Sashe 21
Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_📶AIRTEL DATA_
• 1GB — 750
• 2GB — 1,400
• 3GB — 2,150
• 3.5GB — 1,800
• 5GB — 2,850
• 6GB — 2,900
• 10GB — 5,600
ð™‹ð™–ð™®ð™¢ð™šð™£ð™© :
Opay — 7049439332
AFNAN ADAM
ð™’ð™ð™–ð™©ð™¨ð˜¼ð™¥ð™¥ ð™‰ð™¤: 09040772027
_Thank youâ¤_
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[30/11, 21:36] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA SHA HUÆŠU
Masarautar Judala
Sai da Zuwaira ta gyaÉ—a wa Indo kai, sannan ta cigaba da cewa.
"Tun ranar da Baushe mai magani ya sanar da ni wace ce yarinyar nan, da irin al'amuran da ke tattare da ita. Ya bayyana mini miyagun ƙaddarorin da za su afka wa rayuwarta, don babban abin da ya fi ba ni tsoro yadda na ga ya jiƙe sharkaf da gumi a lokacin da yake yi binciken tauraronta." Zuwaira ta ɗan yi jim sai kuma ta cigaba.
"Na san za ki yi mamaki a lokacin da na shayar da Batul har na yanke jiki na faÉ—i, tun kusan shekarun baya nake fama da wannan lalurar. Kuma Baushe da kansa ya sanar da ni sammu ne aka yi mini wanda ba zan samu warkewa ba har sai na haÉ—u da ita. Kuma na san za ki yi mamaki idan na ce miki ni mayya ce."
Cikin alamun tsoro Indo ta ja da baya, ƙirjinta yana bugawa ta cigaba da kallon Zuwaira. Ganin haka ya sa Zuwaira ta saki murmushi haɗe da gyaɗa mata kai ta ce.
"Ƙwarai kuwa ni 'yar sarkin mayun yankinmu ce, maita gadon gidonmu ce gaba da baya. Kakata da ta haifi mahaifina an ce saboda yadda maita ta huda ɓargon jikinta, ko tsuntsu ne ya zo giftawa ta saman gidanmu sai dai gawarsa ba shi ba. Wani zubin kuwa idan abin ya ciyo ta, ta rasa dabbar da za ta ci. Sai ta je kasuwar mahauta, ta sayi ɗanyen nama ta shige ɗaki ta cinye. Amma kuma duk wannan maitar ta kakata, ba ta taɓa cin ɗan mutum ba har ta ƙare rayuwarta."
Indo a tsorace ta sauke ajiyar zuciya tana gyaÉ—a kai, don wasu kalaman na Zuwaira jin su take ba tare da tana fahimtarta ba. Ita kanta Zuwaira ta lura da haka, ta dafa kafaÉ—arta ta ce.
"Kada kalamaina su tsorata ki Indo, ni ba mai cutarwa ba ce. Kawai ina sanar da ke wani sirri ne, domin tun da na fahimci kina tare da Suryu hankalina ya kwanta da ke. Duk da wani tsagin na zuciyata yana tantamar kasancewarki mahaifiyarta, domin ban ga alamun da Baushe ya ce mahaifiyarta tana da shi a jikinki ba. Ya ce mini mahaifiyarta zuciyar zaki gare ta na rashin tsoro, ke kuma na ga tsoro ƙarara a saman fuskarki. Sai dai kuma na tabbata ko da ba ke ce mahaifiyarta ba, tabbas zuciyarki mai kyau ce Indo." Sai a lokacin hankalin Indo ya ɗan kwanta, Zuwaira ta kawar da ƙwaryar da ta yi wa Batul wanka gefe sannan ta cigaba da faɗin.
"Daga mahaifina har mahaifiyata ƙungurman mayu ne, har sai da ta kai mahaifina ya ci mutum ɗari ba ɗaya wanda silar haka ne ta sa a ka naɗa shi sarkin mayun yankinmu. Duk da dama can mahaifinsa shi yake riƙe da wannan sarautar, amma kasancewar mahaifina yana da tarin 'yan'uwa daga waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya zuwa 'yan uba. Sai suka taso shi a gaba saboda kowa so yake ya gaji sarautar mahaifinsu, sai dai duk miyagun sihirin da suke yi na jifan mahaifina bai yi tasiri a kansa ba. Da suka lura mahaifina yana son damƙa mini ragamar sarautar hannunsa, sai suke shiga jifana da asiri kala-kala. Kuma ni abin da ba su sani ba, ko kaɗan ban taɓa sha'awar riƙe kambun da mahaifina yake kai ba. Don mun sha kai ruwa rana da mahaifina, a kan sai na ci adadin mutanen da ake ci kafin a damƙa maka ragamar sarautar maita. Me zai sa na cutar da 'yan'uwana Indo? Bayan kuma Ubangiji bai hallice mu don mu cutar da kowa ba, kuma me zai hana mu dinga taimakon bayar da magani a madadin cutarwa?"
Indo ta jinjina kai ta ce, "Haka ne kam Inna Zuwaira."
Zuwaira ta ji daÉ—in sunan da Indo ta faÉ—a mata, don ta tabbata a haife kam za ta haifi Indo.
"To don na nuna wa mahaifina haka, sai ƙilu ta ja bau. Mahaifina ya sako ni a gaba, haka dangin mahaifina da suke zargin za a damƙa mini sarauta suka sako ni a gaba. A taƙaice dai har sai da mahaifina ya so bayar da kurwata a bikin bada kurwa da ake yi a yankinmu duk shekara, amma sai mahaifiyata ta tsaya kai da fata don ganin hakan ba ta tabbata ba. In taƙaice miki labari, ban san hawa da sauka ba sai kawai na wayi gari da wasu baƙin cututtuka. Yau da lafiya gobe babu, hatta mijin da na aura mun haɗu ne a wurin neman magani. Da Innata ta kai ni shi kuma ya nuna yana sona, amma duk sanin sirrin maganinsa sai ya gagara gano ainahin abin da yake damuna. A haka na fara haihuwar yara suna mutuwa, abin da ban sani ba ashe dangin mahaifina ne suke kashe mini su suna cinyewa. Wannan ɗan da kika ga na zo da shi masarautar nan, shi kaɗai ne ya rayu a cikin yara goma da na haifa. Shi ma tun cikinsa yana ƙarami na fara zuwa wurin Baushe mai magani, a nan ya dinga ba ni taimakon magunguna har Allah Ya sa na haife shi lafiya. Ranar da na fara shayar da shi, a ranar na ga abin al'ajabi. A madadin ruwan mama ya zuba, sai ya zamana wani baƙin jini ne yake fita. Jaririna ya ƙi karɓa, bayan da na koma wurin Baushe ya ba ni magani sai na samu lafiya. A nan ya sake sanar da ni duk irin cutukan da ke jikina, tare da makarinsu da kuma yadda za a yi na samu lafiya."
BuÉ—e baki Zuwaira ta yi, ta zaro wani abu fari mai tsayi kamar zare. Ita dai Indo tana takure a gefe sai raba idanuwa take yi, kama hannun Batul ta yi za ta saka mata. Da sauri Indo ta janye Batul gabanta yana faÉ—uwa ta ce.
"Don Allah kada ki sa ta zama mayya ita ma, don Allah ki ƙyale ta haka."
Murmushi Zuwaira ta yi, busasshiyar fuskarta da babu tsokar kirki ta sake yamutsewa. Da yake Indo ta gama tsora ta da ita, har gani ta yi fuskar Zuwaira tana neman razana ta. Tana cikin haka ta ji Zuwaira ta ce.
"Ba ƙanƙarar maita ba ce Indo, ina tunanin har yanzu ba ki san wace ce Batul ba. Shi ya sa kike tsammanin zan iya cutar da ita, wannan dalilin ne ya sa na sake tabbatar da ba ke ce mahaifiyarta ba."
Indo ta waiga tana kalle-kalle don kada wani ya ji tattaunawarsu, ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Don girman Allah kada ki furta wannan maganar a cikin mutane, tabbas Batul ba 'yata ba ce. Ba ni na haife ta ba, amma ƙaddara ta haifar mini ita kuma zan riƙe ta hannu bibbiyu."
Nan take Indo ta kwashe duk abin da ya faru tsakaninta da Karima ta sanar da ita, Zuwaira ta jinjina kai ta ce.
"Shi ya sa na ce zuciyarki mai kyau ce Indo, kuma In Shaa Allahu zan cigaba da nuna wa duniya ke É—in mahaifiyarta ce. Kuma na É—auke ki tamkar 'yar cikina, haka kuma Batul kamar jika ta. Sai dai ni ma ina neman alfarma a wurinki."
Idanu Indo ta zuba mata alamar tama sauraronta, Zuwaira ta ce.
"Ki yi mini alƙawarin ba za ki taɓa sanarwa da kowa cewa ni mayya ba ce, haka kuma ba za ka dinga wasu-wasin zan cutar da ku ke da Batul ba. Sannan duk halin da kike ciki, ki mini alƙawarin ba za ki ɓoye mini ba."
GyaÉ—a kai Indo ta yi ta ce, "Zan faÉ—a miki amfanin wannan zaren da zan saka mata, kema kuma idan ba za ki damu ba. Zan saka miki shi a dantsen hannunki, idan kuma ba ki da muradi shi kenan ba zan tilasta miki ba."
Zuwaira tana gama maganar ta naɗa zare ya zama kamar awarwaro, sai ta kamo hannun Batul ta zura mata shi, wani irin haske suka gani a jikin hannun nata. Nan take zaren ya fara kwanciya a fatar hannunta, daga ƙarshe ya shige cikin jikinta gabaɗaya tamkar wani abu bai taɓa wanzuwa ba.
Daga Indo har Zuwaira kallon juna suka yi, bakin Indo yana rawa ta ce.
"Ya... ya... aka yi ne Inna Zuwaira?"
Zuwaira da ta gama tsora ta ta ce, "Wallahi ban san yadda aka haihu a ragaya na, ni a iya sanin da na yi wannan zaren yana zama a jikin hannu ne ba tare da ya ɓace ba. Amma ita nata ki duba ki ga har wata wuta ya yi kafin ya ɗauke." Kamar Indo za ta yi kuka ta miƙe tana jijjiga Batul da ta fara mutsu-mutsu za ta yi kuka. Suna cikin haka sai suka ga daidai wurin tsintaiyar hannun nata ya yi ja kamar an saka awarwaro a wuta an ciro an saka mata a wurin, wanda hakan ne ya tabbatar wa Zuwaira shatin zaren da ta saka mata a hannun ne.
Uwar Bayi