Sashe 19
Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wannan lokacin babu wanda ya hana Indo tatsar nonon akuyar, don haka ta cika cikin Batul taf sannan ta taso ta dawo sashen bayi. Duk jin ta take babu daɗi, saboda ta lura zuwa wannan lokacin Batul a gajiye take tuɓus, don har kawo lokacin ko ruwan zafi jikinta bai gani ba. Hatta sutura babu a jikinta sai zanin da mahaifiyarta Karima ta naɗe ta da shi. Tana komawa ta tarar da an kai musu abinci, kallon miyar kukar ta yi sau ɗaya ta ɗauke kanta saboda yadda ta ji zuciyarta tana tashi. Amma jin yunwa za ta illatata ya sa ta matsa kusa da su, har za ta saka hannu Zuwaira ta ce.
"Indo ga abincinki na ajiye miki, cikin jego ne da ke bai kamata ki shiga cikinmu ki ci abinci ba." Cikin jin daɗi Indo ta yi mata murmushi haɗe da godiya, suna cikin cin abinci uwar bayi ta ƙarasa kansu daga bakin ƙofa ta ce idan sun gama su fito, kowacce za a bata aikin da za ta dinga gudanarwa. Amsawa suka yi, sai da suka gama cin abinci, sannan Zuwaira ta dubi Indo ta ce.
"Akwai ruwan da na roƙi alfarma a wurin uwar tuwo na ɗora, idan kin gama zan yi mata wanka." Gyaɗa kai Indo ta yi, sai dai kuma har kawo lokacin zuciyarta ba ta gama nutsuwa da Zuwaira ba. Cikin ƙanƙanin lokaci bayin ɗakin duka suka watse, Zuwaira ta ɗauko ruwa ta surka a wata ƙatuwar kwarya sannan ta karɓi Batul ta fara yi mata wanka. Shiru Indo ta yi tana kallon yadda ake wankan, don dama ko kaɗan ba ta san yadda ake yi ba.
Sai da mutanen É—akin gabaÉ—aya suka fita sannan Zuwaira ta dubi Indo ta ce.
"Indo wace ce ke?"
Da mamaki Indo ta yamutsa fuska ta ce, "Ni kuma? Me kika gani?"
Zuwaira ta gyara riƙon Batul ta naɗe ta da ɗankwalinta ta ce.
"Batul ba kowacce irin yarinya ba ce, haƙiƙa wannan yarinyar Suryu ce."
"Suryu! Me hakan yake nufi?"
Indo ta tambaya, Zuwaira ta sake ƙura wa Batul ido, ita ma Indo kallon Batul ta yi lokaci ɗaya suka ga idonta ya fara fitar da farin hayaƙi. Cikin sauri Indo ta ja baya ta ce, "Mene ne a idonta?"
Zuwaira ta sake jinjina kai ta ce, "Wallahi yarinyar nan Suryu ce, ita ce wacce tsoho Baushe ya sanar da ni."
Sake kallonta Indo ta yi, Zuwaira ta gyaÉ—a kai ta cigaba da cewa.
"Akwai manyan cutukan da suke addabar rayuwata, lokacin da na je wurin Baushe sai ya ce mini laƙanin makarin lalurar jikina sai na shayar da jaririya Suryu, wacce ta fito daga wani irin tsatso mai rikitarwa." Zaro ido Indo ta yi, Zuwaira ta cigaba da cewa.
"Sai dai ina jin tsoro, tun lokacin da na ga alamunta sun bayyana."
"Tsoro kuma? Tsoron me?"
Indo ta tambaya, Zuwaira ta sauya fuska cikin damuwa, sai ta gyaÉ—a mata kai ta cigaba da cewa.
Sarki GiÉ—aÉ—o
Tamkar wanda ruwa ya shanye haka Sarki GiÉ—aÉ—o ya yi tsuru yana sauraron bokanya Kande, sai da ya ji ta kammala jawabinta sannan ya ce.
"Ki gafarce ni yake mai cetona..."
"Yesu Almasihu shi ne mai ceto ba ni ba."
Bokanya kande ta katse shi a harzuƙe. Russunar da kai ƙasa ya yi ya ce.
"Tuba nake yi bisa aikata saɓo."
GyaÉ—a masa kai ta yi, Sarki GiÉ—aÉ—o ya yi godiya sannan ya cigaba da cewa.
"Ki yi mini afuwa yake hatsabibiya bokanya Kande, haƙiƙa ina cike da ruɗu tare da tashin hankalin jin matata Karima tana raye."
"Wurin nan ba wurin ja'inja ba ne Sarki GiÉ—aÉ—o, idan har kuna tantama game da abin da muka faÉ—a, kuna iya zuwa ku duba kabarinta domin ku tabbatar da abin da muke faÉ—a."
Bokanya Kande ta furta fuska a haɗe, russunar da kai ƙasa ya yi alamar ban haƙuri, Sarki Giɗaɗo ya ce.
"Yanzu ta ina za mu fara wannan aikin yake Bokanya Kande?"
"Ba ma faɗar mafitarmu kai tsaye gabaɗaya, za mu sanar da ku ta cikin baccinku yau da dare idan kun kwanta. Duk abin da kuka gani ko muka bada umarni to hakan za ku zartar da shi, amma kada ku manta muna sake jan hankalinku da ku binciko Karima a duk inda take ko jininta, domin kuwa ita ce maganin matsalarku. Ragowar jawabin zan yi muku a cikin mafarki, kuna iya tashi ku ba mu wuri. Yesu Mai ceto zai yi alfahari da kai, matuƙar ka tabbata a kan addinin gaskiya ba na ɓata ba."
Jiki yana rawa Sarki GiÉ—aÉ—o ya russuna ya ce, "Ina godiya bokanya, sai dai ba a sanar da ni tukwicin da zan bayar ba."
"Tukuwinmu shi ma zai zo a cikin baccinka, domin daga jikinka za mu É—auki abin da muke muradi."
A razane Sarki GiÉ—aÉ—o ya É—ago jin furucin Bokanya Kande ya ce, " A jikinmu kuma?"
"Kada wannan ya razana ka, ba za mu cutar da kai ba. Za mu É—ebi gumin jikinka, tare da duk wani gashi na jikinka, idan ka kuskure wa aljani Æugun, kai da sake samun gashi a jikinka har abada. Wannan ita ce magana ta Æ™arshe da za mu faÉ—a." Daga haka sai ya ga Bokanya Kande ta miÆ™e ta bi ta jikin tafkeken cross É—in da ke fuskantarsu, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya miÆ™e ya fita harabar wurin da ya bar Galadima. Yana zuwa wurin Galadima ba su É“ata lokaci ba, sakamakon kalaman tsubbun da Galadima ya furta wanda bokanya Kande ta koya masa.
Sarki GiÉ—aÉ—o ya jima yana zarya a É—akinsa, haka kawai ya ji soyayyar Zannira tana sake addabar zuciyarsa, ta yadda ba zai iya jure rashinta ba. Musamman da ya tuna tana É—auke ciki a jikinta.
"Ka tabbatar da ka nemo duk wani jariri da aka haifa a cikin masarautarka, ka shafa masa wannan jan garin maganin nan. Matuƙar ka ga jini ya fito daga al'aurarsu mace ko namiji, to tabbas jinin Karima ne."
Sarki Giɗaɗo ya tuna kalaman bokanya Kande, cikin sauri ya miƙe ya nufi ƙofa. Har zai fita, sai kuma ya tsaya cak. Tunowa ya yi da Kabarin Karima, don haka ya yi saurin canja hanya ta ƙofar baya. Ya nufi ɗakin kushewa, babban ɗakin da ake binne duk wani ahali da ya dangancin masarautar. Mukulli ya saka ya buɗe, ya shiga ɗakin cikin sanyin jiki. Sai dai rana ta farko kenan da ya ji gabansa yana tsanannin bugawa, a bakin ƙaton kabarin Karima ya tsaya. Har ya kai hannu, sai kuma ya yi saurin komawa ya tura ƙofar ya rufe. Tamkar ba Sarki Giɗaɗo ba, haka ya zage ya dinga haƙar ƙasar kabarin har sai da ya yashe ta tas. Yana kwashe itacan kan kabarin ya cigaba da dubawa, sai dai sama da ƙasa ya neme ta ba tare da ya ganta ba. Hatta ƙashin da ya ji labarin an ce yana saura a jikin mutum, da likkafani duk bai gani ba. Wata ƙaramar fata ya gani, wacce aka yi rubutu a jikinta. Jikinsa yana rawa ya yi saurin kai hannu ya ɗauka.
"Ka yi kuskure da kake tsammanin za ka hallaka Karima. Sarki Giɗaɗo abin da ka guda shi ne zai faru a daidai gaɓar da ba ka yi tsammani ba, lokaci zai zo da zan yi ajiya mai muhimmanci a cikin fadarka. Sai dai ka sani, yadda ka dakushe mini farincikina, har bada ka yi bankwana da shi. Domin kuwa yadda ka zartar da miyagun al'amura a kaina da mahaifina tsawon kwana arba'in, daga lokacin da na mace a idanun al'umma, kowacce kwana arba'in za ta zame maka mafi masifa da uƙuba a cikin rayuwarka. Ragowar amsoshin da kake buƙata, za ka same su daga bakina a lokacin da ka fahimci Karima ba ta mutu ba. Sai dai ba za ka fahimci hakan ba, har sai lokaci ya ƙure maka. Ba za ka iya ja da ni ba Sarki Giɗaɗo, don a yanzu ba ka da tabbacin mutum ce ko wani jinsin daban."
Sarki Giɗaɗo yana gama karantawa ya yi wurgi da takardar, ko ƙasar kabarin bai mayar ba ya fita daga ɗakin a fusace ya nufi ɗakinsa. A lokacin dare ya tsala sosai, don haka ya haƙurewa washegari gudun kada Zannira ta fahimci wani abin ko ta tada hankalinta. Sai dai yadda ya ga rana, haka ya ƙarasa ganin darensa.
Sai da gari ya waye garau, sannan Sarki Giɗaɗo ya sa aka kira masa Jakadiya, uwar bayi da mai soron baƙi. Kallon fuskarsa kaɗai suka yi, suka fahimci ransa a matuƙar ɓace yake.
"Mun tara ku ne ba don dogon bayani ba, sai don mu sanar da ku. Muna son ku kawo mana duk wani jariri da yake rayuwa a cikin masarautar nan, muna nufin tun daga ɗan shekara biyu zuwa jaririn da aka haifa yanzu. Idan har kuka yi gangancin saɓa mana, mun yi rantsuwa da sarkin da ya busa mana numfashi sai mun azabtar da ruhinku."
Jin kalaman Sarki GiÉ—aÉ—o ya sa Uwar bayi ta yi saurin É—aga hannu jiki yana rawa ta ce, "Allah Ya taimake ka akwai wacce ta haihu a masarautar nan jiya da dare, É—aya daga cikin bayin da aka kawo ce."
Jin kalaman Uwar bayi ya sa Sarki Giɗaɗo ya miƙe zumbur, cikin kausasshiyar murya ya ce.
"A gaggauta kawo mana ita yanzun nan."
Masarautar Kajjura