Sashe 2
Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Malami ya miƙa masa wani garin baƙin magani, sannan ya cigaba da cewa.
"Ka yi shelar dakatar da bayin da za a shigo da su, sannan ka saka garwashi ka turara É—akin da za ka killace su. Wannan aikinka ne ba na bayi ba, abu biyu zuwa uku ne zai faru a wannan lokacin."
Sarki Gambo ya damƙe maganin kamar wani zai ƙwace masa, ya shiga gyaɗa kai kamar na ƙosasshan ƙadangare.
"Na farko idan har jinin Najibullah yana wurin take zai fara haɓo ya bayyana kansa, daidai wurin da suke tsaye ƙasar wurin za ta yi ja kamar wuta. Har da za ka saka hannu za ta iya babbake ka, sai dai kuma na bincika Najibullah ne kaɗai ragowar jinin zuri'arsa a doron ƙasa, amma kuma zuciyata tana yi mini wasu-wasi. Yana tafe da iyalinsa mai ɗauke da tsohon ciki, ka tabbatar da ka kashe shi. Ka killace matarsa har zuwa lokacin da za ta haihu, shi ma ɗa ko 'yar da za a haifa ka kashe su..."
"Dole sai mun jira ta haihu? Me zai hana mu hallaka su lokaci É—aya?"
Sarki Gambo ya furta a harzuƙe, Malami ya girgiza kai ya ce.
"Matarsa za ta yi mana amfani, ko ba ka san jininsa da ya gauraya da nata zai zame maka takin da kowanne manomi yake burin samu ba? Idan har ka kashe É—an da ta haifa ka kawo mini ita nan, ragowar bayanin zan yi maka daga baya."
Godiya Sarki Gambo ya yi masa, Malami ya cigaba da karanta masa bayanin duk abin da ya dace ya yi. Sai gabannin asuba, sannan ya yi masa sallama ya koma turakarsa.
A yadda ya bar Fulani Sadiya a haka ya koma tana zaune jigum, har ya koma ya same ta ba ta koma bacci ba. Dafe kai ta ga ya yi, cike da kulawa ta dafa jikinsa ta ce.
"Tun bayan fitarka zuciyata ke É—amfare da tarin damuwa da tashin hankali."
Sai da ya janyo ta jikinsa, sannan ya sumbaci goshinta ya ce.
"Tarin alkairai ne suke ƙwanƙwaso mana ƙofa Fulani, dangane da tsofaffin kundun da na taɓa baki labari. Sai komai ya tabbata zan sanar da ke yadda aka haihu a ragaya."
Dam! Ƙirjinta ya buga, amma sai ta kawar da damuwar fuskarta.
'Na yi alƙawarin bankaɗa maka labulen kowanne irin sirrin Sarki Gambo, kada wani abu ya dame ka. Na tabbata yana yi mini kallon kitse, ina yi masa na rogo ne.'
Fulani Sadiya ta tuna kalaman da ta furta wa Sarki Giɗaɗo, a lokacin da suka yi wata ɓoyayyar tattaunawar sirri. Amma a fili sai ta saki murmushi ta ce.
"Ina tare da kai Sadaukina, haƙiƙa kai ɗin mai sa'a ne."
Sarki Gambo ya saki murmushi, jin ana ƙoƙarin shiga sallar Asuba ya sa shi fita ya ɗaura alwala ya nufi masallaci.
Asubar fari Sarki Gambo ya sanar wa da Shamaki, da a kulle duk ƙofofi huɗun da ke cikin masarautar. Sannan ya ce a tsaurara tsaro a ƙofar Yamma, domin ta nan ne ya bada umarnin idan Dogaran da suka tafi farautar bayi sun dawo za su shiga.
Har sai da rana ta fara fitowa sannan labari iso wa Mai martaba, kan dawowar babban dogari Sale. Don haka zuciyarsa fal farinciki, ya shirya cikin baƙar alkyabba mai rashin jajayen duwatsu. Daga saman kansa akwai wata hular azurfa, ya ɗaga kansa yana kallon zabgegiyar takobin da ya yi mafarkin an datse kansa da ita.
"Da ita zan datse kanka Najibullah."
Ya furta cikin izza, isa da ƙasaita. Sannan ya ɗauko ta ya saƙala a wuyansa, kai tsaye fadawa suka ba shi hanya. Nan take aka fara busa sarewa da algaita, fadawa suka shiga zabga masa kirari. Yayin da maroƙa suka fara bambaɗanci suna wasa shi tamkar babu gobe. Duk da bai furta musu koda kalma ɗaya ba, amma irin murmushin da yake yi ya sa suka fahimci yana cikin tsananin farinciki. Sai dai kuma a ɓangare ɗaya, suna mamakin wannan umarni da Sarki ya bayar. Domin ba ya daga cikin hali ko ɗabi'arsa, duba bayi a duk lokacin da aka kawo su masarauta.
Tun da aka killace su ƙirjin Najibullah yake dukan uku-uku, gumi ya shiga karyo masa. Ganin yanayin da yake ciki ya sa tsoho Sulaimanu ya girgiza masa kai, duk da hannu da ƙafafuwansu a ɗaure suke hakan bai hana ya yi masa inkiya da ya lulluɓa wa kansa mayafin jarumta ba.
"Tsoho Sulaimanu, haƙiƙa zuciyata ta gama tsinkewa. Tun da nake numfashi a doron ƙasa, ban taɓa jin yanayin da yake kassara ƙwarin gwiwar gangar jikina ba sai yau."
Tsoho Sulaimanu ya yi ƙasa da murya ya ce.
"Ƙwarin gwiwarka ita za ta assasa tawa ƙwarin gwiwa Najibullah. In Shaa Allahu sai mun cimma nasara, domin Ubangiji ba ya zalinci."
"Kai kaɗai ka rage daga cikin zuri'armu Najibullah, kuma a kanka nake saka ran za ka dawo da ƙima da martabar gidanmu. Haƙiƙa a baya an riga da an ci mu da yaƙi, amma ina son na nuna wa zuri'ar jininmu ba za ta ƙare a banza ba. Don haka nake umartarka da ka yi aure a cikin kwanaki ƙalilan, domin ta haka ne za mu cigaba da yaɗuwa a doron ƙasa."
Najibullah ya tuna kalaman mahaifinsa na baya, a lokacin da yake yi masa wasiyyar bankwana. Hawaye masu ɗumi suka zubo masa, sakamakon ido biyu da ya yi da matarsa Zainaba mai ɗauke da tsohon ciki. Yana shirin yin magana, ƙaurin turaren da ke hannun Sarki Gambo ya daki hancinsa. Lokaci ɗaya ya ji kansa ya sara, daga gefen hagunsa ya ji an ce.
"Ka gafarce ni Najibullah, a wannan karon na gagara ba ka kariyar da ta dace." Juyawa dattijuwar matar ya ga ta yi, sai ta ratsa ta jikin bango ta fita tana zubar da hawaye. Lokaci ɗaya ya ji abu mai ɗumi yana fita daga hancinsa, yana sauke idonsa ya ga jini yana zuba. Ɗago idon da zai yi suka haɗa ido da sarki Gambo, da yake jifansa da murmushin ƙeta mai cike da zallar rashin imani.
*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
07062062624
[23/11, 21:33] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA BIYU
https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t
ðŸ›ï¸Assalamu Alaikum – Hafsat Collection ce!
Kinason kayan masu inganci masu kyau kuma cikin sauƙin farashi? To ba ki da matsala! 🥳💃
📌 HAFSAT COLLECTION ta kawo muku: ✨ Kayan gyaran gida
✨ Kayan ado da kyalliya
✨ Kayan mata da maza masu kwalisa
✨ Kayan kitchen masu kyau da karko
🔥 Duk a cikin farashi mai sauƙi!
📦 Muna a Kano, amma muna aikawa zuwa ko ina cikin amincin Ubangiji! ðŸ™
Maza ki shiga group É—inmu yanzu:
👉
📌 Kasance da Hafsat Collection – Sayan daidai, ko sari!

Kamar yadda ƙirjin Najibullah yake dakan lugude, haka tsoho Sulaimanu ya shiga matsanancin tashin hankali. Najibullah ya runtse idonsa cikin sarewa, da wata irin raunanniyar murya ya fara yi wa tsoho Sulaimanu magana mai kamar wasiyya.
"Haƙiƙa ajalina ya gabato tsoho Sulaimanu, don haka zan damƙa ragamar duka wannan yaƙin a hannunka, duk da a yanzu shekaru sun cimma maka. Don Allah ka kula da Zainaba idan har ka samu damar haka, ina mai bar maka wasiyya a kan muradin mahaifina."
Zafafan hawaye suka shiga sintiri a saman dakalin fuskar tsoho Sulaimanu, cikin murya tsufa da kuka ya sunne kai ƙasa a hankali. Ta yadda ba za a ankara da abin da yake faɗa ba ya ce.
"Allah Shi ne masanin daidai Najibullah, amma duk alƙawuran da ka damƙa mini zan rungume su hannu bibbiyu, domin ko babu komai idan Allah Ya ja kwanana zan tabbatar da gaskiya tana iya danne ƙarya."
Duk tattaunawar da suke yi Sarki Gambo yana kula da su, ya saki murmushin gefen baki. Sannan ya fara takawa cikin isa da ƙasaita, kafin ya ƙarasa gaban Najibullah ƙasar da yake tsaye iya daidai saitin ƙafafuwansa ta yi jajir, kamar ƙarfen maƙerar da ya shekara a wuta.
Daga dogarawa, fadawa zuwa bayin da ke ɗaure maza da mata. Gabaɗaya kallo ne ya koma wurin Sarki Gambo da ke tsaye a gaban Najibullah. Babban ɗakin tsit ya yi kamar babu masu numfashi, a karo na biyu Sarki Gambo ya saki murmushin gefen baki. Cikin wulaƙantacciyar murya ya ce.
"Najibullah!"
A razane tsoho Sulaimanu da Najibullah suka ɗago, zuciyarsu ta shiga tsalle kamar za ta yi tsuntsuwa ta hudo ƙirjinsu
Sannan ya nuna dogari Ɗanjuma, ya ba shi umarnin fitowa da Najibullah, ganin haka ya sa wani abu ya tsarga wa Zainaba. Dogari Ɗanjuma irin ƙarfafan mutanen nan masu siffar samudawa ne, kusan indai Sarki Gambo zai zartar da mummunan hukunci shi yake kira. Da ido ya yi masa nuni, tun bai yi magana ba. Ɗanjuma ya shiga kiciniyar kunce Najibullah, nan take ƙananan maganganu suka fara tashi.
Sarkin Zagi ne ya dubi mutanen ya buga musa tsawa, nan take kowa ya ja bakinsa ya tsuke. Jikin Najibullah ban da karkarwa babu abin da yake yi, Ɗanjuma yana fito da shi ya dankwafar da shi a gaban Mai martaba. Shi ma ya zube ƙasa cikin girmamawa ya ce.
"Ina neman izini wurin adalin Sarki, da ya ba ni dama na datse kan wannan ƙasƙantaccan bawan."
Murmushi Sarki Gambo ya yi, ya saka hannu ya ɗago haɓar Najibullah sai ya dubi Ɗanjuma ya ce.
"Wannan hukuncin namu ne, mu za mu zartar da shi."
A wannan karon ma hatsaniya ce ta ɗan fara tashi, domin kusan a saninsu da Takawa. Wannna ce rana ta farko da zai taɓa zartar da mummunan hukunci da hannunsa a gaban jama'a, dogari Ɗanjuma ya sake russunawa ya ce.
"An gama ranka shi daÉ—e, idan an ba ni izini zan iya komawa mazaunina na tsaya."
Da ido Sarki Gambo ya yi masa magana, nan take Ɗanjuma ya ɗaure hannun Najibullah ta baya. Sannan ya koma inda yake ya tsaya, wurin ya yi tsit kowa da abin da yake saƙawa a zuciyarsa.