Sashe 11
Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun bayan fitar Galadima abin duniya ya haɗu ya haɗe masa, dafe kansa ya yi cike da damuwa. Ganin ba shi da mafita ya sa ya miƙe ya haye kan gadonsa ya kwanta yana tunanin makomar rayuwarsa, da yadda duniya take neman yi masa atishawar tsaki ba tare da ya shirya ba. Abu ɗaya ya sani yana da gawurtattun maƙiya guda biyu, Sarki Dikko da Sarki Gambo. Wanda zuciyarsa ta fi karkata da kaso casa'in da tara a kan su suke yunƙurin dakushe tarihin zuri'arsa daga masarautar Judala. Kusan duka wunin da ya yi haka ya ƙarasa shi sukuku, jiki babu ƙwari. Sai zuwa washegari ya ɗan saki jikinsa, ganin Fulani Zannira ta shiga matsananciyar damuwa.
Da daddare bayan sallar Isha'i, Fulani Zannira da Sarki Giɗaɗo suna zaune suna hira a turakarsa. Shamaki ya doka sallama a bakin ƙofar, yana nema wa Galadima izinin shiga. A ɗabi'ar Sarki Giɗaɗo matuƙar aka yi sallar Isha'i ya rufe ganin kowanne irin baƙo. Amma ga mamakin Fulani Zannira sai ta ga jikinsa yana rawa ya amsa wa Shamaki, sannan ya dube ta ya ce.
"Fulani kuna iya shiga daga ciki, domin akwai muhimmiyar tattaunawar da za mu yi da Galadima."
Duk da ta yi mamaki, da yake Zannira mace ce mai kawar da kai, amma sai ta saki murmushi ta ce.
"Ni mai bin umarninka ce ranka shi daÉ—e."
Martanin murmushi ya mayar mata, ya taka mata har bakin ƙofa cike da ɗokantuwar ganin Galadima. A rumfar (Falo) da Sarki Giɗaɗo yake ganawa da baƙi suka zauna shi da Galadima. Cikin girmamawa Galadima ya ce.
"Allah Ya taimake ka, Ubangiji ya ba ka yawan rai ina fatan na same ka lafiya ranka shi daÉ—e."
Sarki GiÉ—aÉ—o ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Kun same mu kafiya Galadima, tun da muka ji labarin neman isonku muka tabbatar akwai alkairi a tattare da zuwanku."
Galadima ya russunar da kai ya ce, "Wannan haka yake ranka shi daɗe, akwai wata ƙasaitacciyar bokanya da muka samu nasarar gano ta. Sai dai ta kasance ƙungurmar kafira, mai bin addinin kiristanci. Sunan da ake kiranta Bokanya Kande, ta kasance hatsabibiya kuma makira. Babban abin farincikin kuma har kawo yanzu, ba kowanne basarake ne ya san da zamanta ba."
Nan take Sarki Giɗaɗo ya faɗaɗa fara'arsa, cikin zaƙuwa ya ce.
"Galadima a tafi kai tsaye."
Galadima ya saki murmushi ya ce, "Allah Ya taimake ka na samu izinin ganawa da hadimanta, sai dai sun sanar da ni babban sharaɗinta ba ta taɓa ganin mutum ido da ido har sai ya yi imani da Allahn da take bautawa, sannan kuma ya amince Allahnta shi ne mai gaskiya, kuma mai zartar da kowanne hukunci. A taƙaice dai, kusan ridda take sa mutum ya yi."
Shiru Sarki GiÉ—aÉ—o ya yi, yana cikin nazari Galadima ya ce.
"Amma fa an tabbatar mini da aikinta tamkar yankan wuƙa haka take yin sa. Kuma tana aiki da mabambamtan jinsin aljanu kala-kala, a taƙaice dai buƙatarka za ta biya ranka shi daɗe."
A fili Sarki GiÉ—aÉ—o ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Mun amince Galadima."
Galadima ya jinjina kai ya ce, "Amma kuma yana da kyau mu yi fitar sirri ranka shi daÉ—e."
"Yanzu haka a shirye muke Galadima, idan babu damuwa za mu iya tafiya. Sai dai ba ma son masarauta ta fahimci ba mu kwana a gida ba."
A fili Galadima ya saki murmushi mai sauti ya ce.
"Ranka shi daÉ—e, Bokanya Kande sha'aninta fa ya shallake duk tunanin mai tunani. Saboda a ziyarar da na kai, hadimanta sun ba ni wuridin da zan furta a zuciya wanda za mu buÉ—e ido mu gan mu a tsibirinta."
DaÉ—i sosai Sarki GiÉ—aÉ—o ya ji, nan take ya shiga Turakarsa ya sauya kayan jikinsa. Yana fitowa ba su É—auki lokaci ba, Galadima ya dafa tsakiyar kan Sarki GiÉ—aÉ—o. Ya saka shi suka rufe ido, sannan ya fara biya wuridin tsafin da zai kai su tsibirin da take rayuwa.
Wata irin sassanyar murya suka ji tana raira waƙar mai matuƙar daɗi, hakan ne ya alamtawa Galadima sun ƙarasa tsibirin Bokanya Kande. Suna buɗe ido suka ga ƙaton cross a gabansu, Galadima ya dubi Sarki Giɗaɗo ya ce.
"Ranka shi daÉ—e, ni iya hurumin da aka lamunce mini kenan. Kai ne za ka
runtse idonka, idan ka dafa wancan gicciyen (Cross) za a biya maka kalmaman imani da Allahn Bokanya Kande.
Kamar Sarki GiÉ—aÉ—o yana jira, cikin sauri ya matsa gaban cross É—in ya dafa shi haÉ—e da runtse ido. Murya da suka ji a farko, ita ta sake karaÉ—e kunnensa tana biya masa kamar haka.
"Ya Ubangiji Yesu, na yarda cewa kai .... Na furta cewa ni mai zunubi ne, kuma yanzu haka ga ni a gabanka ina neman gafararka. Na karɓe ka a matsayin Ubangijina, mai ceton rayuwata. Na buɗe maka zuciyata ka shiga ciki ka ceci rayuwata. Na gode maka da ka ceci rayuwata daga ɓata, Amin."
Muryar tana gama biya wa Sarki Giɗaɗo, ya ga ya sake tsintar kansa a wani babban kogon dutse. Ilahirin cikin dutse cike yake da cross manya da ƙanana, wata gajeriyar farar mace ya gani. Daga ita sai ganye a ƙirji da ƙasanta. Sarki Giɗaɗo yana shirin yin magana ya ji ta katse shi da cewar.
"Barka da shigowa sabon addini sabuwar rayuwa.
Jikinsa yana rawa ya amsa mata. "Barka dai Bokanya Kande." Yana shirin yin bayanin abin da yake tafe da shi ya ji ta ce.
"Duk matsalolinka na gama saninsu. Matanka suna mutuwa duk bayan kwana arba'in da aurensu, a yanzu haka kuma iyalinka tana É—auke da juna biyu, kai kuma ba ka son ka rasa ta." GyaÉ—a kai Sarki GiÉ—aÉ—o ya yi ta cigaba da cewa.
"Mafitarka É—aya ce ka nemo mini tsohuwar matarka Karima, ko kuma ka kawo mini jininta wato 'yarta."
A firgice Sarki GiÉ—aÉ—o ya É—ago ya ce.
"Ya shugabata Fulani Karima ta shafe lokaci mai tsayi da mutuwa. Babu yadda za a yi na iya kawo miki ita, kuma a iya sanina da ita ni ne mijin da ta taɓa aure. Kuma a ɗakina ta mutu, aka binne ta a masarautata."
"Ba ta mutu ba!"
Bokanya Kande ta furta tana zuba masa manyan idanunta farare tas da sha kwalli ya ƙara musu kyau, ji ya yi ba zai iya cigaba da kallon ƙwayar idonta ba. Ta saki murmushi sannan ta cigaba da cewa.
"Har yanzu Karima tana doran ƙasa, domin binciken da na yi tauraron rayuwarta yana nan har yanzu. Amma ban gama tabbatar da shin ainihin ruhinta ne, ko kuma akwai wani ƙulumboto da aka aikata ba. Kuma ta haifi jininta a cikin masarautarka, domin tauraron jaririyar daga tsagin tauraron Karima yake, sai dai har kawo yanzu bincikena bai bayyana mini ainahin fuskar jaririyar ba. Sai dai yana kyau, ka binciki masarautarka. Duk sababbin jariran da aka haifa a ciki, ka shafa musu wannan jan garin maganin da zan damƙa maka. Idan har ka ga jini daga al'aurarsa, wala mace ko namiji ko kuma sauran alamomin da zan raɗa maka a kunne, to tabbas jinin Fulani Karima ne."
*Ummou Aslam Bint Adam*
07062062624
[25/11, 21:38] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA TAKWAS
*MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR*
'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🻠Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki.
zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp.
Location: Kano
Sai kun zo💃ðŸ»
Masarautar Kajjura
Yadda Sarki Gambo ya maƙure wuyan Fulani Zainaba, abin ba ƙaramin tsoro ya ba ta ba. Don har sai da numfashinta ya nemi ɗaukewa, idanunta suka firfito ta fara fita hayyacinta. Wurgi ya yi da ita ta faɗi ƙasa, nan take tari ya turnuƙe ta. Zuwa ya yi ya tsiyayo mata ruwa a tulunsa, ya ƙarasa gabanta ya miƙa mata. A galabaice ta karɓa ta kai bakinta, sai da ta sha mai isarta sannan ta ɗago tana sauke ajiyar zuciya. Kafe ta ya yi da ido yana kallo, ita ma ta zuba masa idanu tana sake jadadda ƙarfin rashin imaninsa.
Sarki Gambo ya ɗago haɓarta, yana bin ta da wani rin kallo mai wuyar fassarawa.
"Zainaba ba yanzu zan kashe ki ba."
Ya furta a kausashe, kamar ta yi masa shiru. Sai kuma zuciya ta É—ebe ta, tana ayyana mata idan har ta yi shiru zai ga kamar ta fara jin tsoronsa ne. Cikin dakiya da taurin zuciya ta ce.
"Rashin kisana da ka yi, yana da nasaba da ganin gawarka da zan yi Sarki Gambo."
Ya ji É—acin maganarta, don haka ya furzar da isa mai zafi ya ce.
"Lokaci kawai nake jira, amma mu koma maganarmu ta baya. Me ya sa kike son É—ora alhakin kisan Fulani Khadija a kaina, duk da kina da masaniyar a wurin haihuwa mummunan al'amarin ya faru da ita?"
"Saboda na san babu abin da ba za ka iya aikatawa ba saboda buƙatar kanka."
Fulani Zainaba ta ba shi amsa kai tsaye. Miƙewa ya yi ya fara zagaye ɗakin yana girgiza kai, sai da ya yi zagayen kamar sau uku sannan ya koma kan kujerarsa ya zauna suna cigaba da kallon juna ya ce.
"Tabbas ba ki yi ƙarya ba Zainaba, zan iya aikata komai kuma a kan kowa matuƙar buƙatata za ta biya. Domin dalilin haka ne ya sa na hallaka mijinki Najibullah da jaririn ɗanki."