniya ba ce a gidan aure".

Wata cikin dangin babar Maryam ta ce"Daɗin abun dai shi ya gani ya yaba, sai a bar shi da zaɓin shi".

Wata ta ce"Kuma mutuwar aure ai ƙaddara ce, ƙaddara kuwa tana kan uban kowa, ko a yau idan uban mutum ya kwanta ya mutu uwarsa ta zama bazawara".

Wata cikin masu kawo kayan ta hasala ta ce"Kin ga kar ki zage ni, wallahi kar ki sake, dama an faɗa mana ba gidan arziƙi ba ne, ƙaddara ce da biyewa zuciya ya kawo shi".

Nan aka fara maganganu, hayaniya ta kaure a gidan, aka rabu baran-baran dutse a hannun riga, ko tukuici ba a samu damar ba su ba, suka tafi.

Wannan abu da ya faru ya ƙarawa Maryam baƙinjini a wajen dangin Alhaji Haruna, musamman mahaifiyarsa da ta cika ta yi fam kamar za ta yi bindiga, musamman idan ta kalli Sauda da yaran a gida, a cewarta ya zaɓi wata mara tarbiyya ya watsar da matarsa ta ƙuruciya da ƴaƴansa, don haka fushi take yi da shi sosai.

A haka dai Alhaji ya toshe kunnensa, suka yi ta hidimar gabansu shi da Maryam, har ranar auren ta zo, aka ɗaura aurensu, an yi yini a gidan su Maryam saɓanin shi da babu abin da aka yi, ko abincin ƴan ɗaurin aure a can gidan matar baban shi aka yi, shi dai yana ta zumuɗin zuwan amarya babu abin da ya dame shi.

Bayan sallar isha'i aka ɗauki Maryam aka kai ta gidan miji a karo na huɗu, wanda take fatan ya zama na ƙarshe da za a sake ɗaura aurenta, ma'ana wannan aure ne ta yi na mutu-ka-raba.

(To fa! Ya kuka hango zaman Maryam a irin wannan gidan?)

Littafin nan na kuÉ—i ne a kan naira 500 kacal!
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay

08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3

PAGE 14

Suna ƙule a ɗakinsu baban nasu ya dawo, Maryam ta tare shi ranta fess, ta haɗa masa ruwan wanka ta kai banɗaki, abin da ba ta taɓa yi wa sauran mazan da ta aura ba, ko ruwa a buta ba ta taɓa zuba musu ba, amma shi wannan da yake zaman gaskiya ta zo ta ɗaura ɗamarar yi masa hidima iyakar iyawarta, tsaf ta taya shi shiryawa bayan ya fito, sannan ta ja hannunsa kamar wani ɗanta zuwa falo, ta kawo masa tuwon, tana ba shi a baki suna ta firarsu cike da nishaɗi, har ya yi mamakinta saboda shi kansa ya san kafin auren ba wani son shi take sosai ba, kiran sallar magriba ne ya tashe shi, ya yi alwala ya tafi masallaci yana jin shi fess da shi, ya manta rabon da ya samu kulawa da soyayya irin wannan, sautari sai bayan magriba yake yin wanka saboda sai ya ce Sauda ta dafa ruwan take dafawa, wataran ma a haka yake kwanciya ko ya yi da na sanyi, sannan Momy ce mai kai masa abinci dining, idan ma ya shiga ɗakinsa yana wani aikin ko kuma ya shigo da wata damuwar, babu ruwan Sauda da zuwa ta ji dalilin ƙin fitowarsa, sai dai ta aiko masa da abincin ɗakin nasa, sannan babu ruwanta da tambayar shi fita unguwa, indai ka ga ta tambaye shi sai dai idan nesa sosai za ta je, gidan Inna kuwa idan za ta je tun rana idan ta tafi sai dare idan ya je yi mata sai da safe su taho tare, babu ruwanta da me zai ci ranar, babu dai wata kulawa akwai matsaloli birjik, wanda shi ne dalilinsa na son ƙara auren, kuma tun yau ya fara tunanin za a samu canji in sha Allah!

Ya dawo daga masallaci Maryam ta ga bai yi maganar yaran ba, ta dai leƙa bayan fitarsa ta ce duk su yi alwala su yi sallah.

Ta ce"Alhaji dama ina so mu yi magan a kan yaran nan".

Ya ce"To, wasu yara?"

Ta ce"Yaranka".

Ya ce"Me ya faru? Ba za ki samu matsala da su ba in sha Allah! Kin ga ma yara ne, uwar ma don Allah ki kau da kai ga matsalolinta".

Ta ce"Ba wata matsala ba ce, ka ga yau taliya na dafa da safe, na ba su suka ce wai ba sa cin taliya, sai kowaccensu ta shiga zaɓar abin da take so, ni kuma na ga ba zao yiwu na yi girki har kala huɗu ba, ko hakan bai zama almubazzaranci ba ai ka ga ni ma ina buƙatar hutu, tun da ba bautarsu na zo yi ba, sannan ba ma tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓin abin da za su ci, na ce su tsayar da guda ɗaya, suka ce tuwo, shi ne na yi, loma ɗaiɗai suka yi suka ce mini ba daɗi, ƙarshe sai suka sha golden morn suka ƙule a ɗaki".

Alhaji ya ce"Ikon Allah! Wai kina nufin su yaran suna gidan nan? Waye ya kawo su?"

Maryam ta ce"Wai dama ba ka sani ba? Daga makaranta mai adaidaita sahu ya kawo su".

Ya ce"Yanzu suna ina?"

Ta ce"Suna É—aki".

Ya shiga ƙwala musu kira ransa a ɓace, suka fito, Kausar da Momy suka haɗa baki wajen faɗin"Abba yunwa muke ji, ba mu ci komai ba".

Ya daka musu tsawa da faÉ—in"Ku nemi wajen zama!".

Suka zauna duk suka sha jinin jikinsu, saboda Abban nasu ba mai yawan faÉ—a ba ne.

Ya ce"A cikinku waye ba ya cin taliya? Yaushe kuka daina cin taliya?"

Duk suka yi shiru suna raba ido.

Ya ce"Wato ku har kun yi girman da za ku yiwa babba rashin kunya? Ku sa ta yi tuwo ku ce babu daÉ—i?"

Ya kalli Maryam ya ce"Idan akwai ki sako musu".
Chapter 18 · 0% Book details