← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 24

Sashe 4

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan kin ba ni haɗin kai, ba zan wahalar da ke ba. Amma matuƙar za ki yi mini gardama, sai na wahalar da ke sannan kuma na gudanar da binciken da yake gabana."
Malami ya furta a ɗan fusace, Sarki Gambo ne ya take hannunwanta biyun. Duk yadda ta so ƙwacewa fir ta gagara, don haka Malami ya saka hannu ya dangwalo jinin ƙasanta. Ya shafe a jikin farin ƙyallen da aka shafe da shi da turaren jan Burhum, sannan ya dubi Sarki Gambo ya matsa ya fara yi masa raɗa a kunne. Wata mahaukaciyar dariya ya ƙyaƙyace da ita, sannan Malami cigaba da cewa.

"Ka tabbatar da ka bi kowacce hanya da kake ganin za ka bi, wacce al'umma ba za su yi saurin fahimtarka ba. Ka dakatar da masallatai biyun da ake gudanar da ibada a ciki, idan ba haka ba. Akwai miyagun al'amuran da za su cigaba da biyo baya."
Cikin damuwa Sarki Gambo ya ce. "Mene ne dalilin yin haka?"

"Idan ka aiwatar zan yi maka bayani daga baya."
Malami ya furta. Har yana gab da fita Sarki Gambo ya ce.
"Bayan waɗannan matsalolin, sai kuma rashin haihuwa da muke fama da ita Malami. Abin yana damunmu, domin a ƙallah mun doshi shekara goma babu haihuwa ni da Fulani Sadiya."

"Idan har ina numfashi za ka haihu Gambo, sai dai ba da Sadiya za ka haihu ba. Yarinyar da za ka aura jinin musulmai ce, wato Khadija. 'Ya a wurin Malam Ubaidu, limamin masallacin yamma. Iya bayanin da zan iya yi maka kenan, zan bincika maka yanayin gamuwar hallitar burujin tauraronku. Idan ban manta ba tauraronka kamar Aƙrabu ne, amma kuma a binciken da na yi kwanaki kamar Jadyu ne ɗabi'a nari. Kada na ja da nisa, ina buƙatar ganin tafin hannun yarinyar domin na karancin ilimin tafin hannunta, ina fatan dai ɗabi'arta ba za ta kasance Nari ba."
Malami ya furta yana shirin fita, har Sarki Gambo zai sake magana sai ya É—aga masa hannu ya ce.

"A yau jawabin da zan yi maka kenan, ita kuma wannan ta gabanka ka aiwatar da abin da na sanar da kai tun lokaci bai ƙure ba." Yana gama maganar ya fita.
Malami yana zuwa bukkarsa ya samu Fulani Sadiya a tsaye, murmushi ya sakar mata sai ya ga ta sake haÉ—e fuska tamau. Kafin ya fara magana ta katse shi da cewa.

"Zuwa yanzu na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba."

Malami sai da ya zauna a kan buzunsa sannan ya ce, "Me kike ci na baka na zuba Fulani?"

"Lokaci yana tafiya, kwanakin Gambo suna ƙara tsayi, har yanzu ba ka hallaka shi ba. Ni kuma a kullum ruhin mahaifina yana sake azabtuwa, idan ba za ka iya ba zan aiwatar da kaina." Ta furta a fusace. Malami ya furzar da iskar bakinsa ya ce.
"Idan Gambo ya mutu yanzu babu ribar da za ki tsinta, rayuwar Gambo a tafin hannuna take. Amma ki sani, gaggawa ba za ta haifar miki da samun É—a mai ido ba."

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
07062062624
[23/11, 22:02] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.

SHAFI NA UKU

https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t
🛍️Assalamu Alaikum – Hafsat Collection ce!
Kinason kayan masu inganci masu kyau kuma cikin sauƙin farashi? To ba ki da matsala! 🥳💃
📌 HAFSAT COLLECTION ta kawo muku: ✨ Kayan gyaran gida
✨ Kayan ado da kyalliya
✨ Kayan mata da maza masu kwalisa
✨ Kayan kitchen masu kyau da karko
🔥 Duk a cikin farashi mai sauƙi!

📦 Muna a Kano, amma muna aikawa zuwa ko ina cikin amincin Ubangiji! 🙏
Maza ki shiga group É—inmu yanzu:
👉
📌 Kasance da Hafsat Collection – Sayan daidai, ko sari!
https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t

Jim Fulani Sadiya ta yi kamar mai nazari, sai ta kafe Malami da wani irin kallo tana nazartarsa sannan ta ce.

"Ba na son na fara dasa zargi a kanka Malami, domin ka san duk duniya babu mutumin da na ba wa yarda kamar kai. Ina gudun na sakankance da kai, a kai gaɓar da za ka fara gasa mini gyaɗa a hannu."

Malami ya saki dariya sannan ya ce, "Tun da na binne sirrinki na wurin marigayya mahaifiyar Sarki Gambo. Ya kamata a ce kin watsar da duk wasu-wasin da ke ɗamfare a cikin zuciyarki, Fulani Sadiya ki sa a zuciyarki ni mai lulluɓa wa ruhinki rumfar kariya da binne sirrinki ne. Babu yadda za a yi na ci amanarki, kin sani na sani. Ni da ke muna amfani da Gambo domin mu cikar muradinmu ne, da zarar mun kai gaɓar da muke muradi za mu yasar da ƙwallon mangoro mu huta da ƙuda."

A fili Fulani Sadiya ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya, sannan ta É—ora da cewa.
"Tun da haka ne, ina son haihuwa da Takawa. Ko babu komai zan bar magaji a masarautar Kajjura, masarautar da babu mai fahimtar gabanta da bayan har sai wanda ya gane sirrinta."

"Ba za ki haihu a masarautar nan ba."
Malami ya katse ta, ya cigaba da cewa.
"Haka kuma har yanzu ba ki san sirrin masarautar nan ba."

"Me ya sa ba zan haihu ba? Kuma wanne sirri ne ya rage da ban gama saninsa ba?"
Fulani Sadiya ta furta cikin damuwa, Malami ya saki murmushi ya ce.

"Saboda mahaifarki tana soke a dutsen Jaddum, haka kuma sirrin Masarautar nan ba za ki taɓa gane shi ba."
Malami ya furta yana buɗe ƙur'anin da ke gefensa, har za ta sake yin magana. Ya ɗaga mata hannu yana cewa.

"A yanzu ina da uzuri Fulani, kina iya dawowa bayan wani lokaci. Domin a daren nan zan sayi rauhanai biyar da za su yi mini wani aiki."

Sam ba haka Fulani Sadiya ta so ba, tana tafiya Malami ya saki murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa. Sai da ya tabbatar da ta yi nisa, sannan ya ɗebi ƙasar sawun ƙafarta. Ya haɗe ta a cikin fatar farin maciji, sannan ya shiga bukkarsa ya ɗora a kan ƙaton shurin da ke tsakiyar gidajen tururwan da ke zagaye da shi.

SARKI GAMBO

Lokacin da Fulani Sadiya ta shiga ɗakinta, ta jima tana kaiwa da kawowa. Kamar wacce aka tsikara, sai ta ƙwala wa baiwarta kira. Cikin girmamawa ta zube ƙasa tana faɗin.

"Hutawarki lafiya uwar gijiyata, Allah Ya ja zamanin giwar sarki. Da yardar Allah Yarima yana bisa hanya, Aljanna mai masoya da yawa. Sikari ba ki yi farin banza..."

"A sanar da Jakadiya ta nemar mini izinin ganin mai martaba."
Fulani Sadiya ta furta a daƙile, jin haka ya sa Baiwa Indo ta sake zubewa ƙasa ta ce.
"An gama ranki shi daÉ—e, hutawarki lafjya mai farar zuciya."
Miƙewa ta yi ta fita kai tsaye ta sanar wa da Jakadiya saƙon Fulani Sadiya, babu jimawa Jakadiya ta nemi izinin shiga ɗakin Fulani Sadiya. A gaggauce ta amsa mata, don a ɗokance take da son ganinsa a wannan lokacin.

"Allah Ya taimake ki, Allah Ya tsare gabanki da bayanki. Takawa bai amsa goron gayyatarki ba, a yi mini afuwa ranki daɗe." Jakadiya ta furta tana sunne kai ƙasa, rai a matuƙar ɓace Fulani Sadiya ta ce.
"Saboda me Takawa zai yi mini haka?"

Jakadiya ta waiga hagu da dama, sannan ta sunne kai ƙasa ta ce.
"Allah Ya taimake ki, ki gafarce ni da abin da zan faÉ—a."
Kallon tsaf Fulani ta yi mata ta ce, "Tafi kanki tsaye."

Jakadiya ta sake yin ƙasa da murya ta ce.
"Allah Ya taimake ki wannan maganar ba za ta faÉ—u ba, sai dai na raÉ—a miki a kunnenki."
Kamar Fulani ta dakatar da ita, sai ta gyaɗa mata kai. Jikin Jakadiya har rawa yake yi, ta matsa saitin kunnen Fulani Sadiya ta fara yi mata raɗa a kunne. Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi, amma sai ta kawar da damuwar fuskarta ta ce.
"Jakadiya an jima zan aiko mini da kyautar alkaki, domin ba zan bar wannan albishir É—in ya tashi a banza ba."
Jikin Jakadiya har rawa yake yi ta zube a ƙasa ta ce.
"Godiya nake ranki shi daÉ—e, an gaida farar mace alkyabbar mata. Allah Ya taimake ki ina neman alfarmar da a taimaka a rufa mini asiri."
Fulani Sadiya ta saki murmushi ta ce, "Kada wannan ya dame ki Jakadiya, ina mai yi miki albashir da yanzu ma muka fara." Jakadiya ta sake zubewa a ƙasa tana godiya sannan ta fita.

TSOHO SULAIMANU

Lokacin da sarkin ƙofa ya tasa ƙeyar tsoho Sulaimau tafiya mai nisa suka yi a cikin masarautar, sai da suka je bakin wata katanga sannan ya damƙa shi a hannun Sarkin horo da ke tsaye fuska babu ɗigon fara'a. Kallo ɗaya tsoho Sulaimu ya yi masa, ya fahimci rashin imani da ƙeƙashewar zuciya ya samu gurbin zama a zuciyarsa.
"Mai martaba ya bayar da umarnin a killace shi a kurkusun ƙasa, a tabbatar da a saka shi a ɗakin Kursum."
Sarkin ƙofa ya furta, sannan ya damƙa shi a hannun Sarkin horo. Kai kawai ya gyaɗa masa, ya dubi tsoho Sulaimanu da jajayen idanunsa masu kama da sabon borkono. Wanda suka sa cikinsa ya kaɗa saboda tashin hankali, da ƙarfi ya hankaɗa tsoho Sulaimanu. Suka bi ta wata siriiriryar hanya, sannan suka ɓulla gaban wata ƙatuwar ƙofa wacce aka sassaƙa ta da farin ƙarfe. Ilahirin saman wurin a zagaye yake da ƙarfe, sai wasu dogarai da ya ci karo da su fuska a murtuke babu alamar fara'a. A nan ma tafiya suka yi mai ɗan nisa, sannan suka ƙarasa wani wuri mai duhun gaske, harshen wuta ya ga an miƙe wa Sarkin horo. Ya karɓi itacen yana haska musu, a nan tsoho Sulaimanu ya ci karo da waɗansu ƙananun ɗakuna. Numfarfashin mutane ya dinga ji sama-sama, wasu kuma ya ji suna roƙon a taimaka a ba su ruwa.
Tsoro ne ya mamaye shi, har yana jin ƙafafuwansa sun yi wani irin sanyi kamar ba na shi ba. Wata mai tsohon ciki ya hango a zaune, cikin galabaita tana cewa.
Chapter 4 · 0% Book details