← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 24

Sashe 20

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hargitse Baiwa Sakina ta fita daga sashen Fulani Sadiya, duk wanda ya ga irin tafiyar da take yi sai ya fahimci ba ta cikin nutsuwarta. A haka ta ƙarasa sashensu na bayi, tana shiga ɗaki ta hangi Ridwan a zaune yana biya karatunsa na allo. A fili ta sauke ajiyar zuciya har sai da ya waigo ya kalle ta, murmushi ya sakar mata ta ƙarasa kusa da shi ta zauna ta ce.
"Ridwan karatu kake yi?"
Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi, ta zuba masa ido tana kallon yadda tsantsar kyawun yaron yake sake bayyana. Dara-daran idanunsa ta kalla, sai ta ga kamar ƙwayar idonsa ta sauya zuwa irin ta maciji, gabanta ne ya faɗi amma sai ta kawar da damuwar abin da ta gani ta ce.
"Kada ka dinga fita waje ka ji Ridwan."
Riƙe bakinsa ya yi, yana yi mata alamar ya aikata wani laifin. Ɗan zaro ido ta yi, tun ba ta tambaye shi ba ya ce.
"Inna ban daÉ—e da dawowa masarautar nan ba, wai dama Inna ba ke kika haife ni ba?"
Da sauri Sakina ta zaro ido waje bakinta yana rawa ta ce, "A ina ka ji? Kuma ina ka je? Ridwan kana son ka saka mu a matsala ne?"
Kamar ba laifi ya yi ba ya saki murmushi ya ce.
"Allah ba ke ba ce, an ce mini mamana tana gidan nan."
Sai kuma ya yi fuskar tausayi ya ce, "To ko tana ina oho? Amma dai an ce min wai tana sona, kuma babana ma kafin a kashe shi yana sona."
Sakina da ƙirjinta yake bugawa ta rasa mafita sai kawai ta fashe da kuka, ganin tana kuka sai jikinsa ya yi sanyi. Ya matsa kusa da ita ya goge mata hawaye, riƙe hannunsa ta yi ta ce.
"Don Allah ka daina irin wannan maganar Ridwan, za ka saka mu a matsala. Ni da na ga yau kana cikin farinciki na É—auka ma abokan wasa ka samu."
Wata dariyar ya sake yi, ya ajiye allonsa a gefe sannan ya ce.
"Inna ni ba na wasa da kowa a gidan nan, sai wasu mutane masu muhimmanci." Za ta tambaye shi su waye, sai ta ji ya cigaba da cewa.
"Kin san me ya sa yau nake cikin farinciki?"

Girgiza masa kai ta yi, ya miƙe tsaye yana 'yan tsalle-tsalle ya ce.
"Na ji daɗi yau Batul za ta mutu, ni dama ba na ƙaunarta."
A hargitse Sakina ta sake kallonsa, sai gani ta yi ya sake washe mata baki cikin murna.

Book 1 yana gab da ƙarewa, ga masu sha'awar karanta book 2&3 za su iya turo kuɗinsu.
700 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lamabar 07062062624 idan ya kammala zuwa document 1k ne.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
07062062624
[30/11, 21:05] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.

SHAFI NA SHA UKU

Sarki Gambo

Ƙuri Sarki Gambo ya yi wa Malami yana sauraronsa, kamar wanda yake nazari sai ya ɗago ya ce.
"Malami waɗanne irin mafita kuka hango mana? Muna fatan ba za ta ɓata mana lokacin da za a fuskanci 'yan biyunmu suna da tawaya ba?"
Cigaba da binciken tsubbunsa Malami ya yi, sai da ya sake É—aukar lokacin sannan ya É—ago ya ce.
"Mafitar guda biyu ce kamar yadda na faɗa maka da farko, kuma a karo na biyu haka binciken ya sake maimaita mana. Mafita ta farko, zan yi aiki da idanun mikiya, kan baƙin maciji da kuma ƙoƙan kan ɗan'uwan wancan tsohon."
Cikin sauri Sarki Gambo ya ce. "Wanne tsoho kenan?"

"Tsoho Sulaimanu!"

Malami ya furta yana kallon Sarki Gambo, cikin mamaki Sarki Gambo ya ce.
"Malami ban fahimci abin da kuke nufi ba, shin shi tsoho Sulaimanu yana da É—an'uwa ne? Ko kuwa shi kansa tsoho Sulaimanu kuke nufi?" Malami ya girgiza kai ya ce.

"Tsoho Sulaimanu yana da ɗan'uwa Babagana, kuma su ɗin tagwaye ne. Sai dai wannan wani sirri ne da ba kowa ne ya san da shi ba, kuma kaifin ƙwaƙwalwa da hangen nesan Babagana ya zarce tunanin mai tunani. Domin zan iya ce maka ya fi mikiya hangen nesa, don haka zan haɗa wannan aikin da ƙoƙon kansa. Idan na haɗa idon mikiya da ƙoƙon kansa, za su haska mini duk wani duhun sihirin da aka gudanar a kan tagwayenka, shi kuma kan maciji zan yi amafani da shi ne domin ka san duk duniya babu dabbar da ta kai maciji jin motsi ko magana duk ƙanƙantarta. Ragowar mahaɗin kuwa ruwan ƙoramar fadar sarauniya Humaira ne, amma wannan mai sauƙi ne. Domin ina da kyakkyawar alaƙa da Aljani Dakkum, na tabbata shi zai ɗeɓo mini shi."
Ajiyar zuciya Sarki Gambo ya sauke, cikin damuwa ya ce.
"Amma ya aka yi a duk binciken da kuke yi mana ba ku taɓa sanar da mu haka ba? Ya aka yi ba mu san da zancan Babagana ba?"

"Saboda komai yana da sila Sarki Gambo, a yanzu ma mafitarka ce ta sa muka binciki maka wannan maganar." Malami ya numfasa sai ya cigaba da cewa.
"Mafita ta biyu kuma, sai dai ka ziyarki kogin Sutturu, wanda yake ɗauke da hatsabibiyar bishiyar kukar nan da ake bautawa. Amma wannan ziyarar taka za ta kasance mafi hatsarin gaske, domin kuwa akwai tarun ƙalubale a cikinta, za ka iya dawowa a raye za ka kuma iya haɗuwa da ajalinka. Domin ba iya ziyarar za ka kai ba, akwai waɗansu abubuwa da za ka gudanar a cikin wannan bishiyar kukar. Sai dai kuma, tunkarar mutuwarka sai ya fiye maka sauƙi a kan ka tunkari wannan bishiyar kukar."

"Mun fi aminta da zaɓin farko! Shin a ina za mu samu shi wannan tsohon Babagana? Don shi kaɗai ne abin da zai nemi wahalar da mu, tun da mikiya da maciji ba za su yi wahalar samu ba." Sarki Gambo ya furta yana kallon Malami. Murmushi Malami ya yi ya ce.

"A yanzu haka Babagana yana ɓoye a fadar sarki Dikko, kuma wannan fadar ta kasance hatsabibiyar da sihiri bai cika tasiri ba. Da ace mutum ɗaya tana raye, ita ce za ka iya samun shiga salin-alin ba tare da wani mummunan al'amari ya faru da ita ba."

"Wace ce ita?"

Sarki Gambo ya tambaya bakinsa yana rawa. Malami ya ajiye bangon ƙur'anin hannunsa ya ce.
"Fulani Karima! Sai dai kuma koda ace tana raye, zai yi wuya ta karɓi buƙatarka hannu bibbiyu. "
A wannan karon damuwar Sarki Gambo ta sake yawa, cikin sanyin jiki ya ce.
"Mene ne mafita tun da ba ta raye?"

"Mafita É—aya ce ka nemi amintacciyar baiwarka, ko wata makusanciyarka. Ka aikata masarautar Sarki Dikko, domin ta san duk wani shige da fican makircin da za ta yi ta samu nasarar auren Sarki Dikko."
Malami yana gama faÉ—a Sarki Gambo ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Idan har wannan ce mafita an gama Malami, domin a kan tagwayena babu abin da ba zan iya aikatawa ba."
Malami ya jinjina kai ya ce.
"Za ka iya tafiya Sarki Gambo, ragowar tattaunawar za mu yi ta daga baya."
Da yake zuciyar Sarki Gambo a cunkushe take da damuwa, miƙewa ya yi ya fice ba tare da ya yi wa Malami sallama ba.

Sarki Gambo yana zuwa turakarsa ya aika aka kira masa Fulani Sadiya, sai da ta sheƙa kwalliya sannan ta ƙarasa cikin takun isa da ƙasaita.
"Barka da hutawa sadaukina!"
Fulani Sadiya ta furta tana sakin shu'umin murmushi, don kallo É—aya ta yi masa ta fahimci yana cikin matsananciyar damuwa.
"Barka dai Fulani!"
Ya amsa mata murya babu yabo babu fallasa, Fulani Sadiya ta sake narke murya cike da kissa ta ce.

"Ina kewar Sarki na tsawon kwanaki, sai dai damuwar da ta cunshe shi tana yunƙurin shata layi tsakanina da shi."
Shi kansa ya san ya yi kewarta, don haka cikin shauƙin so ya ƙarasa kusa da ita ya riƙo hannunta. Da ɗayan hannunsa ya tallafo kanta, suka fuskanci juna kowannensu yana sauke ajiyar zuciya. Zame alƙyabbar jikinta ta yi, ta lumshe ido cike da jan hankali ta ce.
"A kullum na kan tuhumi zuciyata, ko na jefa mata tarin tambayoyin dalilin da ya sa ta afka da'irar ƙaunarka."
Kalamanta ne suka fara tasiri a kansa, don haka a kasalance ya ɗago haɓarta ya haɗe bakinsu wuri ɗaya. Fulani Sadiya ƙwararriyar ce wurin gogewa a kissa da kisisina, don haka duk irin fushin da Sarki Gambo yake ciki matuƙar zai gayyato ta makwancinsa, to tabbas za ta yaye masa kaso mafi yawa daga cikin damuwar da yake ciki.

Cikin salonta, ta shiga sarrafa shi har sai da ta lura saƙon da take isar masa ya gama mamaye ilahirin jikinsa. Zare jikinta ta yi daga na shi, cikin wani irin yanayi ta ce.
"Gwarzona!"

"Me ya sa kika dakatar da mu? Alhalin kin san jikinku ya zame mana madogarar da ke yaye duk damuwar da muke ciki."
Tallafo fuskarsa ta yi, ta sa bakinta ta sakar masa sumba a saman laɓɓansa. Tabbas idan ta ce Sarki Gambo mummuna ta san ta sharara ƙaryar da duk wanda ya ji zai ƙaryatata, tana yunƙurin janye fuskarta ya janyo ta jikinsa ya rungume ta tsam kamar wani zai ƙwace fa. Ɗago idanunta ta yi ta dube shi, kamar mai raɗa cikin sauyin yanayin da ya shiga ya ce.
"Muna cikin damuwa Fulani."

"Dalilin da ya kawo ni turakarka kenan ranka shi daÉ—e, domin damuwar da nake ciki ta ninke taka."
ÆŠan É—agowa ya yi ya zuba mata ido cike da kulawa.

Book 1 ya kusa ƙarewa, masu son cigaban book 2&3 za tura 700 ta acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta nan 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa doc 1k ne.

_MTN AND AIRTEL DATA AVAILABLE...!!🔥_

Monthly data — valid for 30 days

_📶MTN DATA_
• 500MB — 450
• 1GB — 700
• 1.5GB — 1000
• 2GB — 1,300
• 3GB — 1,900
• 5GB — 2,100
Chapter 20 · 0% Book details