← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 24

Sashe 6

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ta tanka musu ba, ta tura ƙofar da shiga, sassanyan ƙamshin rumfar Takawa ta daki hancinta har sai da ta lumshe idonta. Cikin takunta na isa da jan hankali ta fara takawa har zuwa turakarsa, sallama ɗauke a bakinta ta shiga tana faɗaɗa fara'arta. A jingine ta hango shi kan ƙasaitacciyar shimfiɗarsa ta alfarma, sai dai ta lura har ta ƙarasa gabansa bai fahimci ruhinta ya wanzu a wurin ba.

"Barka da hutawa sarkin sarakai."

Ta furta cikin salo mai jan hankali, wuri ɗaya ta ga yana kallo don haka ta zauna daga ƙasansa. Sannan ta kai hannu ta shafa sajensa da ke kwance luf a zagaye da fuskarsa. Murmushi ta ga ya sakar mata, ya fara ƙoƙarin kawar da damuwar da ke kwance a saman fuskarsa.
"Barka da shigowa sarauniya."

"Damuwa ba ta dace da gwarzon mazaje ba, nannauyan tunani bai cancanci samun sukuni a tare da kai ba jarumina." Ta furta tana zuba masa idanu, sannan ta É—ora da cewa.
"Idan ban takura Mai martaba ba, ina son sanin damuwar da yake ciki domin na samu sukunin kawar masa da ita."

Janyo ta ya yi jikinsa yana jin tsananin soyayyarta tana mamaye zuciyarsa, haka kawai yake jin soyayar Zannira ta doke duk ragowar matan da ya aura a baya. Nan take ƙirjinsa ya buga, tausayinta da shi ya mamaye shi. Amma gudun kada ya ɗarsa mata damuwa ya sa shi kawar da damuwar zuciyarsa ya ce.

"Akwai baƙin al'amuran da ke shirin faruwa Fulani, kun san jan ragamar sarauta ba abu mai sauƙi ba ne."

Kwanciya ta yi a jikinsa, ta janyo hannunsa ta shiga wasa da shi sannan ta ce.
"Ni san mijina gwarzo ne, don haka babu gwagwarmayar da za ta dagula masa lissafi. Kai É—in jarumin namiji ne, zuciyarka tamkar ta dakarun jarumai dubu ce."
Yadda a ɗan kwanakin da suka yi da Zannira take ba shi ƙwarin gwiwa abin ba ƙaramin birge shi yake ba, ta kai hannunsa saman cikinta sannan ta ce.

"Allah Ya taimake ka wani babban albishir gare ni, ban san da wanne irin tukwici za a saka mini ba."

Cikin zumuɗi Sarki Giɗaɗo ya ce, "Duk abin da Fulani take muradi za mu mallaka mata, matuƙar bai saɓa da tsarin masarautarmu ba."

"A yau da muka cika kwana talatin da biyar da aure, tun wasu kwanaki da suka wuce na yi ɓatan baƙon watana..."

A zabure Sarki Giɗaɗo ya miƙe, cikin zallar farinciki mai haɗe da tashin hankali ya ce.
"Da gaske Zannirata?"
A ɗan kunyace ta sunne kai ƙasa, ta saki murmushi sannan ta gyaɗa masa kai.
Rungume ta ya yi tsam a jikinsa, nan take idanunsa suka fara zubar da ƙwalla. Hawayen fuskarsa ta saka hannu ta share, sannan ta ce.

"Ranka shi daÉ—e, ban yi tsammani har farincikin rabon jikina zai sa ka hawayen farinciki ba."

Sarki Giɗaɗo ya ɗago murya a ɗan dashe ya ce, "Dole mu yi hawayen farinciki Zannira, kyauta ce da tun muka zo duniya ba mu taɓa samun irinta ba. Sai dai kuma kash..."

Jin ya yi shiru ya sa ta ce, "Sai dai me ranka shi daÉ—e?"
Ya ƙaƙalo murmushin yaƙe ya ce.
"Babu komai Fulani, za ku iya tafiya don akwai muhimman abubuwan da za mu duba yanzu."

Kallon tsaf ta yi masa tana karantar yanayinsa, cikin damuwa ta ce.
"Ranka shi daÉ—e!"
Kallonta ya yi ta cigaba da cewa.
"Tun a tsirarun kwanakin da suka gabata, na fahimci sauyinka. Na fahimci kana cikin matsananciyar damuwa, don Allah ranka shi daÉ—e ka warware mini zare da abawar halin da kake ciki."

'Tabbas ba ki yi ƙarya ba Fulani, a kullum na wayi gari zuciyata cike take da fargabar makomar miyagun al'amuran da ke bibiyar rayuwata. '
Amma a fili sai ya ce. "Idan har akwai abin da yake damunmu kune mutanen farko, da za su fara fuskantar damuwar da muke ciki. Muna buƙatar hutawa Fulani, zuwa wayewar gari akwai kyakkyawan albishir da za mu yi wa mahaifiyar yarima."
Murmushi ta yi, don haka ta miƙe tana gyara alkyabbar jikinta. Janyo ta jikinsa ya yi, ya sumbaci goshinta sannan ya sake ta ta fita daga ɗakin.

Zama ya yi a gefen gado, ya dafe kansa da hannuwa biyu. Yana ayyana ga ƙoshi ga kwanan yunwar da ke tun karo shi, kamar wanda aka tsikara da allura haka ya miƙe zumbur ya fita. Yana zuwa ya samu Dogari Isiya da ke kula da ƙofar turakar Takawa, Sarki Giɗaɗo ya ce.
"A gaggauta kira mana Galadima."
Cikin girmamawa dogari Isiya ya ce.
"An gama ranka shi daÉ—e, Allah Ya tsare gabanka da bayanka É—an toron giwa. Gaba salamun baya salamun uban kowa mai taimakon talakawa."
Ɗaki Sarki Giɗaɗo ya shiga, ba a ɗauki lokaci ba Galadima ya ƙaraso yana neman iso. Nan take Sarki ya ba shi izinin shiga, yana zama ya dubi Sarki Giɗaɗo ya ce.
"Allah Ya taimake ka, an aiko kana nemanmu. Ina fatan ba wani laifin muka aikatawa mai martaba ba."

"Akwai gagarumar matsala Lurwanu, wannan wani sirrina ne da za mu bankaÉ—a maka. Wanda babu wani mahaluki da ya san da shi. Don haka muke son mu yi magana da akai a matsayinmu na É—an'uwanka ba sarkin masarautar Judala ba." Jinjina kai Galadima ya yi ya ce.

"Ina sauraronka ɗan'uwana, In Shaa Allahu zan ba ka gudunmawa matuƙar abin bai fi ƙarfina ba. Kuma ni mai lulluɓe maka bargon sutura ne, ba tare da na bayyana sirrinka ba."

"Duk matan da na aura a baya, waɗanda nake kai wa kurkukun zauren horo. Ba gaskiya ba ne laifin da nake laƙaba musu, kowaccensu mutuwa take yi."

A razane Galadima ya É—ago yana kallonsa ya ce, "Ban fahimce ka ba yaya GiÉ—aÉ—o." Ajiyar zuciya Sarki GiÉ—aÉ—o ya sauke ya ce. "Daga kan marigayya Fulani Karima, kun san mun auri mata masu yawa."
Galadima ya jinjina kai, Sarki GiÉ—aÉ—o ya cigaba da cewa.
"To tun bayan mutuwar Karima, duk matar da muka aura bayan kwana arba'in take mutuwa."
A wannan karon Galadima baki da hanci ya saki yana bin sa da kallon mamaki, Sarki Gidaɗo ya miƙe tsaye yana zagaya ɗakin cikin damuwa ya ce.
"Babban abin ya girgiza duniyarmu, ya dagula mana lissafi bai wuce Fulani Zannira ba."
Kallonsa Galadima ya yi yana son jin ƙarin bayani, Sarki Giɗaɗo ya koma kusa da shi ya zaune murya a raunane ya cigaba da cewa.

"Tun da muke aure, babu macen da muka fi so muka fi ƙauna har cikin jikinmu face Fulani Zannira. Kuma a yanzu maganar da muke yi maka, Fulani tana ɗauke da cikin Yarima ko Sarauniya."
A fili Galadima ya faÉ—aÉ—a fara'arsa, ya É—aga hannu cikin jin daÉ—i ya ce.
"Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, haƙiƙa na yi matuƙar farinciki. Domin idan lissafi ba ƙwace mini ya yi ba, ka doshi shekara kusan ashirin da auren fari ba tare da Allah Ya kawo rabo ba."

Ajiyar zuciya Sarki Gidaɗo ya yi, ya sake miƙewa tsaye a karo na biyu yana girgiza kai. Murya ɗauke da damuwa ya ce.
"Ba a nan gizo yake saƙar ba, domin a yau kwanan Fulani Zannira talatin da bakwai. A ƙiyasin mummunan al'amarin da yake bibiyar matan da na aura, saura kwana uku ta yi bankwana da duniya."
Hankali a tashe Galadima ya miƙe, ya matsa kusa da ɗan'uwansa sannan ya ce.
"Ya zama dole mu nemi mafita, domin haka kawai nake ji a jikina banza ba ta kai zomo kasuwa."

"Shi ya sa muka kira ka, domin ku nemar mana mafita. Mun sha zuwa wurin malaman soro a sirrance, amma kwalliya ba ta biya kuÉ—in sabulu ba. Don haka muke son ku nemo mini hatsabibin bokan da zai magance mana damuwarmu. Don mun tabbata, ba zai wuce kaidi da makircin wancan la'annan Sarkin ba."
Galadima ya gyaɗa kai cike da gamsuwa sannan ya ce, "Tabbas biri ya yi kama da mutum, amma wani hanzari ba gudu ba. Zuwa wurin boka sauka daga doron addinin musulumci da saɓa wa Allah ne."

"Idan mun saɓa masa Ubangiji mai gafara ne, idan buƙatarmu ta biya sai mu ɗaga hannu mu nemi yafiyarSa."
Galadima ya jinjina kai, sannan ya yi wa Sarki Giɗaɗo alƙawarin nemo masa hatsabibin bokan da zai warware masa matsalarsa.

MASARAUTAR KAJJURA

Baki ɗauke da sallama Jakadiya da Unguwar zoma suka shiga ɗakin Fulani Khadija. Jakadiya da ke riƙe da ƙoƙon tofi ta ce.
"Allah Ya taimake ki, Allah Ya buɗe ido lafiya. Ranki shi daɗe ga tofin Shamaki ya karɓo a wurin Mai marta..."

Jin kukan ɗaya daga cikin jariran ya sa ta yi saurin ajiye ƙoƙon ta ce.
"Lami maza duba kamar fa ta sauka."
Da sauri suka ƙarasa wurin Fulani Khadija, a nan suka ci karo da jarirai guda biyu suna wutsul-wutsul a ƙasa. Unguwar zoma Lami ta shiga kiciniyar yanke musu cibiya, Jakadiya kuma ta tallafo Fulani a nan ta ci karo da jinin da ke tsartuwa daga ƙirjinta.

"Fulani! Fulani! Innalillahi Fulani me nake gani haka? Lami taya ni gani ko idanuna ne."
Jakadiya ta furta cikin tsananin kaÉ—uwa da tashin hankali. Lami tana É—agowa ta yi tozali da yanayin Fulani, nan take jikinta ya shiga karkarwa ta ce.
"Na shiga uku ni Lami, yau wacce irin baƙar rana nake gani."

"Maza-maza É—aurewa tagwayen cibiya kada su mutu mu sake shiga uku."
Jakadiya ta furta a hargitse. Hannun Lami ban da karkarwa babu abin da yake yi, a haka ta samu ta ɗaure musu cibi. Kafin ta ƙarasa Jakadiya ta fita da gudu cikin kururwa ta sanar da abin da ya faru.

Kafin wani lokaci tuni labari ya zagaye cikin masarautar, Bayi, Dogarai da masu sarautar masarautar lokaci É—aya jikinsu ya yi sanyi. Saboda kowa ya shaidi Fulani Khadija mutuniyar kirkice, don haka mutuwarta ta zo musu a bazata musamman da ya kasance kisan rashin imani aka yi mata.
Sarki Gambo yana zaune a turakarsa, Shamaki ya faɗa ɗakin babu ko neman izini kamar wanda aka jefo daga sama. Jiki da muryarsa suna rawa ya zube a ƙasa ya ce.
"A gafarce ni ranka shi daɗe, a yi mini aikin gafara. Tuba nake uban talakawa, tuba nake damo sarkin haƙuri. Tuba nake jarumin sarki mai dakakkiyar zuciya, a yi mini afuwa bisa mummunan furucin da zai fito daga bakina."
Chapter 6 · 0% Book details