← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar yadda ya kasance duk sati a kan buɗe ɗakin da tsoho Sulaimanu, shi da Kursum suke rayuwa ake ba su ruwa haka a wannan ranar ma ta kasance. Sai a gabannin wannan ranakun ba su dalilin da ya sa ake kawo musu abinci akai-akai ba, hakan ne ya rage musu raɗaɗin zaman ƙuncin da suke ciki.
Kamar yadda yake a bisa al'adarta, a yanzun ma tana zaune tana rubuce-rubuce a jikin bango duk da ba ta iya tantance abin da take rubutawa a kuma daidai wurin da take rubutawa saboda tsananin duhu. A wannan ranar tsoho Salaimanu ya ci alawashin sake tunkararta da tambayoyin da ya sha jifanta da su, duk da a duk lokacin da ya yi mata ba sa wanyewa lafiya ƙalau shi da ita. Saboda idan ya yi mata tambayoyin haka za ta dinga kartar jikinsa cikin huci da ɓacin rai, har sai da ya yi tunanin ko ba ta magana saboda tun da ya shiga ɗakin bai taɓa jin kalma ɗaya daga bakinta ta amsa masa ba. Ta yadda ya tabbatar da tana magana, da yake yawan jin tana zikiri da istigifari. Sai kuma idan ta tashi sallah ya ji tana karatun sallah, wani lokacin kuma haka za ta wuni tana kuka ko ta wuni tana karatun alƙur'ani.
Tsoho Sulaimanu a daidai wannan gaɓar shi kansa ya saddaƙar da rayuwarsa za ta ƙare a cikin wannan baƙin ɗakin, domin tun bai ɗauki shekaru a gidan ba Sarki Gambo ya sha turowa a tafi da shi, domin ya bada kai bori ya hau. Amma a kullum aka kai shi furucin da yake faɗa shi yake sake maimaitawa, don haka Sarki Gambo ya ce a ajiye shi su cigaba da zama da Kursum har ƙarshen rayuwarsu.

"A tsawon shekara sama da goma da muka shafe tare a ɗakin nan, ya kamata a ce zuwa yanzu kin watsar da duk wani kallo da zargi da kike yi mini Kursum. Na sha faɗa miki ni ba na daga cikin mutanen Sarki Gambo, amma a kullum gani kike lulluɓe kura nake yi miki da fatar akuya. Wallahi-tallahi ni ma zalincinsa ne ya kawo ni wurin nan, saboda na cika burin marigayi Najibullahi."
Tsoho Sulaimanu ya ƙarasa maganar cikin kuka, ƙashin da take rubutun a jikin bango ta wurgar. A tsorace tsoho Sulaimanu ya ja da baya, don ya yi tsammaninsa a wannan karon ma za ta fara yagar namansa kamar yadda ta saba yi a baya. Ya ji sautin tafiyarta ta ƙaraso wurinsa, cikin dakusasshiyar muryarta mai haɗe da tsufa ya ji ta ce.
"Wane ne kai? Me ya sa ka damu da sanin dalilin zuwana? Mene ne dalilinka na ambatar sunan Najibullah? Ya aka yi ka san shi? Yaushe Najibullah ya mutu?"
Da mamaki tsoho Sulaimau yake bin wurin da yake jin sautinta, cikin tsananin farin ciki ya gyara zama domin ya ba ta amsa, don ya fahimci haƙarsa za ta cimma ruwa ba har ya san wace ce ita.

*Ummou Aslam Bint Adam*
07062062624
[29/11, 23:41] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.

SHAFI NA SHA ÆŠAYA

Masarautar Zulwara

Bayan fitar Jakadiya da ta isar masa da saƙon mutuwar jaririn Fulani Hauwa Kulu Sarki Dikko shiru ya yi yana nazari, ta wani fannin zuciyarsa ta fara ɗaci game da takunkumin da boka Tsumbur ya saka masa.

"Ba ni zan ba ka amsar wurin da Kursum tare da É—an'uwana Sulaimanu suke ba, amsoshinka suna cikin littafin 'Ruwa A Wuta' wanda aka binne tare da gawar Sarauniya Humaira a cikin tsohuwar Fada."
Sarki Dikko ya tuna kalaman da tsoho Babagana ya furta masa, furzar da iska mai zafi ya yi a fili ya ce.
"Dole za mu ziyarci kabarin sarauniya Humaira, domin ranar biyan buƙata rai a ba a bakin komai yake ba."

Yana gama faɗar haka ya buɗe wata ƙatuwar randar ruwa, hannu ya zira ya ɗauko kuba a ƙasan ruwan. Har ya nufi ƙofar fita sai kuma ya yi turus, sakamakon tuna wasu sharuɗɗa shiga cikin kabarin nata. Shiru ya sake yi cikin damuwa, kamar wanda ya tuna wani abu sai kuma ya fita da sauri. Yana zuwa harabar sashensa ya sallami masu tsaron ƙofarsa, ko kaɗan ba ya son aikata abin da idanun masarauta za su hau kansa, duk da ya san yana da ikon aikata fiye da haka. Amma sanin kansa ne, haramun ne kuma kuskure ne sannan zunubi ne halartar kabarin sarauniya Humaira tun shekarun baya. Sakamakon camfin da suka yi a kan waɗansu miyagun al'amura da suke faruwa da su, tun yana ƙarami baya mantawa ya ji an ce mahaifin kakansa ya zartar da dokar hana shiga cikin kabarin ana ajiye kayan tsafe-tsafe, ko kuma ɗiban waɗansu kayan tarihi a fita da shi domin biyan buƙata.
Kabarin Sarauniya Humaira, tsohon kabari ne da ya ɗauki tsahon shekaru masu yawa. Asali an ce adaidai wurin da gawarta take, a nan ne aka gudanar da wani mummunan cin amana tsakanin wasu sarakuna da suka gabata har aka hallaka ta. Wasu kuma suka ce a wurin ne aka gudanar da yaƙin Durr, wanda shi ne silar tsaga masarautu ukun da su sarki Gambo suke jagoranta. Don a wani labarin kunne ya girmi kaka, an ce a da masarauta ɗaya ce a cikin daular. Wani hargitsi da ya gifta ne ya kawo musababbin rabuwarta gida uku, har ya zama akwai wata daɗaɗɗiyar gaba a tsakanin gidaje ukun.

Sai dai kuma a labari mafi shahara, wanda har su Sarki Dikko suka samu labari kuma suka yi na'am da shi. An ce Sarauniya Humaira wata jajirtacciyar sarauniya aka yi a lokacin, mara tsoro ga dakiya da ƙarfin zuciya. Uwa-uba baiwar da aka ce tana da ita, domin duk abin da ya shige maka duhu, ko dai game da sha'anin kasuwanci, aure ko mu'amalar abin da ya shafi mulki. Matuƙar ka kai kukanka wurinta, da zarar ta ɗebi wani ruwan ta zuba a wata 'yar ƙorama da ke tsakiyar fadarta. Nan take za ta samu ilimin duk abin da ya shige maka duhu, kuma ta samu sani a game da tarin tambayoyin da aka yi mata.

Asalin wannan ƙoramar an ce ta hada tushe daga babban kogin ƙasar misira, wasu kuma suka ce tushiyarsa tana da mahaɗa da babban kogin maliya. Sai dai kuma mafi yawa daga cikin masana da masu bincike, sun tabbatar da cewa wannan 'yar ƙoramar ta haɗa tushe da dukka kogunan guda biyu, daga na Maliya har na babban ƙasar Misira. Sai kuma wani shu'umin wani ƙanƙanin kogi da yake cikin dajin Buhul, wanda aka ce daji ne da manyan aljanu da rauhanai suke rayuwa. Wasu sun ce Kakan Sarauniyar Humaira yana da kyakkayawar alaƙa da aljanun wannan yankin, domin har yana da wani babban amini rauhani yake da shi. A saboda haka tun Sarauniya Humaira tana ƙarama kakanta ya kan je wannan dajin da ita, idan ya kai ta sai ta shiga cikin ƙoramar nan ta yi ta wasa tare da sa'anninta 'ya'yan aljanun wancan lokacin.
Amma da labari ya faɗaɗa sai wasu suka ce wata lalura ce ta shigo da wani tsohon rauhani ta masarautarsu Sarauniya Humaira, a nan mahaifinta ya taimaka masa da maganin jinya har ya warke. Saboda mahaifinta tun yana ƙarami yake da baiwar sanin itatuwa da ganyaye domin warkar da masu lalura, kuma tun da rauhanin nan ya warke sai ya bayyana masa kansa, suka cigaba da abota har mahaifinta yake kai ta wannan dajin suna wasa da yaransa. Akwai tarin mabambamtan bayanai dangane da zuwan ƙoramar cikin fadar Sarauniya Humaira, wasu masana binciken tarihi suka ce a ziyarar da take zuwa dajin ne wani hatsabibin aljani ya ce yana sonta. Wasu kuma suka ce ba sonta yake ba, sadaukar da jininta zai yi ga wani boka da yake yi wa tsafi a wancan lokacin. Dalilin haka ya sa rauhanin nan amini mahaifinta, ya samar mata da haɗakar koguna ukun nan a cikin fadar mahaifinta. Wasu kuma suka ce ba haka ba ne domin dalilin yana ƙunshe cikin littafin 'Ruwa A Wuta' Wanda aka binne ta da shi, dalilin mutuwarta, da wasu abubuwan almara da take gudanarwa. Tare da tarin bayanan wasu al'amura na duba da ta yi kuma ta rubuta da za su faru a shekaru masu zuwa bayan mutuwarta. Sai dai shi kansa rubutun littafin an samu rarrabuwar kai game da shi, wasu suka ce Sarauniya Humaira ce ta rubuta littafin da hannunta. Yayin da wasu suka ce ta yaya za ta rubuta labarin mutuwarta? Bayan kuma tana raye, tun da an ce har dalilin mutuwarta da ƙalubalen da za a fuskanta a game da zuwa kabarinta duk ta rubuta. Waɗanda kuma suka yarda da cewar ita ta yi rubutun, sun ce ba abin mamaki ba ne tun da tana rayen ai tana da baiwar faɗar abin da zai faru a gaba kuma ya tabbata.
Chapter 16 · 0% Book details