Sashe 11
Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuwa Maryam da kuka sosai ta shiga gidan nasu, lokacin Baba yana tsakar gida yana cin abinci, Uwani da take ta jiran dawowar tata ta miƙe tana rafka salati kamar ba ta san komai ba ta ce"Ba dai yaron nan sakinki ya yi ba?"
Baba ya yi mata wani kallo bai ce komai ba, tun da ya san dama sakin suke so.
Maryam ta shige ɗaki tana ƙara sautin kukanta, Uwani ta mara mata baya, tana cewa"To ai ya isa haka, na ji daɗi da kika shigo da kukan kissar nan wallahi, kin ga babanki zai ce ba da son ranki komai ya faru ba".
Ganin Maryam ta ƙi daina kukan kuma ta ƙi ɗagowa sai ta sha jinin jikinta, ta ce"Maryam to ko dai kina son mijinki?"
Sai a lokacin ta É—ago, Uwani ta yi arba da kumburarriyar fuskarta, ta ce"Innalillah wa inna ilaihi raji'un! FaÉ—uwa kuka yi a adaidaita sahun?"
Tana kuka ta ce"Dukana ya yi".
Uwani ta ji daɗi a ranta, ta ce'Allah Ya ƙara, kaɗan ma kika gani'.
A fili kuwa ta ce"Duka!? Duka dai wanda na sani?Me kike yi da ba ki É—auki turmi kin rotse shi ba?"
Sai ta yi waje tana"Malam! Mun shiga uku...".
Baba ya katse ta da faÉ—in"Kun shiga uku dai".
Ta ce"Shigo ka ga fuskar yarinyar nan, bayan sakin da ya yi mata, har da yi mata dukan kawo wuƙa, fuska ta kumbura kamar an saka mata yis".
Baba ya ci gaba da cin abincinsa bai ce komai ba.
Ta ce"Ga duka ga tsinka jaka? Wallahi ba zata saɓu ba bindiga a ruwa, sai na bi mata kadinta!".
Ta shiga ɗakin, ta tashi Maryam zaune tana cewa"Bar kukan haka, wallahi sai na ƙarti daidai da shi sun yi masa duka, ke dai tun da kin rabu da ƙaya Alhamdulillah!".
Ta fita ta kunna wuta, ta ɗora ruwan zafi, daidai nan Sunusi ya shigo, Baba kuma ya fita, ko sallamar da ya yi ba ta amsa ba, ta tare shi da faɗin"Sunusi ka ga abin da wannan tambaɗaɗɗen yaron ya yi wa ƴar'uwarka? Ya yi mata dukan mutuwa sumanta uku, kuma ya sake ta, da ƙyar ta kawo kanta gidan nan tana jiri tana faɗuwa".
Ya ce"Subhanallah! Ya sake ta kuma? Ko fa sati ba a yi da auren ba, gobe Lahadi shi ne zai cika sati É—aya cif".
Uwani ta ce"Ubanka kai da satin, ina maka zancen duka wato kai mutuwar auren ce ma ta dame ka!".
Ya ce"To babarmu kin san wane tudu da gangare suka hau har ya dake ta? Kin san fa Maryam ba ta da kunya, ƙila zagin shi ta yi".
Ta ce"Kai dalla gafara, kar na gwabje ka, ashe dai bayan raina ba za ka iya ƙwatarwa ƙannenka ƴanci ba, Allah wadaran naka ya lalace".
Sunusi ya buÉ—e É—akinsa ya shige, ita so ta yi ya fusata ya kwashi abokansa a daren su je su yiwa Nazifi duka, ashe ba zai iya komai ba.
Sai da ruwan ya yi zafi sosai sannan ta juye a baho ta kai banÉ—aki, ta shiga É—akin ta taso Maryam ta ce"Maza ki je ki yi wanka, ki gaggasa jikinki sosai da zani, idan ba haka ba ba za ki iya bacci ba, Allah Ya saka miki".
Maryam ta yi wanka, ta zuba mata abinci ta ci, ta kwanta nan take kuwa sai bacci ya É—auke ta.
Washegari Uwani ta kira ƙawayenta da maƙota suka je suka kwashe kaya tass, a ranar kuwa ta siyar da su aka ajiye kuɗin. Sai bayan kwana biyu da Maryam ta nutsu sannan ta gane an kwashi wasu daga cikin kayan lefen, amma dai ta yi shiru ba ta ce komai ba, don ta fi tunanin a cikin masu kwaso kayan ne wata ta ɗiba.
Nan fa ta gyara zaman idda, ta manta da ta taɓa rayuwa da Nazifi, kullum Uwani ƙara koyar da itw darussa take yi, ita kuma tana kwashewa tana adana su a kanta, a haka har ta gama iddarta, ta ɗiɗɗinka kayan lefenta, tana shiga tana fita, sai Uwani ta ba ta shawarar ta fara sana'a don zawarci sai da sana'a, da fari Baba ya hana ya ce ba za ta yi ba, to akwai ƙawarta da take siyar da abinci a tashar kusa da layin nasu, Maryam sai ta tsiri cin kwalliya ta je ta zauna kawai a wajen, suna kwashewa da maza, Baba ya yi faɗan har ya watsar, ƙarshe abokinsa ne ya ba shi shawarar gara ma ya barta ta fara sana'ar don a san zaman tashar nata mai dalili ne, don haka ya barta, ta fara dafa shinkafa da taliya tana kaiwa tashar, uwar kwalliyar da take ci da tsaftarta, uwa-uba kuma yadda take ƙawata abincin, da yadda take sakin baki su yi ta fira da maza shi yake ƙara janyo mata hankulan maza, da ta fito za ta siyar ta koma gida, ta ƙirga ribarta cass ta adana, nan da nan kuwa zawarawa suka fara tururuwar zuwa wajenta, amma sai Uwani ta nuna mata kar ta sake ta ce za ta yi aure yanzu, ta bari sai ta tara wani abu tukunna, don haka duk wanda ya zo da zancen aure sai ta saita masa hanya, wanda kuma dama su ƴan a bi yarima a sha kiɗa ne, ƴan rage dare sai ta yi ta cin kuɗinsu, amma hakan ba ya saka ta bawa wani jikinta, sai dai ta yi ta maka wayo, har ka gaji ka kama gabanka.
Ta kusa shekara a gida, ta haɗu da wani Hamza, lokaci ɗaya ta ji tana ƙaunar shi, kuma za ta iya auren shi, don haka duk yadda Uwani ta so nuna mata ba yanzu ba, ba ta yarda ba, ƙarshe dai ta rabu da ita, suka sasanta tsakaninsu, babu jimawa Hamza ya turo manyansa, bayan gabatar da bincike an ga ba shi da matsala aka saka ranar aurensu wata biyar, suka ci gaba da soyayyarsu suna kuma shirin aure.
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
PAGE 8
A wannan karon Uwani ta dage sosai wajen yiwa Maryam karatunta, ta riga ta gama hawa gada ɗoɗar, ta yarda zawarci ba komai ba ne, don haka ba za ta ɗauki raini ko tauye haƙƙi daga wajen miji da danginsa ba, tun da miji goma ba uba goma ba ne. Kusan rabin kayan ɗakin da kuɗinta ta yi shi, Hamza bai yi lefe ba, kuɗi ya bayar ta sayo kaya ta ɗinɗinka, aka ɗaura aure aka kai amarya ɗakinta, gida ne madaidaici, mai ɗauke da babban falo da ɗakuna uku a cikinsa, sai kitchen da banɗaki, gidan ya yi kyau babu laifi komai fess.
Maryam tana son shi, don Hamza ɗan soyayya ne, sosai take tarairayarta hakan ya ƙara mata ƙaunar shi a zuciyarta, kuma ƴan'uwan shi ma suna sonta suna ba ta kulawa da janta a jiki, don sai da ta yi sati ɗaya ta fara girki, tun washegarin ranar da aka kaita ake aiko musu abinci daga gidansu, fal kula su ci su zubawa baƙi, na safe kawai take yi, ga gararta da ta zo da ita, cefane kawai yake yi a yi lafiyayyen girki.
Uwani tana ta baza kunne da ido ta ji ta inda matsala za ta ɓullo ta ji shiru, ta sha ƙara jaddadawa Maryam idan da matsala fa kar ta ɓoye ta cuci kanta, amma sai ta ce mata lafiya ƙalau suke zaune, takaicin duniya ya ishe ta kuwa, kullum da lamarin take kwana.
Watan Maryam ɗaya a gidan ta samu ciki, mai masifar laulayi kuwa, ga kwaɗayi sosai, sai ta ce a siyo mata abu idan aka kawo kaɗan za ta ci ta fara kwara amai, ga muguwar kasala ta sa kwalliyar ma ta daina yi, kuma ta tsani Hamza ya matso kusa da ita, sai ta ji ba ta son warin jikinsa ko da kuwa yanzu ta fito daga wanka, indai za su kasance to fa sai ta yi ta kwara amai, ƙarshe sai take komawa wani ɗakin ta kwana, tun Hamza yana daurewa har abun ya fara ba shi haushi, duk wata ƴar soyayya da kulawa ta daina ba shi.
Watarana ya sameta kwance a É—aki, yana haÉ—e rai ya zauna ya ce"Tashi za mu yi magana".
Ta tashi tana kallon shi, ya ce"Maryam na ga wannan cikin yana wahalar da ke, kalli yadda duk kika rame kika zama wata iri, duk kin kojale..."
Ganin yana maganar yana taɓe baki kamar mai ƙyamarta ta katse shi da faɗin"Hamza! Ni kake cewa na kojale? Kar fa ka manta ko me ya same ni sanadin cikinka ne, dama na lura wani kallon rainin hankali kake yi mini kwana biyun nan!". Ta ƙarasa maganar a hasale.
Ya ce"Kin ga ni ban ce ki É—aga mini murya ba, masalaha ce na zo da ita".
Ta yi shiru tana sauraron shi . Ya ce"Maryam kin ga fa har yanzu ba a yi wata biyu da aurenmu ba, ɗan amarcin nan ba mu ci ba, ni da na so a ce matata sai ta yi shekara ɗaya ko wata shida haka kafin ta samu ciki, kin ga lokacin an ci amarci an fara marmarin samun ɗa ko ƴa, amma yanzu kalle ki fa don Allah, ni yanzu a shawarata kawai a cire cikin nan, tun da ba ƙwari ya yi ba, sai na siyo miki ƙwaya ki dinga amfani da ita, idan aka kwana biyu kika huta kamar nan da wata shida haka sai ki ɗauki wani cikin, don ni gaskiya yanzu duk na takura gidan ma ba daɗi yake yi mini ba".
Haushi ya kamata ta ce"Ka gama?"
Ya ce"Na gama".