← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 24

Sashe 23

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Har yanzu Sarki Gambo bai yi nasara ba, domin bai san wurin da kundi ukun nan suke ɓoye ba. Najibullah ya san da ɗaya, ni kuma na san maɓoyar biyu."
Tsoho Sulaimanu ya katse Kursum, sautin murmushinta ya ji wanda ya alamta masa murmushin takaici ne take yi. Yana shirin yin magana ya ji ta ce.
"A naka tunanin da binciken duk wani mai tsafi ko binciken sirihi ne, ake tsammanin kai ne mutumin da ya san maɓoyar kundi biyun da na hannun Najibullah. Alhalin a zahiri kuma ba haka ba ne, domin kundi biyun da ake tsammanin kana da masaniyar maɓoyarsu ba su ne ainahin kundin da ake muradin mallaka ba."
Cikin tsananin mamaki Tsoho Sulaimanu ya ce, "Me kike nufi Kursum? Shin kina nufin kundi biyun da na sani, da wanda Najibullah ya sani ba su ba ne? Bayan har bokaye da 'yan tsubbu idan suka yi bincike kundin da muka sani suke faÉ—a."

Takunta ya ji ta fara tafiya, sai kuma ya ji ta tsaya cak! A karo na biyu ya sake jin murmushinta sannan ta ce.
"Kundin da ka sani da na Najibullah duka na jabu ne!"
Zumbur Tsoho Sulaimanu ya miƙe yana sake juya kalamanta a zahiri.

Yanzu ne wasan ya fara ɗaukar zafi😆 kada ku manta na faɗa muku shi fa wannan littafin kowa ba abin yarda ba ne.

Don Allah waɗanda suka yi payment su yi mini salam saboda gobe zan buɗe group, saƙonni wasu sun yi ƙasa zan iya manta wasu. In Shaa Allahu saura shafi ɗaya mu kammala book 1 mai son cigaban 2&3 zai biya 700 ta wannan Acc ɗin Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 1k ne.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[30/11, 21:57] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.

SHAFI NA SHA BIYAR

Masarautar Zulwara

Tun Sarki Dikko yana jin ruwa mai sanyi yana mamaye shi, har ya ji yanayin ruwan ya fara sauyawa zuwa mai ɗumi-ɗumi. Wata irin tsawa ya ji ta tashi a cikin kabarin Sarauniya Humaira, ɗakin kabarin ya fara girgiza tamkar ƙasarsa za ta rushe ta haɗiye shi. Duk taurin zuciya irin ta Sarki Dikko, sai da ya ji wani matsanancin tsoro ya kama shi. Har ya fara saddaƙar da shi kansa tasa rayuwar ta zo ƙarshe, saboda ji ya yi ruwan da ya shanye shi ya daskare ta yadda ba zai iya motsa koda ɗan yatsansa. Yana cikin wannan yanayin, sai ya ji ruwan ya fara yin ƙasa. Wutar cikin ɗakin ta dawo kamar yadda take ci da farko, sai dai a ɓangare ɗaya ji ya yi jikinsa ya yi lakwas har da ƙyar yake iya motsa ƙafarsa. Ganin ya samu kansa, Sai Sarki Dikko bai daddara ba. Ya fara jan jiki a sanyaye ya tunkari wurin da littafin yake, yana miƙa hannu ya ji gabansa ya yanke ya faɗi. Amma haka ya yi ta maza ya miƙa hannunsa na hagu da zummar ya ɗauka. Wani irin sagewa mai haɗe da yin sanyi ya yi masa, ya janye hannunsa da ƙyar ya miƙa hannun dama a nan ya samu nasarar ɗauko littafin. Sai dai yana duba littafin ya ji daga bayansa an ce.

"Mutuwa, Rayuwa, Hatsari da Rai."

Da sauri ya waiga, sai dai bai ga komai ba, cike da mamaki ya sake maimaitawa.
"Mutuwa, Rayuwa, Hatsari da Rai. Me hakan yake nufi?"
Ya wurga wa kansa tambaya ba tare da hango wurin da amsar take ba.
Cikin ɗakin ne ya cigaba da girgiza tamkar ƙasar ciki za ta faɗa ciki, don haka cikin sauri Sarki Dikko ya fice daga ɗakin sannan ya sake biyo siriryar doguwar hanyar da ya shigo. Sai da ya ƙasara cikin turakarsa, sannan ya rungume littafin a ƙirjinsa ya runtse ido cike da tsananin farinciki.

"Haƙiƙa na yarda rayuwa kasada ce, cimma buri jajircewa ce. Duk wanda ya yi tseren agali tilas ɗayan biyu zai faru, kodai ya mace murus kuma ya kai ga hawa turbar tudun tsira."

Sarki Dikko ya furta cike da farinciki yana sake ƙanƙame littafin kamar wani zai ƙwace masa. Har ya kai hannu zai buɗe littafin, sai kuma ya saki murmushi ya nufi ɗakin da tsoho Babagana yake zaune. Sai da ya zauna a kujerar da ke fuskantarsa, cikin izza, isa da ƙasaita ya ɗago masa littafin.
Cikin tsananin mamaki Babagana ya É—ago a hargitse yana kallonsa, Sarki Dikko ya saki malalacin murmushi mai É—auke da manufa da izgilanci ya ce.
"Babagana na sha sanar da kai ni mai nasara ne! Duk wani abu da na saka a gaba sai na same shi."
Babagana ya kawar da mamakin fuskarsa, don kada Sarki Dikko ya fahimci lagonsa ya ce.
"Kana da nasara a wurin da nasarar da ma can taka ce, Sarki Dikko kada wannan nasarar da ka samu ta sa ka fara jin ka a matsayin mai nasara."
A ɗan harzuƙe Sarki Dikko ya ce. "Me kake nufi?"

"Ina nufin kai ba komai ba ne, domin wannan abin da ka yi kowanne mai numfashi ma zai iya."

Babagana ya furta, duk waɗannan maganganun yana yin su ne don ya dasa wa Sarki Dikko wasu-wasi a zuciyarsa. Domin har a cikin ransa yake jin tsoro da shakkun makirci da taurin zuciya irin ta Sarki Dikko. Miƙewa tsaye Takawa ya yi, ya kalli Babagana ya bushe da wata mahaukaciyar dariya, wacce ta sake kaɗa hanjin cikin Babagana.

"Matuƙar wannan littafin shi ne zai ja mini gora zuwa ga ɗan uwanka Tsoho Sulaimanu da Dattijuwa Kursum. Ina mai tabbatar maka da nesa ta kusa zuwar mini kusa, haka zalika ina gab da mallakar manyan kundin da kowanne basarake yake fatan samu musamman Sarki Gambo da Sarki Giɗaɗo."
Sarki Dikko ya yi furucinsa yana sake sakin dariyar ƙeta, duk da kalamansa sun sayaya jikin Babagana hakan bai dakushe masa ƙwarin gwawa ba. Cikin yanayin jikin tsufa ya dafa bangon ɗakin ya miƙe, sai da ya yi taku biyu ya matsa gaban Sarki Dikko sannan ya ce.

"Na ji daɗi da rashin sani ya zama babban duhu ga kowanne mai numfashi. Ba zan ce maka uffan a kan maɓoyar Kundi uku ba, haka kuma ba zan dakatar da kai daga bulayin nemansa ba. Sai dai zan ce maka ga wani abu a kan matar sarki da ace da ido da tuni ta gani. Ko kuma na ce maka da magani a gonar yaro, amma rashin sani ya sashi bai sani ba." Babagana ya saki dariyar mugunta. Da sauri Sarki Dikko ya waigo ya ce.

"Akwai abin da ka sani Babagana, ka hanzarta sanar da ni tun ban É—auki mummunan mataki a kanka ba.

Babagana ya gyaɗa kai ya ce, "Tabbas ina da masaniya, ina da sani mai zurfi game da wannan Kundin. Amma ba a yanzu ne lokacin ya dace na motsa ba, hukuncinka kuma a shirye nake da na karɓe shi kowanne iri ne. Amma ka sani, koda ka kashe ni na rantse da sarkin da ya busa mini numfashi. Ba za ka dakatar da wacce take ƙoƙarin ceton rayuwata daga nakasa taka rayuwar ba. Abu ɗaya zan ce maka Sarki Dikko, ita ɗin ta jima da yi maka illa, don ta kowacce fuska ta shammace ka. Ba za ka fuskanci haka ba sai a nan gaba, na tabbata ko ba na raye za ka tuna da kalamaina."

Shiru Sarki Dikko ya yi yana nazari, cike da sanyin jiki ya ce.
"Wace ce ita? A ina take? Me ya sa ban santa ba? Ko a binciken bokayena me ya sa ba su hango mini ita ba?"

"Saboda ita ma ba ta fito ba sai da ta shirya, ta kasance tamkar ingarman dokin da ke gudu a dokar dajin sahara. Ta kasance wuta mai laƙume duk wani makamashi, ita ɗin zakanya ce mai ɗauke da zuciyar gawurtattun zakuna dubu..."

"Ya isa!"

Sarki Diko ya katse Babagana daga maganar da yake yi, cikin ƙufula ya ce.
"Duk hatsabibancinta sai na tsamo ta da hannu."
Babagana ya saki murmushi ya ce.
"Ina maka fatan alheri."
Daga haka Sarki Dikko ya fice daga É—akin cikin takaici.

Sarki Dikko zama ya yi a kan ƙasaitacciyar kujerarsa, ya ɗago littafin da aka buga bangonsa da fatar tsohon jemage. Daga ƙasan litttafin akwai wani gashi, wanda duk wanda ya san gashin ɗawaisu yana gani zai gane shi ne. Daga sama kuma wani gashi ne, wanda duk wani maharbi yana gani zai san gashin jelar zaki ce. Daga tsakiyar bangon littafin cikin rubutun ajami an rubuta 'RUWA A WUTA' Sai waɗansu ƙananan rubuce-rubucen ajami, wanda sai ka ƙura ido sosai za ka gane abin da aka rubuta. Ganin zai wahalar da kansa, ya sa shi buɗe shafin farko ba tare da ya karanta ba.

"Duk kalma É—aya da ka tsallake daga cikin littafin nan, daidai take da gayyato masifar da ba ka yi tsammani ba a kundin rayuwarka."

Ya ji an furta da wata irin murya, wacce yaka jin kamar ya taɓa saninta. Yana sauke idonsa don ya cigaba da karatu ya ji sallamar Shamaki a bakin ƙofa, da sauri ya rufe littafin. Ya ƙarasa can ƙarƙashin gado ya zaro wata tsohuwar akwati ya zura a ciki. Sai da ya koma mazauninsa, sannan ya ba wa Shamaki izinin shiga.

"Allah Ya taimake ka, Allah Ya ƙara maka lafiya. Jakadiya ce take neman iso idan ka lamunce mata ranka shi daɗe." Shamaki ya furta yana sunkuyar da kai ƙasa.
"A ba su dama."
Sarki Dikko ya furta a taƙaice. Cikin girmamawa Shamaki ya ce.
"A huta lafiya ranka shi daÉ—e."
Miƙewa ya yi ya fita bayan Takawa ya ba shi izini, yana fita Jakadiya ta shiga. Sai da ta zube ta kwashi gaisuwa bayan ya amsa mata ta ce.
"Allah Ya taimake ka, Fulani Asiya ce take son ganawa da kai ranka shi daÉ—e."
Murmushi ta ga ya suɓuce masa, cike da annushuwa ya ce.
"A cewa Fulani muna nan zuwa gare ta, mun hutar da ita da zuwa wurinmu."
Chapter 23 · 0% Book details