← Book details Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunan littafin 'Ruwa A Wuta' Yana da nasaba da ƙoramar fadar Sarauniya Humaira, a lokacin da Sarauniya Humaira tana raye idan ta so yin duba ko nishaɗi ta kansa a ɗebar mata wani ruwan daban na cikin masarautar ta zuba a cikin ƙoramar, tana zubawa sai nan take tsakiyar ƙoramar ta kama da wuta, kuma a zagaye da ita ruwan da ke cikin ƙoramar bai fasa kaɗawa ba. Haka kuma duk wanda ya yi ganganci taɓa wannan ruwan a nan take jikinsa yake sandarewa, daga nan numfashinsa ya ɗauke gabaɗaya. Kuma tun da wannan al'amarin yake faruwa, ba a taɓa jin Sarauniya Humaira ta furta kalma ɗaya game da hakan ba, kuma ba ta taɓa gargaɗi ko jan hankali ga mutane a kan su kiyaye wannan ƙoramar.
Tun daga ranar da aka tsinci gawar Sarauniya Humaira, sai aka ga ƙoramar tana ci da wuta. Sai ruwan ya fara kwarara daga cikin raminsa, haka ita ma wutar ta fara ƙaruwa. Ana tsaka da tsoron halin da aka tsinci kai, sai aka ji irin muryar Sarauniya Humaira daga sama tana shela da bayar da umarnin da a haƙa babban ɗaki mai girma, a kuma sassaƙa mafi gajartar bishiyar kukar da ke Masarautar, kamar yadda ake sassaƙar jirgin ruwa a fafe cikinsa. Sai a saka gawarta a ciki, akai ta ɗakin da ke tsakiyar ƙoramar a binne, tare da wannam littafin da suka gani.

A cikin kaso casa'in da labaran da ake kawowa, an ce Sarauniya Humaira musulma ce. Yayin da mahaifinta ya kasance ƙungurmin kafiri mai bin addinin gargajiya. Wasu kuma suka ce, ita ma tana bin addinin gargajiya saboda a ra'ayinta tana ganin don mutum ya yi haɗakar addinan da yake so ba kuskure ba ne. A lokacin da aka binne ta an ce mutanen da suka yi wannan aikin babu wanda ya rayu, tun daga wannan ranar duk wanda ya shiga ɗakin sai dai a nemi gangar jikinsa a rasa ba tare da an sake ganin wulgar ko mai kama da shi ba. Tun daga nan sai malamai, bokaye da 'yan tsibbu suka shiga fagen binciken abin da yake haddasa haka. Sai da ƙyar suka gano mafitar da za ta sa a kamo bakin zaren ga duk wanda yake da buƙatar shiga ɗakin gawarta, shi ya sa a duk lokacin da mutum zai shiga domin neman biyan buƙatar kansa, ya zama wajibi ya tafi da wanda zai sadaukar da jininsa, ma'ana suna zuwa ɗakin ya fara hankaɗa shi sai daga baya shi kuma ya shiga ya yi abin da zai yi. Tun da aka binne Sarauniya Humaira, ba a taɓa samun mahalukin da ya yi gangancin buɗe cikin kabarin ba. Saboda yadda kowa ya san hatsabibancin ɗakin, da mummunan al'amarin da zai biyo baya. Duk da a hakan ma yawan shigar da ake yi ya haddasa musu abubuwan masu yawa, daga ciki har da ambaliyar ruwa, mutuwar jarirai akai-akai da gurɓatar ruwan kogunan yankin. Tun daga lokacin ne aka haramta wa mutane shiga ɗakin, da niyyar neman biyan buƙata ko yin wani abu.

Sarki Dikko

Sarki Dikko yana nan tsaye yana nazari, ya ga bawa Bukar ya shiga hannunsa ɗauke da daron abincin dakawansa. Sai da ya russuna har ƙasa sannan ya ce, "Allah Ya taimake ka, Allah Ya ƙara maka lafiya. Barka da hutawa uban gidana maganin kukana, Allah Ya ja da kwana ya raya mana Yarima da Sarauniya lafiya."
Farincikin Sarki Dikko ya faɗaɗa har a fili, cikin murya ƙasaita ya ce.
"Bukar a kai daron nan a dawo muna buƙatar ganinku."
Cike da girmamawa bawan ya sake zubewa a ƙasa ya ce.
"An gama ranka shi daÉ—e, ni mai bin umarninka ne."
Murmushin cimma nasara Sarki Dikko ya saki, yana nan tsaye babu jimawa bawan ya dawo yana jiran umarninsa. Itace ya ce ya kunna, sannan ya nuna masa hanyar nufa tsohuwar fada, gaban bawan ne ya faɗi amma sai ya dake ya cigaba da bin umarnin uban gidansa har suka ƙarasa jikin siririyar hanya mai duhun gaske, wacce za ta sada su da tsohuwar ƙofar fadar.

"Rarr... ranka shi...daÉ—e... tsohuwar fada za mu shiga?"
Bawan ya furta bakinsa yana rawa cike da tsoro, kallo ɗaya Sarki Dikko ya yi masa ba tare da ya tanka masa ba. Nan take ya haɗiye kalamansa, yana jin zuciyarsa tana harbawa kamar za ta ɓullo daga ƙirjinsa.
Ƙofar jikin tsohuwar fadar ta yi ƙura sosai, har yana ta yanyame ta gabaɗaya tare da ƙananna ƙwari. Kallon bawan ya yi, da yake ya fahimci abin da yake nufi nan take bawan ya saka hannu ya fara cire yanar da hannunsa, sai dai kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci kwanciyar hankali ta yi bankwana da gangar jikinsa. Sai da ya gama cire yanar, sannan Sarki Dikko ya zura kuba ya fara cire sakatar ciki, wata irin guɗa suka ji cikin zazzaƙar murya mai daɗin sauraro. Sai dai ƙara da kauɗinta yana addabar kunne kamar zai tarwatsa shi, hakan ne ya sa daga Sarki Dikko har bawa Bukar suka toshe kunnuwansu. Sai da suka ji guɗar ta tsagaita, sannan ya cigaba da buɗewa, duk da zuciyarsa tana harbawa sama-sama.

Yana jin ƙofar ta buɗu ya tura ƙauren, nan take wata walƙiya ta haske idanunsu wacce ta sa suka hangi wata mace a tsaye sanye da alkyabba kanta yana kallon sama. Ganin haka ya sa hantar cikin Bawa Bukar ta kaɗa, cikin shammata Sarki Dikko ya hankaɗa shi cikin ɗakin. A karo na farko Sarki Dikko ya ji wata tsawa da ta nemi hargitsa kwanyarsa, duk taurin zuciyarsa sai da ya ji tsoro ya ɗarsar masa. Amma da ya tuna abin da yake tafe da shi, sai ya furzar da iska daga bakinsa wata sabuwar ƙwarin gwiwa ta mamaye shi. Tun lokacin da Sarki Dikko ya hankaɗa Bawa Bukar bai sake jin motsi ba, cikin sanɗa ya dinga takawa yana haske ɗakin da itacen ɗakinsa. Ɗakin ya yi ƙura sosai, duk inda ya taka sai ya ji sautinsa tare da tashin ƙura da yanar da yake cin karo da ita. Sannu a hankali ya fara jin tashin busar sarewa, sai kuma yake jin motsi daga cikin kowacca kusurwar ɗakin. Ajiyar zuciya ya sauke a ɗan tsorace, ganin baƙin al'amuran suna neman zautar da shi ya sa shi tunkarar ɗakin da aka saka gawar Sarauniya Humaira. Sai dai yana ƙarasawa wurin ya ga wutar cikin ɗakin kabarin ta kama, take ƙoramar da ke zagaye da ita ta bayyana. Kamar yadda ya samu labarin yanayin yadda aka ajiye sassaƙaƙƙiyar bishiyar kukar da aka saka gawar Sarauniya Humaira, haka ya gan ta har lokacin da yake komai na ɗakin ana hangowa daga waje. Sai kuma ya hango littafin da ya shigo ɗauka yana kallon kabarin, a lokacin ya faɗaɗa fara'arsa ya cigaba da kusa kai cikin ɗakin har ya ƙarasa wurin bakin ƙofar shiga ɗakin kabarin. Hannunsa ya kai kan ƙofar, lokaci ɗaya ya ji wani zum! Tamkar yadda wayar wuta take jan mutum, yarfe hannu ya gama yi ya sake miƙa hannunsa. Sai dai ga mamakinsa a lokacin babu abin da ya ji, kansa tsaye ya shiga cikin ɗakin da zummar ɗaukar wannan littafin. Bai yi tsammani ba ya ji jiri yana ɗaukarsa, yana shirin dafa bango sai gani ya yi ƙofar ɗakin da ya shigo ta shafe. Harshen wutar da ke gefen kabarin ta yi tsayi zuwa gabansa, a razane ya ja da baya yana sauke ajiyar zuciya. Yana cikin wannan yanayin sai gani ya yi hasken wutar ya ɗauke, daga wurin ƙafafuwansa ya ji wani irin ruwa mai sanyi yana kwararowa jikinsa har zuwa saitin maƙogaronsa.

Masarautar Judala

Ba iya Indo ba hatta ragowar bayin da ke tsaitsaye sai da tsoro ya mamaye su, cikin sauri wasu mata suka yi ta maza suka ƙarasa kan matar. Ɗaya ce ta shiga kiciniyar cire jaririya Batul, sai dai jin yadda jaririyar take shan maman cikin kwanciyar hankali ya sa ta dubi ɗayar ta ce.
"Allah sarki, dubi yarinyar nan ashe yunwa ce. Yanzu yaya za mu yi da ita?"
Cikin sauri É—ayar matar da ke shafawa matar da ke kwance ruwa ta ce.
"Maza cire ta Dago, ba ki ga halin da take ciki ba?"

Da sauri wacce aka kira da Dago ta shiga kiciniyar cire jaririya Batul daga jikinta, sai dai ita kanta abin ya ba ta mamaki yadda jaririya ƙarama take yunƙurin fin ƙarfinta. Ta ɗago tana shirin sanar da su halin da ake ciki, sai ta ji ta yi nasarar raba jaririya Batul da matar. Sai dai babban abin da ya sake ɗaga hankalinsu ganin bakin jaririyar kace-kace da jini, a razane duk suka ja baya. Cikin rawar muryar Dago ta ce.
"Ku taimaka ku raba ni yarinyar nan don Allah." Ta ƙarasa maganar hawaye yana zuba.

"Don Allah ki kula mini da Batul, tamkar yadda za ki kula da 'yar cikinki. Na damƙa miki amanarta, don Allah kada ki ci amanata."
Indo ta tuna kalaman Karima, jiki a sanyaye ta matsa gaban matar ta ce.
"Kawo ta."
Dago tana miƙa wa Indo jariraya Batul suka ga matar da ke kwance a ƙasa ta ɗago, gumi ne ya shiga keto mata tana sauke ajiyar zuciya.

"Wannan wacce irin irin yarinya ce saboda Allah, ku dubi yadda jini yake fita ko dai idanuna ne? Ke yarinya an ya kuwa ba ki da haÉ—i da maita?"

Wata gajeriyar mata ta faɗa a tsorace tana sake leƙa fuskar Batul da ke mamular baki, amma da yake hankulan mutane yana kan matar sai ba su bi ta kan Batul ba.
"Wallahi tun wuri ki koma wurin can ki ajiye musu 'yarsu, don wallahi yarinyar nan ba mutum ba ce. Idan kuma ba haka ba, wallahi za ki kuka da kanki."
Zinaru ta furta wa Indo cike da jan kunne, idanun Indo suka ciko da ƙwalla. Zuciya ta shiga raya mata a kan ta je ta mayar da jaririya Batul, tana cikin wannan nazarin ta ji ana yi wa matar sannu.
Chapter 17 · 0% Book details