← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 24

Sashe 10

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ayarin rukunin bayi ne suke tafe cikin gajiyawa saboda irin doguwar tafiyar da suka yi, ba su ƙarasa cikin masarautar Judala ba sai kusan lokacin da dare ya tsala. A sashen bayi aka zuba su tamkar wasu kayan wanki, a galabaice suke saboda yunwa da ƙishirwa. Don haka suna zuwa a kan ruwa suka fara dira kamar waɗanda suka shekara ba su gan shi ba, bayan da suka sha suka yi ƙat sai ya zamana cikkunansu ya ƙulle saboda rashin abinci. Ƙanan yara maza da mata suka shiga kukan yunwa, da yake ba lokacin abinci ba ne a kan dole iyayensu suka lallashe su don su haƙure wa zuwa wayewar gari.

A lokacin da dare ya tsala sosai, a ƙalla kusan ƙarfe biyu da rabi na dare. Fitsari ne ya tashi Indo, don haka ta dubi katafaren filin da suke kwance. Da tarin bushiyoyin da ke zagaye da su, haka kawai ta ji tsoro ya kama ta. Saboda ko a garinsu babban dalili ne yake fitar da ita waje da daddare, don haka a hankali ta miƙa hannu ta tashi Zinaru tana yin ƙasa da murya ta ce.
"Zinaru! Zinaru!"
Cikin gajiya da magagin bacci Zinaru ta ce, "Tuba muke don Allah ku yi haƙuri ku bar mu a ƙauyukanmu, kada ku kai mu masarautarku mu zame muku bayi."
Sake taɓa ta Indo ta yi don ta fahimci firgicin da suka shiga a lokacin da za a kamo su, daga garinsu ne ya sa Zinaru take surutai har a cikin bacci.

"Zinaru Indo ce, don Allah ki raka ni na yi fitsari."

Sai a lokacin Zinaru ta sake wartsakewa, ta miƙe tana hamma tare da murza idanu tana kalle-kalle.
"Yanzu Indo a wannan dokar dajin za mu tafi fitsari, ni fa wallahi tsoro nake ji."
Indo da fitsari ya gama matsarta ta ce, "Wallahi ni ma tsoron nake ji Zinaru, amma ko É—an gabancan ki taimaka ki raka ni."
A hankali suka fara takawa zuwa bayan ɗakunan Bayin da suke jere, kasancewar duk mutane ne a warwatse ya sa suka ƙara tafiyar da ɗan nisa. Musamman da ya kasance akwai hasken farin wata, sai tsoron da suke ciki ya ragu sosai.

A bakin wata ƙatuwar bishiyar tsamiya Indo da Zinaru suka tsugunna ba tare da addu'a ba, sai da suka gama sannan suka rasa abin da za su yi tsarki da shi. Don haka suka laluba suka ɗauki duwatsu suka shafa a madadain ruwan da ba su samu ba. Miƙewa suka yi suna waigowa suka ganta jingine, a jikin wani ƙaton shuri da ke kallon bishiyar tsamiyar da suke tsaye. Gaban Indo da Zinaru ya yi mummunan bugawa, har sai da kusan lokaci ɗaya suka saka hannuwa biyu suka dafe ƙirjinsu.

"Wash! Wayyo cikina da marata, ku taimaka ku zo ku agaza mini."
Matar ta furta tana yarfe hannu alamar tana cikin tsananin ciwo, sai a lokacin suka lura da tsohon cikin jikinta. Zinaru ce ta yi ta maza ta ce.
"Da me za mu taimaka miki?"

"Naƙuda nake yi wash!"

Ta furta gumi yana sake tsattsafo mata, kallon juna suka yi, jikin Indo ne ya shiga rawa. Ganin haka ya sa Zinaru ta ja hannunta don su yi gaba, cikin galabaita matar ta ce.
"Ku ma mata ne, watarana ba ku san inda za ku tsinci kanku ba, don Allah ku taimaka mini."
Sosai kalamanta suka tausasa zuciyar Indo, ta tsaya cak wuri ɗaya. Da sauri Zinaru ta kalle ta, Indo ta ƙarasa gaban matar cike da tausayawa ta ce.
"Kema kina daga cikin tawagar bayin da aka kawo ne?"

Kai matar ta gyaɗa mata a daidai wannan lokaci suka ji ta saki nishi, nan take jaririyar 'yarta ta faɗo. Tsoro ne ya kama Indo, kasancewar bata taɓa ganin an yi haihuwa a gabanta ba. Da sauri ta ƙarasa wurin Zinaru da ke tsaye har lokacin tana kallonsu, cikin sauri ta ce.
"Zinaru don Allah ki zo ki taimaka mata ke ce kika taɓa haihuwa."

Wani mugun kallo ta watsa mata, cikin masifa ta ce.
"Saboda ni ma ba ni da hankali kamar ke ko? Wai Indo ba za ki zo mu tafi ba?"
Shiru Indo ta yi, ta waiga tana kallon matar tana yankewa jaririyar cibi. Wani ƙaton ganyen ayaba ta ga tana ƙoƙarin cirowa, da sauri Indo ta ciro ta miƙa mata. Sai ta ga ta ɗora jaririyar akansa, ta dubi Indo tana sakin murmushi a galabaice ta ce.

"Sunana Karima kuma a cikin masarautar nan nake, sunan da zan saka wa wannan Jaririyar Batul. Don Allah ki taimaka ki yi mini wata alfarma, ki riƙe mini yariyar nan akwai kayana a bayan shingen can da zan ɗauko."

Kamar Indo ba za ta yi magana ba, jiki a sanyaye ta miƙa hannu ta karɓi jaririyar. Zinaru da ke can gefe tana ganin haka ta saki ƙwafa haɗe da yin tsaki ta yi gaba, tana sake jaddada rashin hankalin da Indo take yi.
Daidai wurin da Karima ta tashi nan ta nuna wa Indo, sai a lokacin ta lura da mazaunin matar a kan ƙaton gidan tururuwa ta yi shi. Ya jiƙe sharkaf da jini, ga waɗansu manyan tururuwai da ba ta taɓa ganin irinsu ba sun zagaye jinin suna ta tsotsa.

"Baiwar Allah zuciyata a cike take da fargaba da ruÉ—a ni, don Allah kada ki cutar da ni."

Indo ta furta zuciyarta tana rawa kamar za ta saka kuka, kama hannunta Karima ta yi, nan take Indo ta ji wani yarr tsigar jikinta ta fara tashi. Ga wani irin sanyi da ta ji hannunta kamar ta tsamo daga cikin ƙanƙara, ta sakar wa da Indo murmushi ta ce.
"Ba zan cutar da ke ba, ungo riƙe wannan."
Karima ta furta tana miƙa mata abu kamar wacce take shirin ba ta abu. Zuciya ɗaya Indo ta miƙa hannunta, Karima ta zuba mata ido har sai da tsoro ya sake mamaye Indo sannan ta ce.

"A duk inda kike zan cigaba da bibiyar rayuwarki, ina son ki riƙe mini Batul tamkar 'yar cikinki. Akwai tarin ƙalulaben da za su afko cikin rayuwarki, sai dai duk abin da ya sha miki duhu. Ki zo bakin shurin nan za ki samu mafita, duk adadin shekarun da zan ɗauko zan dawo gare ki Indo..."

"Don Allah me kike faÉ—a ne? Ban fahimce ki ba."

Karima ba ta tanka mata ba, ta tsugunna ta damƙi ƙasar gjdan turuwar, sannan ta damƙi ta saman shurin. Ta shafa a fuskar Indo, sannan ta shafa a fuskar jaririyarta Batul da ke hannun Indo. Nan take Indo ta ji wata irin juwa tana yunƙurin ɗaukarta, tun tana ganin Karima har ta fara yi mata dishi-dishi. Ba ta yi tsammani ba, ta ji Karima ta matso wurinta ta fara yi mata raɗa a kunne mai kama da barin wasiyya.Tana buɗe idonta ta ji jariraiya Batul ta tsanyare da matsanancin kuka, sai dai ba kukan ne ya fi ɗaga mata hankali ba. Rashin ganin mahaifiyar Batul ya fi hautsina hanjin cikinta, tana fara waige-waige ta ji Zinaru ta ce.
"Indo ba za ki ajiye 'yar nan ki zo mu tafi ba?"

Cikin sauri Indo ta ce, "Ban ganta ba Zinaru, na shiga uku wallahi ban ganta ba."
Kafin Zinaru ta bata amsa suka ga Dogaran sun ƙaraso da sauri suna cewa.
"Kai baƙaƙen munafukai, wato da guduwa za ku yi? Allah Ya tona muku asirinku ku wuce mu je."
Daga Zinaru har Indo rasa mai bakin magana aka yi, Dogarin da ke gaba sai a lokacin ya lura da jaririyar da ke hannun Indo tana kuka. Cikin mamaki ya ce.
"Ke! Dama haihuwa kika yi shi ne har za ki gudu?"

Indo da ta rasa bakin magana sai ta fashe da kuka, saboda gabaÉ—aya tsoro ya kamata ita da ko auren fari ba ta yi ba ya za ta yi da jaririya sabuwar haihuwa.

"Ko ba magana nake yi miki ba?"

Dogarin ya sake buga mata tsawa, Indo da ta rasa mafita cikin kuka ta ce, "A'a ba guduwa zan yi ba."
"To ku wuce mu koma, ƙananan munafukai. An faɗa muku duk girman masarautar nan idan kun shigo za ku iya fita ne?"
Zinaru da Indo suka yi carko-carko musamman Indo da damuwa ta cunkushe mata kai.
"Indo kin ga irin abin da nake gudu ko? Wai ina uwar jaririyar nan? An ya kuwa ba gamo muka yi da aljana ba?"
Kamar Indo tana jira ta ce, "Wallahi Zinaru ban san inda ta yi ba, kamar ƙiftawar ido tana gama yi mini siddabaru na neme ta na rasa. Ni yau na shiga uku."
Duk maganganun da suke yi ƙasa-ƙasa suke yin su, shi ya sa ma Dogaran ba su san wainar da suke toyawa ba.

"Indo ki faÉ—a musu gaskiya kawai."
Zinaru ta faÉ—a tana satar waigensu. Indo ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Yanzu wannan labarin mai kama da almara waye ya zai yarda da shi? Idan aljana ce me ya sa 'yarta ta kasance mutum, wallahi ina cikin tashin hankali Zinaru." Indo ta ƙarasa maganar cikin kuka, musamman da ya kasance ita ma jaririyar ban da kuka babu abin da take tsalawa.

Sarki GiÉ—aÉ—o
Chapter 10 · 0% Book details