← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 24

Sashe 18

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Oh ni jikar mutum huÉ—u, sannu Zuwaira kin ji."
Wata 'yar uwar matar ta furta, Zuwaira da ta É—ago a galabaice ta ce.
"Ku kawo mini jaririyar nan, don Allah ku ba ni ita. Wallahi ita É—in ta dabance, don Allah kada ku nisanta ni da ita."
Da mamaki suka dinga bin ta da kallo, Indo da Batul ke hannunta ta sake ƙanƙame ta.

"Ke yanzu ba ki dubi halin da kika shiga ba, amma kike ƙoƙarin gayyato wa kanki mutuwa? An ya kina cikin hankalinki kuwa Zuwaira? Ko da ma can haka kike shayarwa?"
Wata mata ta yi caraf ya karɓe zancan, Zuwaira ta dube su sai ta saki murmushi ta ce.
"Da kun san wace ce ita..." Sai kuma ta yi shiru, ta gyaÉ—a kai ta ce.

"Eh haka nake goyo na, wani lokacin idan ina shayarwa yana jini, idan hakan ta kasance har suma nake yi. Na taɓa tambayar wani mai magani, ya ce mini cuta ce. Ina gab da komawa karɓar magani aka kamo mu."

Lokaci É—aya jikin mutanen wurin ya yi sanyi, tausayin Zuwaira ya mamaye su. Sai suka É—auke mummunan zargin da ke zuciyoyinsu a kam Batul, jin Batul ta fara motsi ya sa Zuwaira ta dubi Indo ta ce.
"Miƙo mini ita yarinya na shayar da ita."
Girgiza kai Indo ta yi, don haka kawai ta ji ba ta gamsu da amsar da Zuwaira ta bayar ba. Cikin muryar kuka ta ce.
"A'a ina tsoron kada wani abu ya sake samunki."
Suna cikin haka, wata mace ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Amma can kamar garken awaki ne, me zai hana mu tatso mata nonon akuya ta sha."
Kallon kallo aka shiga yi wa juna saboda tsoron kashedin uwar bayi, ganin haka ya sa Indo ta nufi wurin Dogarawan da ke can nesa da su. Tun ba ta buÉ—i baki ba, wani Dogari ya buga mata tsawa da cewa.

"Ke wanne irin kunnen tsiya gare ki, ba cewa aka yi ki zauna a cikin 'yan'uwanki ba?"
Baki yana rawa Indo ta ce, "Don girma Allah ku lamunce mini na tatsi nonon akuya zan shayar da jaririyat..."
Tun ba ta rufe baki ba, Dogarin ya zuba mata dorina a bayanta. Azaba da gigicewa suka sa ta yi baya ta faɗi, don kaɗan ya rage jaririya Batul ba ta bugu da ƙasa ba. Da ƙarfinsa ya ƙarasa gabanta ya sake ɗaga hannu ya zuba wa Indo dorinar dukan dokin, ta yi saurin sunkuya don kada ya samu Batul da buguwar da suka yi, ta sa ta yin shiru kamar ta san abin da yake faruwa.

"Au tare mata za ki yi? Shi ne kika zagayo ta bayana? Ai kuwa wallahi za ki gane ba ki da wayo."

Indo da sauran Dogaran suka ji ya faÉ—a yana waigen bayansa, ko kaÉ—an babu wanda ya ga kowa. Don haka É—aya daga cikinsu ya ce, "Kai Mamman, wai lafiyarka kake magana kai kaÉ—ai?"

Tun bai gama maganar ba, suka ga Dogari Mamman ya fara kai duka yana nausar iska. Tun suna ganin abin kamar wasa, sai suka rufa masa baya suna kiran sunansa. Daga haka suka ji ya saki wata gigitacciyar ƙara ya faɗi ƙasa yana shure-shure.

Ganin hankalinsu ya tafi kan wurin da Mamman yake, ya sa Indo ta yi saurin rarrafawa cikin garken awakin. A cinyarta ta zaunar da Batul, da saka hannu ɗaya tana tatsar nonon wata ƙatuwar akuya tana tara da ɗayan hannunta. A hankali take ɗisa mata a baki, nan da nan Batul ta shiga tsotsa tana ba ta har ta lura da ta ƙoshi, tana gama shayar da ita babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.

Ajiyar zuciya Indo ta yi, ta zuba wa fuskar Batul ido, ta É—aga hannu cikin muryar karaya da kai kuka wurin Ubangiji ta ce.
"Ya Allah ka ga kyakkyawar niyyata, Allah ka taya ni rainon wannan baiwa taka. Idan ma ba mutum ba ce kamar yadda zuciya take raya mini, Allah kada ba wa ahalinta ikon cutar da ni." A hankali ta shafa a fuska, sannan ta miƙe ta fito daga cikin garken awakin. Ta ƙarasa wurin ragowar bayin ta zauna, sai dai kallon da Zinaru take yi mata ya sake sanyaya mata jikinta. Haka suka ci gaba da zaman jigum-jigum har aka fara kiran sallar asuba, kuma a daidai wannan gaɓar labarin kisan wulaƙancin da aka yi wa gawar Dogari Mamman ta riske su. Indo ba ƙaramin kaɗuwa ta yi da jin irin kisan da aka yi masa ba, tana cikin wannan jimamin Uwar Bayi ta ƙarasa ta ingiza ƙeyarta da jaririya Batul ba tare da ta san dalili ba.

_MTN AND AIRTEL DATA AVAILABLE...!!🔥_

Monthly data — valid for 30 days

_📶MTN DATA_
• 500MB — 450
• 1GB — 700
• 1.5GB — 1000
• 2GB — 1,300
• 3GB — 1,900
• 5GB — 2,100

_📶AIRTEL DATA_
• 1GB — 750
• 2GB — 1,400
• 3GB — 2,150
• 3.5GB — 1,800
• 5GB — 2,850
• 6GB — 2,900
• 10GB — 5,600

𝙋𝙖𝙮𝙢𝙚𝙣𝙩 :
Opay — 7049439332
AFNAN ADAM

𝙒𝙝𝙖𝙩𝙨𝘼𝙥𝙥 𝙉𝙤: 09040772027

_Thank you❤_

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[30/11, 20:57] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.

SHAFI NA SHA BIYU

Tamkar raƙuma da akala haka Indo ta cigaba da bin Uwar bayi, sai da suka wuce soro uku ganin tafiyar ta fara nisa ya sa Indo ta ce.
"Don Allah ina za mu je?"
A yatsine Uwar bayi ta waigo ta dube ta, sheƙeƙe ta ce.
"Idan mun je za ki gani."
Haɗiye yawu Indo ta yi cike da damuwa, ta sauke ajiyar zuciya tana kalle-kallen yanayin tsarin gidan sarauta, da zane-zanen da aka ƙawata na fari da ja ba ƙaramin birge ta ya yi ba.
Wurin wani babban fili suka ɓulla, daga nesa ta hangi dandazon maza a tsaitsaye waɗanda take tsammanin Dogarai ne. A ɗan tsorace Indo ta ƙarasa saboda yadda ƙirjinta yake dakan lugude.
"Sarkin tsaro shin wannan ce yarinyar da kuke magana a kai?"

Ƙuri suka yi wa Indo suna nazari, saboda lokacin da ta same su da dare hasken farin wata ne.
"Ƙwarai ita ce, ke zo nan!"
Nan take Indo ta sake rungume Batul, ta fara takawa a tsorace. A tsammaninta saukar duka za ta ji a jikinta, amma ga mamakinta sai ta ji ya sunkuyo daidai fuskarta ya yi ƙasa da murya ya ce.
"Yarinya ki faÉ—a mana tsakaninki da Allah, me kika yi wa É—an'uwanmu har muka tsinci gawarsa a tsakiyar dajin da muka bi shi."
Ajiyar zuciya Indo ta sake saukewa ta ce.
"Wallahi-tallahi ban yi masa komai ba, tsakanina da Allah nake wannan maganar."
Indo ta ƙarasa maganar tana goge hawayenta, shiru suka yi suna nazari sai ɗaya daga ciki ya ce.
"Ka san fa dama hanyar É—orawar can ba ta da kyau, ko dai wani abin ya takawa mazauna wurin suka huce fushinsu a kansa?"
Cike da É—aurewar kai Dogarin ya É—ago yana dafe kai cikin jimami ya ce, "Na shiga ruÉ—ani wallahi, to amma fa tun kafin ya shiga dajin ya fara surutai kamar mai magana da iskokai."
Duka shiru suka yi cikin jimami, Uwar bayi ta ja bawan da ya gama magana suka É—an yi gaba. Sai da ta tabbatar da ta yi nesa da su ta ce.
"Bala an ya ba za ku bar wannan maganar ba, don idan Mai martaba ya ji wannan zancan ina ganin kamar da matsala."
Cikin sauri Dogari Bala ya riƙe baki ya ce, "Uwar bayi me ya kai mu aikata wannan ɗanyen aikin? Ni fa gabaɗaya tsoron yarinyar nake yi, don wallahi ganin idona Mamman yana gama dukanta ya fara wannan haukar, ai kawai ki ja ta ku koma ciki."
Jinjina kai Uwar bayi ta yi ta ce, "To shi kenan, mu kuma da muke tare da ita Allah Ya kiyaye mu." Kusan lokaci É—aya suka saki dariya.
Indo tana zaune cikin zullumi Uwar bayi ta riƙo hannunta tana washe baki kamar ba ita ba ta ce, "Yarinya mu je kin ji, wai ya sunanki ne?" Da yake har lokacin Indo a tsorace take, jiki a sanyaye ta ce.
"Sunana Indo."
Cikin bugar ciki Uwar bayi ta ce, "Indo tsohuwa, wai kuwa tare da mijinki aka kawo ki gidan nan?"
Ras! Gaban Indo ya faÉ—i, cikin in'ina ta ce.
"Na'am... ai... a'a... ba tare muke ba, mijina ya mutu tun kwanaki."
Ƙuri Uwar bayi ta yi mata tana son gano wani abu daga kalaman Indo, sai ta ɗan kalle ta daga sama zuwa ƙasa ta ce.
"Amma kuma na ga garau kike tafiyarki jiya-jiya da haihuwa, kodayake ai kowacce mace da yanayin jikinta." Ita dai Indo shiru ta yi, a haka har suka ƙarasa sashensu na bayi. Indo tana shiga ta ga mutane suna bin ta da kallo, duk sai ta ƙara tsarguwa. Hakan ya sa ta raɓe can a gefe, zamanta babu jimawa Batul ta fara kukan yunwa. Da sauri Zuwaira ta matso kusa da ita ta ce, "Kawo ta na bata..."

"A'a zan nemo mata nonon akuya, saboda na ga jiya ta ji daÉ—insa sosai."
Indo ta katse ta, tana miƙewa tsaye. Murmushi Zuwaira ta yi, Zinaru da ke gefe ta saki guntun tsaki ta ce.

"Ke dai wahala ta gan ki wallahi Indo, amma a juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe."
Duka mutanen ɗakin kallon Zinaru suka yi, jikin Indo a sanyaye ta fita. Sai dai Indo tana fita ƙananan maganganu suka fara tashi, wasu suka shiga kare Indo yayin da wasu suka fara tsegumi a kan ƙanƙantar Indo a matsayinta na mahaifiyar Batul.
Chapter 18 · 0% Book details