← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 24

Sashe 3

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Sarki Gambo ya fara zaro sihirtacciyar takobin hannunsa, nan take tsoro ya ƙara mamaye bayin da suke ɗaure. Don a tunaninsu ɗaya bayan ɗaya haka za a hukunta su, Zainaba tana ganin haka ta durƙushe a wurin. Ba tare da ta damu da tsohon cikin jikinta ba, cikin magiya, roƙo da ƙasƙantarwa ta furta.
"Allah Ya taimake ka, Ubangiji Ya ba ka yawan rai. Kai sarki mai adalci ne, ka yi wa mijina afuwa idan har akwai kuskuren da ya aika..."

"A shekarun da suka gabata, an ce mahaifiyata ta yi irin wannan roƙon da bai amfane ta da komai ba. Zainaba! A matsayina na mijinki, kuma shugabanki. Ina umartarki da kada na sake jin bakinki a wurin nan."
Najibullah ya furta cike da É—acin zuciya, jin haka ya sa Zainaba ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Ajiyar zuciya Sarki Gambo ya sauke, yana jin É—aci a zuciyarsa. Ya É—an russunar da kansa kaÉ—an, ta yadda ba kowa zai ji tattaunawarsu ba ya ce.

"Haƙiƙa tarihi yana ƙoƙarin maimaita kansa kenan Najibullah, sai dai ka sani. Idan har kai ka rayu, abin cikin iyalinka zai zama matacce, iyalinka kuma..."
Sai Sarki Gambo ya saki murmushi, sannan ya ɗago. Sai da ya dubi ilahirin mutanen da ke wurin, sannan ya ɗaga takobin hannunsa yana sakin dariyar ƙeta ya datse kan Najibullah da shi.

A razane Zainaba ta ƙwallah wata irin gigitacciyar ƙara, lokaci ɗaya ta faɗi a wurin babu numfashi. Tsoho Sulaimanu ya sunkuyar da kai ƙasa yana zubar da hawaye, jin abu ya gangaro jikin ƙafarsa ya sa shi buɗe idonsa. A nan ya ci karo da kan Najibullah, a razane ya janye ƙafarsa. Sarki Gambo ya sake kallon Ɗanjuma, ganin haka ya sa Ɗanjuma ya ƙarasa ya kunce tsoho Sulaimanu.

"A umarce shi da ya kawo mana kan wannan ƙasƙantaccan ɗakin gabas, ita kuma matarsa muna buƙatar a bata kulawa har zuwa lokacin da za ta haife cikinta. A tabbatar da an kawo mana jariri ko jaririyar da za ta haifa, ita kuma a killace mana ita." Sarki Gambo ya furta, sai ya fara takawa cikin izza fadawa suka rufa masa baya haɗe da yi masa kirari.

Lokacin da Sarki Gambo ya ƙarasa ɗakin gabas, a zaune ya samu Malami yana duba wata fatar ɓauna wacce take cike da ƙananan rubuce-rubuce. Zama ya yi a kujerar da take kallon ta Malami, Sarki Gambo fuskarsa ɗauke da annushuwa ya ce.

"Komai ya tafi daidai yadda muke muradi."

"Amma kuma tsugunne ba ta ƙare maka ba."
Malami ya furta yana cigaba da karatun ba tare da ya É—ago ba, da mamaki Sarki Gambo ya ce.
"Ai na ɗauka na yarda ƙwallon mango zan huta da ƙuda? Malami ina son ka fitar da ni daga duhu."

Malami ya ninke fatar hannunsa, sannan ya ce.
"Kana neman ka yi kitso da kwarkwarta Sarki Gambo." Cike da damuwa Takawa ya ce.
"Ban fahimce ka ba Malami, na fi so ka warware mini zare da abawa."

Miƙa masa fatar hannunsa ya yi ya ce, "Akwai wanda ya san duka tanadin da kake yi a cikin masarautar nan, domin kuwa a yau da safe na tsinci wasiƙar sirri zuwa ga abokan adawarka." Hannun Sarki Gambo yana rawa ya karɓi fatar ya duba, sai ya ci karo da cewar.

_Kada shirun da ka ji ya sa ka dakata da shirinka, akwai sauran rina a kaba. Domin kuwa ƙoƙofi ukun da kake muradin buɗewa ana shirin haramta maka su. Ba sai ka damu da sanin fatar dabbar da aka yi rubutun ba, kawai ka yi abin da ya dace._

Da mamaki Sarki Gambo ya ce, "Malami ban fahimci komai ba, shin mene ne amfanin wannan rubutun?"
Karɓar fatar Malami ya yi ya ajiye ta a gefe, sannan ya dubi Takawa ya ce.

"A ziyarar da ka kawo mini jiya, akwai wanda ya ji tattaunawarmu. Wannan wasiƙar za a tura ta zuwa ga ɗaya daga cikin sarakuna biyun da baƙin layi ya shata a tsakaninku. Ana sanar da su ka kusa mallakar kundi ukun da na maka bayani, shi ya sa aka siffanta su da ƙofa. Da aka ce kada a damu da sanin fatar dabbar da aka yi rubutu, ana nufin marubucin ba sai ya bayyana kansa ba."
Malami ya miƙe ya fara takawa, yana cikin haka suka ji an nemi izinin shiga ɗakin. Da kansa ya ƙarasa ya buɗe ƙofar, sai ga tsoho Sulaimanu hannunsa ɗauke da kan Najibullah. Kallon-kallo suka tsaya yi wa juna, tsoho Sulaimanu ya kafe shi da ido yana nazartar fuskar Malami da tsantsar cin amanar da ya yi masa.

A gaban Sarki Gambo aka dankwafar da shi, har zai fara magana Malami ya ce.
"Gambo sai ka sake miƙewa tsaye, domin na fahimci idon masarauta har yanzu yana kanka." Jinjina kai Sarki Gambo ya yi sannan ya dubi tsoho Sulaimanu ya ce.

"Duk wata tambaya da zan yi maka ka riga da ka san amsarta. Najibullah ya san maɓoyar kundi ɗaya, kai kuma kana da sani a kan ragowar. Idan ka sanar da ni, za ka tsira da rayuwarka. Idan kuma ka ƙi, za ka ƙare rayuwarka a kurkuku."
Murmushin takaici tsoho Sulaimanu ya yi ya ce, "Idan na sanar da kai ba tsira zan yi ba, don haka ni ba maci amana ba ne. Ba zan taɓa bayyana sirrin nan ba, kuma ina mai tabbatar maka. Lokaci zai zo da za a ɗauki kanka a hannu kamar yadda ka aiwatar wa Najibullah."
A fusace Sarki Gambo ya miƙe ya yi kan tsoho Sulaimanu, cikin zafin nama Malami ya shiga tsakiya. Sannan ya kai bakinsa saitin kunnensa ya yi masa raɗa, jinjina kai Takawa ya yi. Sannan ya koma mazauninsa, Malami ne ya leƙa ya kira sarkin ƙofa. Bayan ya shiga ya zube a gaban Sarki Gambo ya ce.
"Allah Ya taimake ka ranka shi daÉ—e."

"A ɗauki wannan tsohon a kai shi kurkukun ƙarƙashin ƙasa, ɗakin da Kursum take rayuwa." Sarki Gambo ya furta cikin taƙama.
"An gama ranka shi daɗe, Aljanna mai masoya da yawa. Sikari ba ka yi farin banza ba, ina gwanin wani ga nawa. Kabari mai ƙulla sabuwar abota, mutuwa mai sa a tuna barzahu. Gaba salamun bayanka salamun ubangidana maganin kukana, ka yi shekaran jiya, ka yi jiya kuma gobe ma da kai za a yi In Shaa Allahu."

Sarkin ƙofa yana gama yi masa kirarin ya tasa ƙeyar tsoho Sulaimanu, suna fita Malami ya saki murmushi sannan ya ce.
"Ka gama da wannan babin, idan har gumi ta yi gumi. Da ka tuntuɓe shi zai bada kai bori ya hau."

"Ai dole gyaɗa ta yi mai idan ta ƙi ta sha matsa."
Sarki Gambo ya furta yana sakin murmushi, shi da Malami sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama.

ZAINABA

Sarki Gambo yana fita, Dogari Nalami ya sallami ragowar mutanan. Ya bayar da umarni aka yayyafa wa Zainaba ruwa a fuska, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fara bin tsirarun mutanen da ke tsaye a kanta. Uwar bayi ce ta shiga ɗakin ta riƙo ta suka nufi can sashensu na bayi, Zainaba tafiya kawai take yi kamar wacce aka zarewa laka a jiki. A wani ɗaki aka ajiye ta mai ɗauke da mutane biyar, wata mai ciki ɗaya ta gani sai ragowa mata da yara. A gefe ta zauna, tana tuna al'amarin da ya faru da mijinta a kan idonta.

Sannu a hankali ta fara jin mara da bayanta suna yi mata ciwo, ta shiga yarfe hannu tana cije baki saboda a zaba.

"Ki tabbatar kin saka wa matar nan ido, Mai martaba ya ce tana haihuwa a kai masa abin da ta haifa ita kuma a killace ta. Kin san fa a yadda na ji an ce mijinta yana da tsohuwar tsattsamar alaƙa da Takawa, wai shi ya sa ya kashe shi. Kuma an ce kashe jaririn ma zai yi."
Ta ji muryar matan da suke tattaunawa daga wajen ɗakin, tagar ɗakin ta kalla ta ganta 'yar mitsitsiya. Ta ga ƙofar ɗakin a rufe ballantana ta nemi mafakar guduwa, tana cikin haka naƙuda ta ciyo ta gadan-gadan. Tun tana daurewa har ta fara kiran sunan Allah ƙasa-ƙasa, ɗaya daga cikin matan da ke ɗakin ce ta leƙa ta tagar ta ce.
"Wannan matar fa naƙuda take yi."

Dam! Ƙirjinta ya buga, tana nan zaune ta ga uwar bayi ta shiga ɗakin sannan ta sa aka fitar da ƙananan yaran. Yanayin da Zainaba take ciki ne ya tabbatar mata da ta galbaita, kuma har lokacin haihuwa shiru sai jinin da take zubarwa. Uwar bayi ce ta fita, domin ta sanarwa da Takawa abin da yake faruwa. Don ba ta fatan abin da zai sa ta ɓata wa Sarki Gambo rai, musamman da ta fahimci Zainaba na da matuƙar muhimmanci a wurinsa.

Bayan da aka shafe lokaci mai tsayi, Zainab ta haifo jaririnta namiji ƙato. Shigowar uwar bayi ɗakin tare da unguwar zoma ya sa ta ƙarasa wurinta da sauri, jaririn ta yi saurin ɗauka. Sai dai ganin ba ya numfashi ya sa jikinta ya yi sanyi. A ɗarare ta nufi wurin Sarki Gambo, ta zube a gabansa tana sanar da shi abin da ya faru. A tsammaninta ba ƙaramin faɗa zai yi mata ba, amma sai ta ga ko ajikinsa. Ya karɓi jaririn ya ajiye, sannan ya ce a yi gaggawar kawo masa Zainab. Uwar bayi tana fita, Sarki Gambo ya shiga uwar ɗakinsa. Daga ƙarƙashin gadonsa a kwai wani tsohon kabari, ya yashe ƙasar da hannunsa kamar yadda Malami ya ba shi umarni sannan ya tura jaririn ciki ya binne shi.

A daidai lokacin da aka kawo Zainaba dare ya fara yi, kuma a sannan Malami ya sake dawo wa wurin Sarki Gambo. Ta galabaita sosai, hatta idanunta da ƙyar take iya buɗe su. Ƙuri Malami ya yi mata da ido, sannan ya zura hannu a ƙasanta. Duk da yanayin da take ciki hakan bai hana ta kare kanta ba, cikin zafin nama ta bige hannunsa. Ta ɗago shayayyun idanunta tana jifansa da mugun kallo.
Chapter 3 · 0% Book details