← Book details Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 23

Sashe 21

Miji Goma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ajiye mata ledar hannunsa, ya ciro kuÉ—i a aljihunsa ya ajiye mata ya fice, bai tarar da kowa a falon ba, sai ledar da ya ajiyewa Inna, cike da dumuwa ya bar gidan. Amma ko da ya je gida ya tarar da amaryarsa sai ransa ya yi fess, yana son Maryam sosai, suka sha amarcinsu hankali kwance har ta mantar da shi yana cikin damuwa.

Washegari ya tafi kasuwarsa, ita kuma ta gyara gidan, tana ta baƙi jefi-jefi da maƙota da ƴan'uwa, maƙotan dai duka ƙawayen Sauda ne, don haka gulma ce kawai take kawo su, kowacce idan ta shiga ta ganowa idonta sai ta kira Sauda ta yi mata sharhi, wanda hakan bai ƙara mata komai ba, sai baƙinciki da tsanar Maryam ɗin, ita kuwa Maryam dama ta yi tunanin za a yi hakan, don haka babu wata mace da ta sakarwa fuska, kadaran-kadahan take karɓarsu.

Wajen ƙarfe biyu ta gama girki tana sallah ta ji ana buga gidan, an daɗe ana bugun saboda tana tayar da sallar aka fara, da ta idar ta taho da sauri ta buɗe, sai ta ga yara ne su huɗu da unifom a jikinsu, jikinta ya ba ta ƴaƴan mijinta ne, sai mai adaidaita sahun da ya ajiye su ya ƙaraso da waya a kunnensa yana cewa"Ai ga shi ma ta buɗe".

Don kuwa da ya ga yaran suna ta bugawa ba a buɗe ba, sai ya kira Sauda ya faɗa mata, ta kuwa harzuƙa ta miƙe tsaye tana zage-zage da cewar gidan ubanta ne da za ta hana su shiga?

Ya miƙawa Maryam babbar jakar dake hannun shi yana cewa"Ga shi mamansu ce ta ce na kawo su".

Maryam ta karɓa ta ce"To ka gaishe ta".

Ta kalli yaran ta ce"Ku shiga, sannunku da zuwa".

Babu wanda ya amsa, ballantana su gaishe ta, wannan huÉ—ubar mahaifiyarsu ce, suka shige É—akin kwanansu, Maryam ta biyo su da jakar kayansu ta ajiye tana cewa"Ku cire unifom, sai na yi muku wanka ku canza kaya ko?"

Momy da take babbar ta ce"A'a, mun yi wanka da safe".

Ta ce"To ku canza kaya ku fito ku ci abinci".

Suka fara kiciniyar cire kayan, ban da Momy da ta ja ta tsaya tana ta ɓata rai, sai da Maryam ta fita sanan ta fito da duka kayan cikin jakar, sai ga waya keypad ta bayyana, ta ɗauka ta shige banɗaki, ta danna ta kira babarsu a waya, Sauda tana ganin kiran ta miƙe ta shige ɗaki, don ko Inna ba ta san da wannan shirin nata ba, tana ɗagawa ta ce"Momy yaya aka yi?"

Momy ta ce"Ta ce mu yi wanka na ce mata mun yi, shi ne ta ce mu fito mu ci abinci".

Sauda ta ce"To ko me ta dafa ku ce ba kwa ci, kowa ya zaɓi abin da yake so ya ci, kin ji ko?"

Ta ce"To, amma wallahi Nana ce uwar kwaÉ—ayi, na san ci za ta yi".

Ta ce"Ki gargaɗe ta, ki ce idan ta ci za ta mutu, ta ce doya take so ta ci, ku kuma ku zaɓi wani abun kowa na shi da ban".

Ta ce"To"

Ta ce"Ki ɓoye wayar nan fa sosai, ki saka a ƙarƙashin katifarku, kuma kar ki fita ko falo da ita".

Ta kashe wayar ta fito ta faki idon ƙannen nata ta ɓoye, sannan ta ba su kayan da za su saka, ta zaunar da su ta ce"To Umma ta ce ko me ta dafa kowa ya ce ba ya ci, ke Nana ki ce doya da ƙwai za ki ci, ke Kausar ki ce shinkafa da wake, ke ke kuma Ummi ki ce shinkafa jollop, idan kuma shinkafar ta dafa sai ki ce macaroni, wallahi Umma ta ce duk wacce ba ta ce haka ba sai ta ci ubanta".

Duk suka gyaÉ—a kai, sannan suka fito a tare, Maryam tana falo tana chart, ta ce"Kun fito?".

Ba su ce komai ba, ta tashi ta shiga kitchen ta juye musu taliyar da ta dafa da miya, leda É—aya ce dama ta dafa ko ci ba ta yi ba, plate biyu ta yo ta kawo ta ajiye a gabansu tana cewa"Ku yi maza ku ci".

Daidai lokacin kiran Uwani ya shigo wayarta, ta É—aga tana gaishe ta, Uwani ta ce"Oh! Maryam har na fara kewa, ya kike ya gidan?"

Ta yi ƴar dariya ta ce"Lafiya ƙalau".

Ta ce"Babu wata matsala dai ko? Kin san zama da kishiya".

Da a da ne sai ta faÉ—a mata ga shi har yaran shi sun zo, amma yanzu kuwa ta ce mata babu komai, kuma ba ta ma faÉ—a mata uwar gidan ta yi yaji ba, ko da Æ´an kai amarya suka zo ma duk a zatonsu É—aki ta shiga ta kulle saboda kishi.

Suna gama wayar ta juyo ta ga yaran ba su da niyyar sakkowa su ci abincin, ta ce"A'a! Ya ba ku fara ci ba? Ko sunayenku ba ku faÉ—a mini ba ma, ku gama ci ku zo mu yi fira ko?"

Momy ta ce"Mu ba ma cin abinci a ƙasa sai a dining, kuma ba ma son taliya".

Ta ce"Ba kwa son taliya? Kwata-kwata ba kwa ci a gidan?"

Ta ce"E".

Maryam ta ce"To me za ku ci?"

Momy ta ce"Ni tuwo nake so".

Ummi ta ce"Ni kuma jollop É—in shinkafa".

Nana ta ce"Ni doya da ƙwai".

Kausar ta ce"Ni shinkafa da wake, da mai da yaji da salak da tumatur da albasa, da cocomba". Ta ƙarasa da karsashi, don dama Momy kowa abin da ta san ya fi so ta ce ya faɗa.

Maryam ta tsaya kallon su da mamaki, ba sai ta wahalar da kanta da tunani ba, saboda ba zai taɓa yiwuwa ta biyewa yara ta yi girki kashi-kashi ba kamar wata ƴar aiki, girki kala huɗu? Sannan wannan ai ba tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓar abincin da za su ci, don haka ta ce"Duk na ji, amma fa sai dai ku zaɓi abu guda ɗaya dukanku, saboda kun ga idan na yi girki har kala huɗu na yi almubazzaranci, don haka ku tsayar da abu ɗaya".

Duk sai suka kalli Momy tun da ita ce shugabar tawaga, ta ce"To ai mu ba ma cin taliya".

Ta ce"Na ni ba za ku ci taliya ba, ku zaɓi kala ɗaya sai na dafa muku".

Ta ce"Sai dai a yi mana tuwon shinkafa miyar agushi".

Maryam ta ce"Ni ba ni da agushi, sannan ba zan takurawa babanku ba yana kasuwa, amma akwai wake, zan yi muku miyar wake".

Da gaske Nana ba ta cin miyar wake, don haka ta taɓe fuska za ta fara kuka ta ce"Ni dai ba zan ci ba".

Kausar ta ce"Nana ba ta cin miyar wake".

Maryam ta ce"Zan dafa mata indomi".

Ta wuce kitchen É—in, a ranta tana mamakin yadda aka sangarta yaran, ita idan Æ´aÆ´anta ne gaskiya ba za ta saki fuskar da za su yi mata haka ba, amma su ma É—in muddin a wajenta za su zauna to kuwa tabbas sai ta saita su. Ta É—ora tuwon da yake ta tarar da komai har farar shinkafar da akwai, da yake gas É—in mai huÉ—u ne tana wanke waken sai ta É—ora miyar, sannan ta zauna ta ci taliyar.

Tana tafiya kitchen Momy ta tashi ta shige É—akinsu, ta É—auki waya ta shiga banÉ—aki ta kira Ummansu, tana É—agawa ta zayyane mata komai, Sauda ta ce"Amma dai Allah Ya yi miki albarka Momy, yanzu kin san yadda za a yi?"

Ta ce"A'a".

Ta ce"Idan ta gama tuwon ku yi loma É—aya ku ce babu daÉ—i ku ba kwa ci kun ji ko? Ko kun ji daÉ—i fa kar ku ci".

Momy ta ce"To Umma yunwa muke ji fa".

Ta ce"Idan kun ƙi ci sai ku shiga kitchen ku ɗauki golden morn ku haɗa ku sha, idan ya dawo ku ce masa ba ku ci komai ba yunwa kuke ji, ku ce ba ta ba ku tuwon ba".

Momy ta ce"To". Amma a sanyaye, saboda yunwa take ji.

Sauda ta ce"Ki yi haƙuri kin ji ƙawata, ni na san me zan siya muku".

Ta ce"To".

Ta ajiye wayar, sai da Maryam ta koma kitchen sannan ta sake tsarawa yaran, ta ce inji Umma, ta ce sai sun ƙi ci za ta dawo, ai kuwa suka yarda.

Sai da ta sauke tuwon ta dada indomin saboda ta manta, ta zubo ta kawo musu,lokacin har ƙarfe uku ta gota, ta ajiye ta ɗakkowa Nana indomi, ita kam ana ajiyewa ta fara ci ta manta da gargaɗin yayarsu saboda yunwa take ji, kuma dama duka-duka shekararta huɗu, su kuwa manyan ba su saɓa ba, loma ɗaya kowa ya yi a layi, idan wannan ya ci, sai wannan ya ci, sai suka tsaya suna kallon tv, Maryam ta ce"Ya dai? Ku ci mana".

Momy ta ce"Ni dai ba na ci, na ji babu daÉ—i, ko Kausar?"

Su ma suka haÉ—a baki wajen faÉ—in"E babu daÉ—i".

Ran Maryam ya ɓaci, lallai sun yi sa'a a wannan karon zama ta zo na mutu-ka-raba, da babu abin da zai hana ta fesawa babbarsu mari, ba ta ce komai ba, ta kwashe ta kai kitchen, babbar ta shige ɗaki, duk suka bi ta, babu jimawa kuma ta fito ta shiga kitchen ɗin Maryam ta bi bayanta, ta tarar tana haɗa golden morn, ta haɗa shi kofi uku ta ƙwala musu kira, suka fito suka ɗauka suka koma ɗaki, ita kuwa Nana sai ta zauna a nan falon tana kallo.

Maryam ta cika da mamakin yaran sosai, ta kuma saka a ranta ta san zaman da za ta yi da su.

Da yamma da ta yi baƙi sai ta ba su taliyar, tuwon kuma ta rufe musu shi, tana jira babansu ya dawo ta sanar masa ta ga matakin da zai ɗauka.

LITTAFIN NAN NA KUÆŠI NE AKAN NAIRA 500
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay

08028966015

*MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3

PAGE 14
Chapter 21 · 0% Book details