Sashe 14
Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To 'yar nan ai ba shiru za ki yi ba, yanzu kin ga mu baƙi ne a wurin nan. Ballantana a tatsar mata nonon akuya."
A daidai lokacin da dattijuwar ta furta haka Uwar bayi ta ƙarasa cikin gadara ta ce. "Kai! Ba ma son shashancin banza da wofi, lafiya kuka cika mutane da surutu tun asuba ba ta yi ba? Jaririyar wace da ba za ta kula da ita, sai ta hana mutane bacci?"
GabaÉ—aya shiru suka yi, sai dattijuwar ce ta sake cewa.
"Tuba muke yi, dama yarinyar nan ce ta haihu. To kuma yanzu haka jaririyar sai kuka take ga babu ruwa a maman."
A wulaƙance Uwar bayi ta dubi Indo da ke raɓe tana zare ido, ta taɓe baki ta dube su ta ce.
"Kuma duk cikinku babu mai shayarwa? Ba za a samu wata ta ba ta kafin nata ya zo ba?"
Shiru suka yi babu wanda ya iya magana, sai wata busasshiyar mata ce ta É—aga hannu ta ce.
"Allah Ya taimake ki yanzu haka shayarwa nake, idan mahaifiyar jaririyar ta lamunce sai na shayar da ita."
A sheƙe Uwar bayi ta dubi Indo ta ce, "Kin ji ai abin da ta faɗa, idan kuma ba za ki ba ta ba sai ki bar ta ta yi ta tsala kuka." Tana gama maganar ta yi gaba, har ta fara tafiya ta waigo ta ce. "Idan na sake jin hayaniya har na sake fitowa, to kuwa za ku yaba wa aya zaƙinta."
Tsuru-tsuru suka yi duk tsoro ya sake mamaye su, a hankali Indo ta ƙarasa wurin matar da ta ce za ta shayar da jaririya Batul. Ta miƙa mata ita cikin sanyin jiki ta yi mata godiya, zuciya ɗaya matar ta karɓi Batul ta zauna sannan ta saka mata mama a baki. Batul tana kai bakinta jikin matar sai gani suka yi matar ta yanke jiki ta faɗi.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[26/11, 21:49] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA GOMA
*AF'S DATA PLUG*
_MTN AND AIRTEL DATA AVAILABLE...!!🔥_
Monthly data — valid for 30 days
_📶MTN DATA_
• 500MB — 450
• 1GB — 700
• 1.5GB — 1000
• 2GB — 1,300
• 3GB — 1,900
• 5GB — 2,100
_📶AIRTEL DATA_
• 1GB — 750
• 2GB — 1,400
• 3GB — 2,150
• 3.5GB — 1,800
• 5GB — 2,850
• 6GB — 2,900
• 10GB — 5,600
ð™‹ð™–ð™®ð™¢ð™šð™£ð™© :
Opay — 7049439332
AFNAN ADAM
ð™’ð™ð™–ð™©ð™¨ð˜¼ð™¥ð™¥ ð™‰ð™¤: 09040772027
_Thank youâ¤_
Masarautar Kajjura
Shiru Jakadiya ta yi kamar mai nazari, saboda sai a lokacin take ganin girman wautar da ta aikata na sakin bakin da ta yi a wurin Fulani Zainaba. Cikin inda-inda ta ce.
"Na'am... ranki... shi daÉ—e, dam... dama na ce a yi mini afuwa ban san wurin da turakar sirrin take ba."
Kallon tsaf Fulani Zainaba ta yi mata, ta ƙarasa gabanta murya a kausashe ta ce.
"Idan har kika ɓoye mini wani abu, to tabbas sai na haɗa miki tuggun da ba za ki taɓa fita ba. Ko a kan mutuwar Fulani Khadija, ina iya zarge wuyanki har gaban Mai martaba. Don haka ina son ki feɗe mini biri har wutsiyarsa, idan ba haka ba za ki gane ba ki da wayo."
Cikin Jakadiya ne ya kaÉ—a, cike da tsoro ta ce.
"Don Allah ki yi mini rai, ki yi mini aikin gafara ranki shi daÉ—e."
GyaÉ—a mata kai Fulani Zainaba ta yi ta ce, "Ina sauraronki."
Sai da Jakadiya ta waiga, ta ƙara matsawa gaban Fulani har sai da ya kasance suna jin numfashin juna sannan ta ce.
"Ranki shi daɗe, wani ɓoyayyan sirrin ɗakinsa ne da ke cikin turakarsa. Idan kika shiga rumfar (Falo) ki tsaya a daidai tsakiyarsa, idan kika ɗaga kanki sama daga jikin azarar za ki hangi wata gajeriyar aska a saƙale a sama, ita wannan askar ta tsafi ce. Ita ce za ki ɗauka, ki shafa jinin sarki gambo a jiki. Saboda a yadda na taɓa jin labari, an ce duk shigar da zai yi ɗakin sai ya yanki jikinsa da wannan askar. Jininsa ya taɓa jikin askar, a haka zai zo saitin tsakiyar rumfar ya fara haskawa da ita. A nan za ki ga daidai ƙofar da take shimfiɗar wurin tana yayewa, da zarar kin soka askar ƙasar wurin za ta dare. Idan za ki shiga ki tabbatar askar tana hannunki na hagu, kuma da ita za ki shiga har cikin ɗakin. To da zarar kin shiga, shimfiɗar wurin za ta haɗe ta koma yadda take."
A fili Fulani Zainaba ta sauke ajiyar zuciya, tare da sharce gumin da yake saman goshinta. Cikin damuwa ta ce.
"Jakadiya dole sai ta wannan hanyar?"
Gyaɗa kai Jakadiyanta yi ta ce, "Ai ba a nan ma gizo yake saƙar ba ranki shi daɗe!"
"A ina ne?"
Fulani Zainaba ta yi saurin wurga mata tambaya, gyara zama Jakadiya ta yi ta ce.
"A wurin fitowar ne, don a yadda na ji labari an ce a yadda Sarki Gambo ya sihirce ɗakin ba ya fitowa a take a lokacin da ya shiga, har sai doshin magriba. Sai dai ina jiye miki tsoron kada Sarki Gambo ya gano ki ranki shi daɗe, domin na tabbata sai ya zartar miki da mummunan hukunci, don an ce ya taɓa hallaka ƙaninsa Galadima wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya saboda wannan ɗakin. To da yake dai jita-jita ce, amma zancan da nake yi miki Galadima ya yi ɓatan dabo har yau ba a sake ganinsa ba. Dalilin haka ya sa ake yi masa wannan zargin, amma Allah Shi ya bar wa kansa sani."
Jakadiya ta numfasa sannan ta cigaba da cewa.
"Saboda an ce ba iya waɗannan takardun ne a cikin ɗakin ba, ɗakin ya haɗa duk wani babban sirri da ƙudurin Sarki Gambo. Don a wata majiya da na ji, an ce akwai wata doguwar hanya idan aka bi ta har maɓoyar da Kursum take rayuwa. Don har kawo yanzu, babu wanda ya tabbatar da ainahin abin da ke ƙunshe a cikin ɗakin. Saboda babu wanda ya taɓa shiga cikinsa ya fito har ya cigaba da rayuwa, sakamakon kisan wulaƙancin da yake sa wa ayi wa mutum. Saboda a zargin da ake yi, mutane kusan uku ne suka taɓa gangancin shiga."
Kan Fulani Zainaba ne ya cunkushe, ta miƙe ta fara zagaye tana nazartar kalaman Jakadiya. Duk sai ta ji gwiwarta ta yi sanyi, don gani take ba za ta iya cimma alƙawarin da ta ɗaukar wa marigayin mijinta Najibullah ba.
"Ke da tsoho Sulaimanu kaÉ—ai, kuka rage waÉ—anda za ku cika muradin ahalina. Sai kuma jinina da ke jikinki idan kin sauka lafiya, Zainaba ina ji a jikina za ki yi tsawon rai har ki cika mini burina."
Fulani Zainaba ta tuna kalaman marigayi Najibullah, nan take ta hau girgiza kai ta ce.
"In Shaa Allahu zan iya, zan cika maka burinka matuƙar ina numfashi. Idan har ni da tsoho Sulaimanu mun gagara cika muradinka, jininmu da ke rayuwa a masarautar nan zai kawo ƙarshen komai In Shaa Allah Najibullah. Na zaɓi ya yi ɓoyayyar rayuwa ne, har zuwa lokacin da zai ɗauki fansar zuri'arku."
Jakadiya tana daga zaune ta yi kasaƙe, tana nazari da mamakin yadda aka yi Fulani Zainaba take da ɗa a cikin masarautar ba tare da kowa ya sani ba.
Gyaran muryar da Fulani Zainaba ta yi ya sa Jakadiya ta sake russunar da kai ƙasa ta ce.
"Amma Allah Ya taimake ki, idan kin lamunce zan sanar da ke wata maganar."
Cikin sauri Fulani Zainaba ta waiga ta ce, "Je ki kanki tsaye Jakadiya."
Jakadiya ta yi gyaran murya sannan ta ce, "Allah Ya taimake ki akwai abin da ban sanar da ke ba, amma don girman Allah ki dubi darajar Allah ki rufa mini asiri ranki shi daÉ—e."
Shiru Fulani ta yi don ta fahimci maganar Jakadiya tana da matuƙar muhimmanci, don haka ta zauna a kujerar da ke fuskantarta ta ce.
"Na yi miki alƙawari Jakadiya, tsakanina da Allah babu mahaulikin da zai san da wannan tattaunawar tamu."
Jinjina kai Jakadiya ta yi ta yi ƙasa da murya ta ce, "Allah Ya taimake ki, bayan ke fa akwai wacce take dakon bankaɗa labulen sirrin Sarki Gambo. Wato Fulani Sadiya, don ta jima tana son ta samu irin wannan damar da kike son samu. Kuma ni na san Fulani hatsabibiya ce, matuƙar ta samu labarin kin ziyarci ɗakin sirrin Sarki Gambo, na tabata za ta iya aikata komai domin cikar muradinta."
Ajiyar zuciya Fulani Zainaba ta sauke ta ce, "Na fahimci komai Jakadiya, tun ranar da Sarki Gambo ya kawo ni sashen matansa a matsayina na matarsa. Na fara nazartar hali da É—abi'ar Fulani Sadiya, don haka har yanzu nake kan binciken yadda aka yi Fulani Khadija ta mutu, da irin kisan cin zarafin da aka yi mata. Don abin da ya sa na gagara nutsuwa an tabbatar da an cire zuciyarta, wanda hakan yake alamta mini akwai dalilin yin hakan."
Jakadiya da ta shiga nazarin yadda suka dawo, suka samu Fulani Khadija a daidai gaɓar da take gargarar mutuwa ta ce.
"Allah Ya taimake ki duka zancanki a hanya yake, Allah Ya bayyana gaskiya duk É—acinta."
Fulani Zainaba ta amsa mata sannan ta sallame ta, tare da ba ta kayan sha tara ta arziki. Don tana buƙatar ta huta, domin ta san ta yadda za ta tunkari turakar sarki Gambo. Saboda ta ci alwashin duk rintsi, ba za ta shafe mako guda ba tare da ta tunkari turakar sirrinsa ba. Don ta haka ne za ta samu sukunin karanta wasiƙun da za su yi mata iso zuwa ga wurin da aka killace Kursum kamar yadda Jakadiya ta sanar da ita, cewar ita ce ta san kowanne irin sirrin da ke cikin masarautar.
Fulani Sadiya