← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 24

Sashe 13

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarki Dikko ya katse boka Tsumbur, bai tanka masa ba ya cigaba da shafa ƙasar shurin gabansa yana wani zane a kanta sannan ya ce.
"Tauraronka Himlu ne kuma ɗabi'ar nari, sannan duk wani bincikena bai bankaɗo mini ainahin abin da yake ƙunshe a cikin duhun ba."
Ajiyar zuciya Sarki Dikko ya sauke cikin damuwa, yana shirin yin magana boka tsumbur ya katse shi da cewar.
"Sarki Dikko kuna iya ba mu wuri, domin a yanzu haka muna da babban baƙo, shugaban rauhanai na ƙarƙashin ƙasa ya ziyarce mu. Matso kusa mu sanar da kai sharuɗɗanmu, da dokokin da za mu gindaya maka."

Sarki Dikko kamar yana jira, ya yi saurin matsawa kusa da boka tsumbur. Ya jima yana yi masa raɗa, sai dai tun bai kammala ba gumi ya jiƙe shi sharkaf saboda tsananin fargaba da tashin hankali. Har ya buɗe bakinsa zai yi magana boka tsumbur ya ɗaga masa hannu da cewar.
"Mun riga da mun gama zartar da hukunci Sarki Dikko, don haka dabara ta ragewa mai shiga rijiya. Amma muna iya baka shawara, idan har buƙatar hakan ta kama."
Jiki a sanyaye Sarki Dikko ya miƙe, suka fita da Waziri yana fargabar sharuɗɗan da boka ya gindaya masa.

Sarki Dikko yana komawa gida kai tsaye turakarsa ya shiga, kai kawo ya dinga yi a cikin É—aki cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali.

'Shin kana ganin za ka iya fita a kan muradin boka Tsumbur? Ta ina za ka fara?'
'Kada ka manta duk abin da ka yi, za ka yi shi ne domin kyawun goben 'ya'yanka. Idan har ka gagara yin haka, sannu a hankali watarana za a shafe tarihinka da irin sarautar da ka shimfiɗa a doron ƙasa.'
'Buƙatar boka ba abu mai sauƙi ba ce, ya zame maka wajibi ka zage damtse domin gujewa kuskure masa.'

Ire-iren kalaman da zuciyar Sarki Dikko ta dinga wassafa masa kenan, cikin tsananin damuwa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.
"Ya zama dole mu nemo wa kanmu mafita."

Cikin sauri ya buɗe wata ƙaramar ƙofa da ke bangon Yamma na cikin ɗakinsa, wani tsoho ne tukuf a zaune. Sai da Sarki Dikko ya zaune a gefensa sannan ya ce.

"Muhimmiyar magana ce ta kawo ni wurinka Babagana."

"Na riga da na san haka, domin banza ba ta kai zomo kasuwa."
Tsohon ya furta muryarsa tana rawa, Sarki Dikko ya ce.
"Ina mai cigaba da ba ka haƙuri bisa killace ka da na yi a nan na tsahon shekaru, duk da na tabbata duniya ta jima da binne shafin rayuwarka."
Babagana ya saki murmushin takaici sannan ya ce.
"Lokaci zai zo da zan bayyana a idon al'umma, a wannan gaɓar da za ta zo kuwa ina matuƙar tausayinka Sarki Dikko."
Sarki Dikko ya zuba masa manyan idanunsa da suka kaÉ—a jajir, ya dafa kafaÉ—ar Babagana ya ce.

"Kafin lokacin mun gama samun biyan buƙatun kanmu har mun hallaka ka."

"Lokaci ne zai nuna, don yana gab da zuwa a daidai wannan gaɓar." Babagana ya furta yana sakin murmushi, duk tsahon shekarun da Babagana ya ɗauka a wannan ɗakin bai taɓa jin Babagana ya furta doguwar magana haka ba. Don haka tsoro ya so mamaye zuciyarsa, amma gudun kada ya nuna a gabansa ya sa shi cewa.
"Babagana ban san abin da kuka taka ba har kuke ƙoƙarin nuna mana ƙwarin gwiwarku? Shin mene ne abin da kuka taka?"

Kamar yadda yake yi akai-akai, haka yanzun Babagana ya fara tari sama-sama. Sai da Sarki Dikko ya miƙa masa ruwa ya sha, sannan ya ce.
"Ƙwarin gwiwata tana gab da zuwa, sai dai a wanne lokaci? Ni kaina ban sani ba, amma na sani ba za ta taɓa bari gangar jikina ta mace a hannunka ba."

Ajiyar zuciyar Sarki Dikko ya yi sannan ya ce.
"Mu ajiye tattaunawarmu a gefe, za mu ajiye mata lokaci domin mu samu tattaunawa."
Jinjina kai Babagana ya yi ya ce, "Ina sauraronka, wataƙila ina da masaniya a game da damuwarka."

Gyara zama Sarki Dikko ya yi ya ce, "Bayan Waziri babu wanda ya san da wannan sirrin namu Babagana."

"Ba iya Waziri ba, har waɗanda ba ka taɓa tsammani ba sun san da wannan matsalar taka, kai dai ka saka ido mutanen da ke kewaye da kai. Hatta shi kansa Waziri ban gama aminta da shi ba, amma wannan ra'ayinka ne ka ɗauki shawarata ko ka watsar da ita."
Shiru Sarki Dikko ya yi da jin kalaman Babagana, ya ƙura masa ido yana kallo tare da sake jinjina baiwa da hikimar da yake da ita. Sai da ya gyara zamansa sannan ya ce.
"Dattijo Babagana, shin kuna nufin bayan Waziri akwai waÉ—anda suka san ina haifar yara masu nakasa?"
Gyaɗa masa kai Babagana ya yi ya ce. "Ba ka yi mamakin yadda aka yi ni da nake kulle a ƙarƙashin ikonka a tsawon shekaru na sani ba, sai waɗanda suke rayuwar 'yanci a doron ƙasa? Shi ya sa na ce ka cigaba da kula da hagunka da damanka, domin za ka sha mamaki idan ka ji masu son bankaɗa labulen sirrinka."

"Sautari muna mamakin da tambayar kanmu, shin kuna taimakonmu ne ko kuwa mu maƙiyan juna ne Babagana?" Sarki Dikko ya furta yana kallon Babagana, shi ma kallonsa yake sai kuwa ya saki murmushi ya ce.
"Kada ka saki jiki ɗari bisa ɗari da ni Sarki Dikko, domin murmushin maƙiyi ba abin yarda ba ne. Duk wani taimako da za ka ga na yi maka, ina yi ne domin na haskawa mai shirin fitar da ni hanya."

"Wace ce ita?"

Sarki Dikko ya wurga masa tambaya a kausashe, a madadin Babagana ya ba shi amsa sai ya saki murmushi ya ce.
"Bari na saukaka maka bincikenka, mace wacce ta kasance tana yawo a cikin rayuwarka. Amma ka rubuta ka ajiye, duk daren daɗewa za ta zo har cikin nan sannan ta tono duk wani ƙulli da ka binne kuma ta bayyana a idon duniya."

Haɗiye yawu mai ɗaci Sarki Dikko ya yi ya ce, "Mun ji duk kalamanku, ita ma wannan maganar mu ajiye ta a gefe. A ina zan samu Kursum? Kuma a wannen yanki zan haɗu da ɗan'uwanka tsoho Sulaimanu? Domin Boka Tsumbur yana buƙatarsu a cikin aikin da ya yi mana."
"Ba ni zan baka wannn amsar ba, amsarka tana cikin littafin 'Ruwa A Wuta' wanda ka binne shi tare da gawar Sarauniya Humaira."
A hargitse Sarki Dikko ya É—ago yana kallonsa, Babagana ya gyaÉ—a masa kai ya ce.
"Domin kuwa ga dukkan alamu tarihi ne yake yunƙurin maimaita kansa."
Ajiyar zuciya suka saki su duka biyun, daga haka Sarki Dikko ya miƙe ya ce. "Na bar ka lafiya Babagana, ina fatan za ka cigaba da hutawa cikin aminci." Yana gama faɗa bai jira cewar Babagana ba ya fice daga ɗakin. Sai da ya tabbatar ya rufe ƙofar, sannan ya cire kubar ya wuce maɓoyarsa ta sirri sannan ya zauna ya zabga tagumi.

Yana nan zaune babu jimawa, ya ji sallamar Jakadiya daga bakin ƙofa. Sai da ya ba ta izinin shigowa sannan ta shiga cikin girmamawa ta zube a ƙasa tana faɗin.
"Allah Ya taimake ka, Ubangiji Ya ƙara maka lafiya. Allah Ya sauki Fulani Hauwa kulu lafiya, sai dai a gafarce ni abin da ta haifa Allah Ya yi masa rasuwa."
Sarki Dikko ko a jikinsa, saboda ya san ko babu komai yana da waɗanda za su gaje shi su ɓangaren sarauta a wannan lokacin. Don haka ya ce, "A cewa Shamaki su yi duk abin da ya dace, idan an kintsa Fulani muna buƙatar ganawa da su." Godiya Jakadiya ta yi masa ta fice, sannan ta ƙarasa ɗakin Fulani Hauwa kulu. Sai dai tana zuwa ta same ta a bakin ƙofa, ta zube a ƙasa ta ce.
"Allah Ya taimake ki ranka shi daÉ—e ya ce a sanar da Shamaki ya yi abin da ya dace." GyaÉ—a kai Fulani Hauwa kulu ta yi, ta ce.
"Ki je kawai Jakadiya, duk abin da ya dace zan aiwatar wa abin cikina, daga haka kuma zan binne shi a É—akina domin hankalina zai fi kwanciya." Jakadiya tana son sake magana, ganin babu fuska ya sa ita yi godiya sannan ta fice daga sashen Fulani Hauwa kulu. Bayan fitarta Fulanin ta shige É—akinta, ta shafa cikinta tana sakin murmushi sannan ta ce.
"Tun da na gama da wannan shafin, a yanzu ne zan dawo Fulani Karima kamar yadda nake a baya, ba Fulani Hauwa kulun da aka sanni ba."

Masarautar Judala

Kukan da jaririya Batul take tsalawa shi ya tashi mafi yawan bayin da ke kwance suna bacci, jiki a sanyaye Indo ta ƙarasa cikinsu hannunta rungume da jaririyar. Sai da dogaran suka ga su Indo sun zauna, sannan suka wuce suna cigaba da faɗan kamar yadda suke yi a baya.
Ɗaya bayan ɗaya haka suka dinga bin ta da kallon tuhuma, wasu suka fara mamakin yadda ƙaramar yarinya ta haihu lafiya ƙalau ba tare da sun ji nishinta ba. Wasu kuma ganin yadda take raɓe-raɓe, ta sake birkicewa ya sa suka fara zargin ko ba 'ya ce ta halaliya ba. Kallon Zinaru ta yi idonta yana cigaba da zubar da hawaye, Zinaru ta kawar da kai gefe alamar can ta matse miki tana sakin guntun tsaki.

"Ke yarinya ki ba ta ta sha mana, wannan ai É—aukan hakki ne. Ba kya ganin yadda take tsala kuka?"
Wata dattijuwa da aka kamo su tare da su Indo ta furta, birkicewa ta sake yi ta shiga inda-inda ganin haka ya sa suka sake tabbatar da lallai haihuwar fari ce Indo ta yi. Saboda sun lura da yadda take jin nauyin shayar da ita, murmushi Dattijuwar ta saki ta ce.
"Ƙuruci dangin hauka, yarinya ai kowa kika gani da haka ya fara. Bari ki gani, idan aka ce za a bi ta kunya ai da ke ma ba ki kawo haka ba."
Dattijuwa ta sake furtawa, sannan ta miƙe ta isa gaban Indo. Sakata ta yi ta gyara zamanta, ta saka hannu tana ƙoƙarin ciro maman Indo. Wata mata daga gefe ta ce.
"To ko ruwan maman ne bai zo ba? Kin san wasu fa dama sai zuwa wani lokaci yake sauka."
Kamar Indo ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ta, bakinta har rawa yake ta ce.
"Eh bai zo ba."
Chapter 13 · 0% Book details