← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 24

Sashe 9

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fulani Sadiya tana fita daga É—akin Takawa kai tsaye É—akinta ta nufa zuciyarta fes, sai da ta shiga É—akinta sannan ta fara kai kawo cikin farinciki ta ce.
"Fulani Zainaba ke kaɗai kika rage mini. Tun da har Fulani Khadija ta tafi, na tabbata kema ta ki tana hanya. Sai na tabbatar da na aiwatar da ƙudurina, a kan duk wanda zai ba ni matsala a doron ƙasa koda kuwa Sarki Gambo ne."

Motsi ta ji daga cikin ɗakinta, da sauri ta ɗaga labule ta shiga. Cikin girmamawa Baiwa Sakina ta zube a ƙasa ta ce, "Barka da shigowa ranki shi daɗe."

"Tun yaushe kike a nan?"

Fulani Sadiya ta furta da sauri, saboda ba ta yi tsammanin akwai wani a É—akin ba.
"Allah Ya taimake ki kafin fitarki kin manta kin saka ni gyaran É—aki. Amma idan na yi laifi ki gafarta mini ranki shi daÉ—e."
Baiwa Sakina ta furta tana sake russunar da kai ƙasa, saboda yadda gabanta yake faɗuwa. Domin wani irin tsoron Fulani Sadiya ne ya mamaye ta.

"Sakina!"
Fulani Sadiya ta kira ta da wata irin murya, a sanyaye Baiwa Sakina ta amsa. Sannan Fulani ta cigaba da cewa.
"Ki ji kamar ba ki ji ba, idan kika yi yunƙurin furta kalma ɗaya daga cikin abin da kika ji. Na rantse da girman Yesu mai ceto, sai na sa an yi miki azabar da ba a taɓa yi wa wani mai numfashi a cikin gidan nan ba, sai na wulaƙanta ruhinki ta yadda za ki dinga yagar naman jikinki kina ci da haƙoranki."
A razane Baiwa Sakina ta É—ago, sai ta rarrafa a guje zuwa gaban Fulani ta ce.
"Ki yi mini afuwa Fulani, Na tuba wallahi ba zan taɓa aikata miki wannan kuskure ba."
Fulani Sadiya ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce. "Daga yau idan kika sake kika ɓoye mini wani abu, wallahi ranki zai yi mummunan ɓaci. Idan kika bari na gano wata manaƙisar da kike ɓoye mini za ki yaba wa aya zaƙinta. Kuma daga yau, za ki fara shiga cikin wasu al'amuran da nake gudanarwa a bayan fage."
A wannan karon ma cikin tsoro haɗe da girmamawa Sakina ta amsa mata, daga ƙarshe Fulani Sadiya ta sallame ta.

Jikin Baiwa Sakina yana rawa ta nufi sashen bayi, tana mamakin jin miyagun abubuwan Fulani Sadiya take aikatawa. A ɓangare ɗaya ta shiga fargabar rantsuwar da ta yi da Yesu mai ceto, saɓanin Allah Ta'ala da ta san gabaɗaya cikin masarautar suna bautawa.

Baiwa Sakina tana shiga harabarsu ta hangi Ridwan zaune a gefe, daga can nesa tsirarun yaran bayi ne suke ta wasanninsu. Ƙarasawa ta yi wurinsa ta ce, "Ridwan!"

ÆŠagowa ya yi ya kalle ta, nan take ta ga idanunsa sun kaÉ—a jajir kamar sabon borkono. Gabanta ne ya faÉ—i, don haka ta matsa kusa da shi ta ce.
"Me yake damunka Ridwan?"

"Wallahi sai na kashe ta."
Ridwan ya furta cike da ɓacin rai, Baiwa Sakina tana shirin sake magana ta ga ya furzar da wani gudan jini daga bakinsa. Tana nan tsaye ta ga ƙasar wurin da jinin ya ɗiga ta rauzaye ta faɗa ciki. Tsoro ne ya sake mamaye ta, duk da ba a wannan lokacin Ridwan ya saba baƙin al'amura masu ɗaure kai ba. Amma na wannan lokacin ya tsorata ta, don jin kalmar kisa da ta yi ya firgita hanjin cikinta.

"Ridwan me kake faÉ—a haka? Duka shekararka goma amma har kake furta kalmar kisa, wa za ka kashe? Kuma a ina ka ji wannan kalmar?"
Baiwa Sakina ta kawar da tsoron da ke kwance a saman ƙirjinta, ta furta masa tana kallon yanayinsa. Manyan idanunsa ya ɗago ya zuba mata, har sai da ta ji tsoro ya mamaye ta. Sai ya kawar da kai cike da rashin damuwa ya ce.

"Ba ki santa ba."

"Kai a ina ka santa?" Baiwa Sakina ta furta cikin sauri, Ridwan ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Tana masarautar Judala, masarautar Sarki GiÉ—a..."

"Kul."
Baiwa Sakina ta furta tana toshe masa baki da hannunta, jikinta yana rawa ta ja hannun Ridwan É—aki. Sai da ta zaunar da shi a kan gado sannan ta ce.
"Kul Ridwan, koda wasa kada na sake jin Masarautar Judala a bakinka. A ina ka ji sunan? Ko kana son wani ya kai wa Mai martaba tsegumi a hallaka mini kai? Ba ka san furta sunan masarautar a cikin wannan masarautar kusan daidai yake da hukuncin kisa ba?"
Kawar da kansa ya yi gefe yana taɓe baki sannan ya ce, "Haka kawai na ji ba na sonta, shi ya sa nake son kashe ta. Kuma Masarautar Judala ai masarautarmu ce, mahaifata ce..."

"Me kake faÉ—a ne Ridwan? Wa yake faÉ—a maka waÉ—annan maganganun?"
Baiwa Sakina da ta gama firgicewa ta katse Ridwan, Ridwan ya washe baki cikin rashin damuwa ya ce.
"Wallahi Inna wata tsohuwa ce take faɗa mini, kuma duk dare ma a can nake kwana. Ta ce za ta sanar da ni maɓoyar Kundi ukun da sarakuna uku suke son mallaka, amma wai ai sai na ƙara girma."
Kusan mutuwar zaune Baiwa Sakina ta yi, tana son sake tambayarsa amma tsoro ya mamaye ta.

"Kuma a can na ga an haifi Batul! Ni kuma ba na sonta shi ya sa nake son kashe ta."
Ridwan ya sake faÉ—a cikin damuwa, Sakina ta kamo hannunsa ta ce.
"Kana son ka daina ganina Ridwan? Ko kana son na dinga yi kuka?"

Da sauri ya girgiza mata kai, Sakina ta cigaba da cewa.
"To ka daina faÉ—ar irin maganganun nan, idan ba haka ba waÉ—annan maganganun za su kai mu har gaban Mai martaba. Kuma zai iya zartar mana da hukuncin kisa."

"Shi ma Sarki Gambon ba na sonsa, ta ce mini na kashe s..."

A wannan karon da sauri Sakina ta sake toshe masa baki gabanta yana faÉ—uwa.
'Na shiga uku ni Sakina, me Ridwan yake neman janyo mana?'
Ta raya a ranta tana zubar da ƙwallah.
"Inna kin ga can fa."
Ridwan ya furta cikin murmushi yana nuna mata kusurwar bangon É—akin.

SARKI GAMBO

Sarki Gambo yana zaune aka kai masa tagwayen jariransa duka mata, waɗanda ya yi wa laƙabin Hasana da Usaina. Kowaccensu ta saka hannu a baki tana tsotsa. Jiki a sanyaye dogaransa suka sunkuyar da kansu ƙasa, Sarki Gambo ya fara zubar da hawayen tausayin halin da jariransa suke ciki. Ya jima a haka, sannan aka iso aka sanar da shi an gama haɗa gawar Fulani Khadija za a sallace ta. Da ƙyar Sarki Gambo ya iya miƙa wa Shamaki su, ya bayar da umarnin a kai su ɓangaren Fulani Sadiya domin ta kula da su. Sannan ya ce a tabbatar da an tatsi nonon awaki an ba su don gudun kada yunwa ta illata su.
Cikin ƙanƙanin lokaci mutane da dama suka sallaci gawar Fulani Khadija, don mahaifinta ne ya jagoranci sallar gawarta. Bayan da aka kai ta gidanta na gaskiya, mahaifiyar Fulani ta nemi da a bata jariran domin ta kula da su. Amma fir Sarki Gambo ya ƙi amincewa, saboda tsananin soyayyarsu da yake ji a cikin zuciyarsa. Kusan wuni guda Sarki Gambo ya yi yana karɓar gaisuwar Fulani Khadija, sai yamma liƙis ya shiga turakarsa. Da shigarsa babu jimawa, Jakadiya ta zo nema wa Fulani Zainaba iso wurinsa. Ya yi matuƙar mamaki, don haka kai tsaye ya amsa wa baƙuntarta.

Sallama ɗauke a bakinta ta shiga, sai dai kamar kullum fuskarta a cunkushe take babu ɗigon fara'a. Sai da ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi sannan ta ji ya ce.
"Mun yi matuƙar mamakin ganinku Fulani Zainaba, yau kusan shekara goma kenan da shigowarku rayuwarmu. Sai dai ba ku taɓa neman izinin ganinmu a turaka ba, idan ba mu muka nemi ƙeɓewa da ku ba."

"Saboda babu buƙatar hakan a tattare da ni, a yanzu ma akwai dalilin da ya kawo ni turakarka."
Fulani Zainaba ta furta cikin tsana, Sarki Gambo ya saki murmushi ya ce.
"Zainaba ba za ki taɓa sauyawa ba."

"Zan sauya Sarki Gambo, amma lokaci alƙali ne yana nan tafe."
Ta ba shi amsa kai tsaye, sai kuwa ya ƙura mata ido. Ita ma ba ta janye idonta ba, ta cigaban da kallonsa har sai da ya matso gabanta ya ce.
"Dalilainmu masu muhimmanci ne suka sa muka bar ku a raye Zainaba, tun da kun san ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba."
Fulani Zainaba ta saki murmushin takaici ta ce, "Ni kuma Ubangiji Ya ja da kwana ne, domin na fahimtar da kai kuskuren da ka tafka a baya."
A fusace Sarki Gambo ya É—ago, Fulani Zainaba ta girgiza kai cike da takaici ta ce.
"Na zo na ji ya aka yi Fulani Khadija ta mutu? Don ina zargin wani abu a mutuwar baiwar Allahr nan. Sanar da ni, ya aka yi aka haihu a ragaya? Domin a sanin mugun halin da na yi maka tun daga shigowata gidan nan, na tabbata babu abin da ba za ka iya aiwatarwa ba."
Da sauri Sarki Gambo ya dube ta, cikin zafin rai ya ƙarasa ya maƙure wuyanta.

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
07062062624

[24/11, 17:29] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.

SHAFI NA BAKWAI

ADVERT

*MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR*
'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🏻 Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki.
zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp.
Location: Kano
Sai kun zo💃🏻

Masarautar Judala
Chapter 9 · 0% Book details