← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 24

Sashe 22

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uwar bayi sai da ta fito daga fadar sarki Giɗaɗo sannan ta ankara da irin katoɓara da kuma suɓutar bakin da ta yi. Musamman da ta tuna abin da ya faru da Dogari Mamma, gabanta ne ya shiga faɗuwa sai kuma ta tuna wane ne Sarki Gidaɗo da hatsabibancinsa. Da wannan ta ɗan ji faɗuwar gaban ta ragar mata, tana shiga soron farko ta ji kamar an hankaɗa ta har sai da ta kusa faɗuwa. Waigawa ta yi ba ta ga kowa ba, tana juyo da kanta don ta cigaba da tafiya sai ta hangi wata dattijuwa a gabanta. Da sauri ta ja baya tana sauke ajiyar zuciya, tsohuwar ta fara matsawa gabanta cikin muryar tsufa ta ce.
"Uwar bayi sannu da ƙoƙari, ko babu komai za ki taka muhimmiyar rawa a wannan tafiyar..."
Daga haka sai tsohuwar ta wuce soro na biyu, cikin sauri Uwar bayi ta bi ta. Sai dai tana zuwa soron ba ta ji koda takun tafiyar tsohuwar ba. Juya kalaman tsohuwar ta fara yi ba tare da ta fahimci inda suka dosa ba, don haka jiki a sanyaye ta cigaba da tafiya har ta fita daga soron ƙarshe. Zaniru ta hango suna surfe, ta yafito ta da hannu alamar ta zo. Jiki yana rawa Zinaru ta ƙarasa ta ce.
"Barka da fitowa uwar bayi."
Uwar bayi ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Mene ne ma sunaki?"
Cikin sauri Zinaru ta ce, "Sunana Zinaru!"

"Yarinyar jiya da ta haihu fa?"
Uwar bayi ta tambaya tana zuba wa Zinaru idanu, shiru Zinaru ta yi tana nazari, cikin son gwaninta da neman samun wurin zama a wurin Uwar bayi ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Uwar bayi Indo fa ba ita ta haifi jaririyar nan ba, hasali ma Indo budurwa ce ko auren fari ba ta yi ba."
Da sauri Uwar bayi ta dube ta ta ce, "Ke Zinaru ki fito ki yi mini bayani dalla-dalla, domin zancan da nake yi miki yanzu haka Takawa ne ya turo ni na kai ta wurinsa ita da jaririyarta. Kin ga kuwa tun da kin zo da ƙarin haske, za mu tafi da ke domin ki yi bayanin komai a wurinsa."

Ƙuuu! Cikin Zinaru ya bayar da sautin mai ƙarfi, hankali a matuƙar tashe ta ce. "Don girman Allah don zatinSa ki yi mini rai Uwar bayi, wallahi tallahi abin da na faɗa gaskiya ne ba sai an kai ni gaban mai martaba ba." Da wani irin kallo Uwar bayi ta dube ta, sai kuma ta haɗe fuska ta ce.
"Ke Zinaru ki shiga hankalinki, ni da kika gani ban taɓa faɗar magana an musa mini a wannan ɓangaren namu na bayi ba. Saboda haka dole ki wuce mu je har da ke gaban Takawa ki yi masa jawabin abin da kika sani, idan ba haka ba kuwa wani hukuncin daban zai iya biyo wa ta kanki." Uwar Bayi tana gama maganar ta yi gaba, wasu gajerun zafafan hawaye ne suka siraro daga ƙwayar idon Zinaru. Lokaci ɗaya ta ji nadama ta mamaye ta, tana danasanin ɓarin zancan da ta yi don ba ta yi tsammanin wankin hula zai kai ta dare ba.

Zuwaira da Indo suna tsaka da tattaunawa, ba su yi aune ba suka ga Uwar bayi ta bankaÉ—a labulen É—akin. Da sauri duka suka dube ta, kusan lokaci É—aya gabansu ya yanke ya faÉ—i. Saboda ganin yanayin da Uwar bayi take ciki, fuska babu walwala ta ce.
"Ke Indo! Ki É—auko jaririyarki Mai martaba yana son ganinki cikin gaggawa."
A hargitse Indo ta É—ago, nan take jikinta ya É—auki karkarwa har ta matsa gaban Uwar bayi ba tare da ta sani ba.
"Na'am... Uwar bayi... zuwa zan yi?"
Cikin masifa Uwar bayi ta ce. "Kin ji abin da na faɗa tsabar iskanci ne ya sa kike sake tambayata." Kamar Indo ta san abin da yake faruwa, nan take hawaye ya cika idonta. Tana waigawa suka haɗa ido Zuwaira, alamar ta kawo mata ɗauki. Amma sai ta ga ita ma Zuwairar ta sunkuyar fa kai ƙasa cikin sanyin jiki. Babu yadda Indo ta iya, haka ta rungumi Batul ta ja sagaggun ƙafafuwanta ta bi bayan Uwar bayi suka nufi sashen Sarki Gidaɗo. Indo ta yi mamaki da ta ga har da Zinaru aka nufi sashen Takawa, sai dai ko kaɗan ba ta kawo komai ba. Sai ta yi tsammanin ko an gano sun tsinci jaririya a masarautar ne ba tare da sun sanar ba.

Su uwar bayi ne a kan gaba wurin shiga ɗakin, sai Indo da take ƙarshen shiga. Tana tsoma ƙafarta ta ji baƙuwar murya a kunnenta ta ce, "Kada ki shiga, za a salwantar mini da ita. Kada ki manta Indo, amana ce na damƙa miki."

Cak! Indo ta tsaya tana nazari. Kuma ta tabbata muryar Karima mahaifiyar Batul ce, tana nan tsaye kamar an daskarar da ita ta ji muryar Uwar bayi cikin tsawa tana faÉ—in.
"Hattara Indo, kina gaban Mai martaba."
Ajiyar zuciya ta sauke, ta fara takawa a hankali kamar wacce aka zare wa laka a jiki. Tana shiga É—akin ta ji Batul da ke rungume a hannunta ta tsanyare da kuka, a duburburce ta shiga jijjiiga ta gabanta yana cigaba da faÉ—uwa, sai dai har ta zauna Batul ba ta daina tsanyara kuka ba.

"Allah Ya taimake ka, wannan ita ce wacce na ce maka ta haihu jiya a masarautar nan. Sai dai kuma a yanzu maganar ta sha bambam da tawa ranka shi daÉ—e, domin wannan sunanta Zinaru ita kuma ta tabbatar mini da Indo ba ita ce mahaifiyar jaririyar ba. Amma idan ka lamunce mini ranka shi daÉ—e, zan gabatar da Zinaru ta warware mana zare da abawa."
Uwar bayi ta yi maganar cikin girmamawa, fuskar Sarki GiÉ—aÉ—o a murtuke take. Don haka murya babu walwala ya ce.
"Muna sauraren Zinaru."

Indo ce ta ɗan zunguri Zinaru, Zinaru da ta gama yin fiƙi-fiƙi da idanu ta kawar da kai gefe daga kallon Indo ta ce.
"Allah Ya taimake ka, abin da na faÉ—a haka yake. Indo ba ita ce mahaifiyarta ba, hasali ma Indo budurwa ce ko auren fari ba ta yi ba. Jiya da daddare mun fita na raka ta fitsari..."
Zinaru ta kwashe duk iya abin da ta sani ta sanar wa da Sarki Giɗaɗo, ƙuri ya yi wa Indo yana kallo. Cikin rashin imani ya zaro wata sihirtacciya kuma kaifaffiyar askarsa da ke walwali da sheƙi ya ajiye a gefen cinyarsa. Sannan ya dubi Indo cikin wata irin murya ya ce.

"A kawo mana jaririyar nan."

Kalaman Sarki Gidaɗo ya yi daidai da faɗuwar gaban Indo a karo na barkatai, idanuwansa ne suka yi mata kwarjini. Jikinta ya shiga karkarwa kamar mazari, don haka jiki babu ƙwari ta miƙe ta fara takawa har gaban Sarki Gidaɗo. Babu yadda ta iya, haka ta ɗora masa Batul a saman hannunsa, wani irin zummm ya ji, haka ita ma daga ɓangaren Indo. Tana nan durƙushe a gabansa ya ce.

"Wace ce ke? Wace ce ta damƙa muku jaririyar nan? Muna nufin wace ce mahaifiyarta."

Tun sarki Gidaɗo bai rufe baki ba, daga can bakin ƙofa ya ji muryarta ta ƙarade kunnensa da cewar.
"Ni ce mahaifiyarta."
Ba iya sarki GidaÉ—o ba, hatta su Jakadiya mutuwar zaune suka yi suna bin ta da kallo.

Masarautar Kajjura

Jin Tsoho Sulaimanu ya yi shiru ya sake fusata Kursum, don haka a harzuƙe ta matsa wurin da take jin hucinsa. Cikin fusata ta kai hannu ta shaƙo shi, sai ta yi nasarar shaƙar daidai wuyansa. Nan take ya fara kakari tamkar numfashinsa zai rabu da gangar jikinsa, sai da ta ji ya fara fita daga hayyacinsa sannan ta yi wurgi da shi ya faɗi ƙasa yana mayar da numfashi.

"Na ce wane ne kai? Mene ne haÉ—inka da Najibullah? Kuma yaushe ne ya mutu?"

Tsoho Sulaimanu ya furzar da iska yana sauke ajiyar zuciya a galabaice ya ce.
"Sunana Tsoho Sulaimanu, kuma marigayi Najibullah tamkar ɗa yake a wurina." Sai ya haɗiyi yawu mai ɗaci, yana jin ɓacin rai da kewar Najibullah tamkar a lokacin sarki Gambo ya hallaka shi.

"Sarki Gambo ne ya hallaka Najibullah da kisa mai muni, kuma ya sa aka killa ce matarsa Zainaba da zummar idan ta haihu a kashe abin da ta haifa. Idan har kunnuwana ba gizo suke yi mini ba, na ji ya ce zai auri Zainaba idan ta haife cikinta." Kuka ya fara cin ƙarfin Tsoho Sulaimu, sai da ya share hawayensa sannan ya cigaba.
"Ni kaina ya kawo ni wurin nan me saboda na gagara bayyana masa maɓoyar kundin da yake kwana ya tashi da su. Kuma na san a tsawon waɗannan shekarun ya hallaka abin cikin Zainaba. Kaico! Da ban samu nasarar cika burin Najibullah ba."

Tsoho Sulaimanu yana gama maganar ya fashe da kuka, yaraf! Ya ji alamar zamanta a ƙasa. Yana nan zaune bai yi tsammani ba sai ji ya yi ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Jikinsa ne ya sake yin sanyi, don tun daga ranar da ya shiga ɗakin har ya shafe waɗannan shekarun masu tsayi a tare da ita. Bai taɓa jin ta yi kukan da yake jin zafinsa har a cikin zuciyarsa ba. Don haka bai hana ta ba, haka kuma bai san dalilin kukan nata ba. Sai da ta yi mai isarta sannan ya ce.

"Na jima ina jin sautin kukanki, sai dai ban taɓa jin makamancin irin wannan ba. Haƙiƙa akwai wata ɓoyayyar alaƙa tsakaninki da Najibullah, domin yanayinki ya sauya tun a lokacin da na ambaci sunansa."

"Tabbas kalamanka haka suke, domin hawayen mahaifiya ya sha bambam da kowanne irin hawaye a faÉ—in duniya. Wannan kukan da nake yi yana tuna mini tarun abubuwan da suka cunkushe rayuwata. Na farko rashin mijina, mahaifi a wurin É—ana. Na biyu killace ni da azzalumin wancan bawan ya yi tsawon shekaru, ba tare da na cimma muradin mijina ba. Na uku rashin É—ana Najibullah, wanda na É—ora amincewa ta É—ungurungum zai iya dawo da martabar ahalinsa." Kursum ta share hawayenta sannan ta ce.

"A baya zuciyata tamkar dutse take, sai dai a yanzu ta yi laushi tuɓus domin Sarki Gambo ya gama ruguza duk wata ƙwarin gwiwar da ke tattare da ni. Domin ya riga da ya hallaka duk wani..."
Chapter 22 · 0% Book details