← Book details Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 43

Sashe 9

Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin cewa watakila Salisun yana jin su yasa ya daga murya, “kai Salisu, Mu’utar na jiran ka a waje.” Ya fada yana daukar buta ya zagaya yana jinjina kishin matarsa duk da sun tsufa.

Mukhtar yayi nisa a tunanin yadda zai cigaba da harkokin sa tunda ya samu aikin nan Salisu ya fito yana ta baza kamshin turare don kamshin ne ma ya dawo da Mukhtar hayyacin sa.

“Haka dai, kullum cikin tunani.” Abunda ya fara cewa kenan wannan ya sa Mukhtar din murmushi.

“Dan malam yaki halin malam. Wannan kwalliyar fa?” Muktar ɗin ya faɗa lokacin da ya ɗora idanun sa kan Salisun

Juyawa Salisun yayi alamun shi ya hadun nan sannan yace, “haba dan Allah kullum kazo sai ka tsaya anan kamar wani barawo sai kace baka san ɗakina ba a cikin gidan.”

Mukhtar bai amsa masa ba suka fara tafiya cikin layin.

“Toh ya ake ciki ne mutumina. Ya aikin?” Ya tambaya bayan yaga alamar ba zai samu amsa ba.

“Komai normal, Alhamdulillah ana ta ƙoƙari dai.”

“Toh Allah ya taimaka amma nikam Allah ya kiyaye nayi teaching kuma a private degree ne fa dakai na BUK kuma. Kamar ni dai ace nike da result ɗin ace ina teaching Ina? Nooo…” inji Salisun ya fada yana saka hannunsa a aljihu.

Murmushi Muktar ya yi. Kai ai ɗan gata ne kana da uba, ni kuwa wasu ke jira in samo in basu, ƙannena fa huɗu aƙa yanzu duk mata, in ban basu ba ai bana ce su zasu ban ba"

“Nima ɗin ai ba shi Malam ke min komai ba kaima ka sani” Salisun ya faɗa lokacin da yaɗan haɗe rai.

"Amma dai shi ke ciyar ka ko?"

Banza Salisun ya masa tare da yin gaba, iska Muktar ɗin ya furzar kafin ya ɗan ƙara sauri ya taddo shi.

Shiru sukayi saboda kowa da kalar tunanin da yake yi har suka isa majalisar tasu. Kamar ko yaushe in daya ya bawa daya haushi sai su chanja wajen zama. Suna zama kuwa sauran abokanan nasu suka lura.

“Oh ku dai ba kwa girma.”

Mukhtar ya bata rai. “Bar sokon mana. Matar sa ta gamu da wahala, tunda har yanzu ya gaza hankali ya gane a Nigeria ko me ka samu zaka haka zakayi indai ba haram bane”

Fusata Salisu ya yi, " waye maras hankalin ai kai kasan ba hankali ka fini ba, ko dan kawai mutane na fade kana da nutsuwa kake tsanmanin da gaske suke?"

Dafa shi Muktar ya yi "sorry my guy wasa nake, yo banda abun ka ai abokin ɓarawo ɓarawo ne, abinda ya ni shi ya yi ka, ko me nace kamar akaina nake faɗa"

Hararar sa Salisu ya yi "Karka raina mun hankali fa"

Dariya Muktar yasa, nan Salisu ya kuma ƙuluwa

Ibrahim ne wanda ya ce “Haba guys, ya kuke mana haka ne? Please Muktar ka dena dariyar haka" An danyi shiru ana tunanin topic din magana kenan Mukhtar ya leka gefen Salisu cike da zolaya yace,

“Kuma fa kayi kyau yau mutumina. Ya kamata Maryama taga kwalliyar nan ta yaba.”

Banza Salisu yayi kaman bai ji ba.

Miƙewa Muktar ya yi bari in je gida inason kwanciya da wuri sabida tashin safe, har ya yi nisa ya ji Muryar Salisu tsayani zanje Gidan su Maryam suka jera tare suna tafe suna hira tamkar ba sune sukai rikici ɗazun ba ko da yake dama Salisu ne sarkin ruko shi Muktar da ya fahinci abin zai zama faɗa zai mayar wasa in kuma ya zama da anyi shikenan ya wuce.’
Har sun wuce Salisu ya riƙo shi "Please kazo muje yau ɗaya dai"

Kallon agogo Muktar ya yi " na faɗa ma so nake in kwanta da wuri"

Tsaki Salisu ya yi " kwanciya at this time kofa magariba ba'ai ba, ko kuma baka sallah ne yau?"

Haushi ne ya kama Muktar "kaifa ɗan iska ne wallahi, to wanki nake son inyi in maka short test ɗin da na musu and ina son duba Google"

Watsa hannu Salisu ya yi " ba zancen iskanci nasani ko ka fara al'ada ne, yanzu muje in mun dawo zan taya ka wankin"

Dafe kai Muktar ya yi " wai ana dole ne?, ni kasan sam bans son sabgar ƴan mata wallahi, bare ma ƙaramar yarinya irin Maryam ba in da zani"

Jan sa Salisu ya fara "wallahi sai kaje" jin ya rantse yasa Muktar kawai bin sa s baya rai a bace, shi in za'ai komai kar asashi sabgar mata.

Tsaye suke ƙofar gidan su Maryam ɗin Muktar ya harde hannun sa a yalwataccen ƙirjin sa, fuska a ɗaure, Salisu ne ya matso "dan Allah Malam ka taimaka ka saki ranka karka tsoramun ita" hararar sa Muktar ya yi, fitowar Maryam yasa shi fasa faɗar abin da zai ce, ya ɗan saki fuskar sa kaɗan.

Fuskar ta ɗauke da fara'a ta ɗan rissina " lah Malam yau da kai aka zo ina wuni?"

Kafin ya amsa Salisu ya yi caraf ya ce " eyye mai nake son gani wato idaniyar bani suka fara gani ba wato to walllahi kishi nake"

Dariya ta yi "Haba Masoyin Maryam kaima kasan kai na fara gani wai in fara girmama shi matsayin baƙo" ta faɗa cikin salon tata yaudarar, "anma kayi haƙuri bari inkuma fitowa" ta faɗa kamar zata juya .

Murmushi ya yi " ai nasan ni kika fara gani" taɓo Muktar ya yi wanda ya yi saƙaro yana kallon su, kallon da bazaka iya cewa na mamaki bane ko na jin haushi " Malam tana gaida ka kayi tsit"

Murmushi Muktar yayi " ba shiru na yi ba jira nake ku gama soyayyar sai in amsa" kunya ce ta rufe Maryam ko da Muktar bai koyar da ita ba a secondry shiɗin bai da kalar raini bare kuma malamin ta ne.

"Koma dai mene ni karka sa ta dena magana zo ka tafi," Salisu ya faɗa yana ɗan ƙoƙarin tura shi.

Murmushi ya yi "dadai ni na kawo kaina shine za'a koren, Malama Maryam mu kwana lafiya" ya faɗa kafin ya bar gun.

Har ya wuce ya dawo duda gari ya fara duhu amma hakan bazai sa ya kasa gane ɗaya cikin ƙannen sa ba duk inda ya ga wani, Hajara ya hango lafe jikin dutsen dala inda ya raba layin da gidaje yayin da Garba ke tsaye jikin gidan yana kallon ta kwatar da ta raba siririn layin ta musu tsakani dariya kawai take da alamu hirar ko abin da ya faɗa ma ya mata daɗi.

Rai ɓace Muktar ya ƙarasa sam bata ankara da shi ba lokacin da yake tawowa sai muryar sa ta ji "Uban me kike ana" a tsora ce ta bar gun da ɗan gudun ta ba tare da ta tsaya bashi amsa ba.

A fusace ya juyo ya kalli Garba wanda ya yi tsuru tsuru "yanzu in ƙanwar ka ce zaka ji daɗi wani kato ya jawo ta zance wani gurin ba ƙofar gidan ku ba?"

Sosa ƙeya Garba ya hau yi " wallahi ba cutar da ita zan ba nifa auren ta za..""

Ɗaga masa hannu Muktar ya yi "zaka aure tan ka kasa jurewa a baka damar zuwa gida zance, malam ka fita sabgar ta tun kan ƴan sanda suyi mana iyaka" fuuu ya bar gun

Ita kuwa Hajara tana zuwa gida ɗaki ta shige hankali tashe sam batayi tsammanin ganin yayan nata a hanyar ƴan Kado ba tunda tasan sam baya yin area ɗin shi yasa ma ta ce su dinfa haɗuwa da Gaban anan.

"Ke Hajara!!!" Ya faɗa cikin hargowa lokacin da ya shigo gidan "kina ina ne ko sai na fito da ke na tattataki ki"

Jiki a saluɓe ta fito gaban ta na faɗuwa sam bata son abu ya haɗata da yayan nata bare irin wannan, cikin faɗa yake magana " wato da na ce ki fita sabgar yaron nan shine kika koma binsa wani gurin ko, wato ke ba zaki iya maraicin ki ba"

Cikin rawar murya ta ce " wallahi yaya Inna ce ta aikeni ƴan kado gurin Musa mai kilishi shine nagan shi tsayawa ta kenan mu gaisa kazo gun Allah" ta faɗa tana ɗaga hannu sama.

Tsaki yaja " nidai shawara zan baki da ki ɓata sunan ki gwanda ki ce ya fito a aurar dake kowa ya huta" ya faɗa tare da shiga ɗaki ba tare da jiran amsar taba.

Inna ce ta kalle ta " Gaskiya ya faɗa miki gwanda ki ce ya fito kowa ya huta, ni da ki jaza min masifa a gari, ƙarim wani zagin a unguwar na ban muku tarbiyya ba gwamma ko bashi ne in ɗauko inmiki kayan gado"

"Allah inna kawai gaisawa zamuyi yaya yazo..." Harar ta kawai Inna ta yi ta kasa karawa.

***** *********

Yes shigo ya faɗa lokacin da take buga ƙofar Hafsa ce rike da riguna kala biyu ta shigo ɗakin wanda baka jin komai sai ƙamshin air freshener mai sanyaya zuciya ɗan ta shi zaune Usman ya yi daga kwanciyar da ya yi ya dube ta " to sarkin damu mene kuma, kinsan dai ba ɗin ki nake ba ko?"

Murmushi ta yi " kai yaya Usman nima ba ɗin ki na kawo ma, tayani zaɓa wanne zai fi mun kyau zamu je ɗan wani outing ne."

Zaro ido ya yi " what are you mad ke da waye" dariya ta yi "kalli fuskar ka to ni da Hidaya da Bilkisu ne" ajiyar zuciya ya yi ta wasa "oh na ɗauka keda wasu ƙatti ne yanzu mutun ya jawowa kansa"

Dariya tasa mai ƙarfi " kaji Yaya Usman da kuri sai kace zaka iiya wana abu"

Kwafa kawai ya yi " Allah yarinyar nan kin rainani walllahi, wannan ta fi kyau" ya nuna ta hannun daman ta.

Kallon ta ta yi na sakanni " No wannan ta fi" ta faɗa kafin ta fice girgiza kai ya yi wannan yarinyar da matsala take da tasan wadda take so zata zo damun sa.

Bai gama tunanin ba ta dawo "baka ban gudunmawa ba, jiya naje gidan yaya Sadik ya bani nasa saura kai" ta fada tana miƙa hannu.

"Ni mai zan baki?, Shi ai rich man ne ni kinsan am broke, Lecturers are not rich"
Chapter 9 · 0% Book details