← Book details Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 43

Sashe 31

Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya yi "Banda abin Momy kwana nawa ne an gama anma fara test da tayi exam ɗin shikenan , kinga ai da yake sunyi dabara both na second semester ɗin da zatayi da wanda zata gyara Level 2 yake mata, kinga babu batun in tazo level 2 ɗin ya koya mata, yanzu in ance za'a samo wani malamin kafin ta yi adapting to his teaching methods wani abin ne daban, in kuka ta faɗi second semester ina faɗa miki her CGP will be bad, irin mumin da zai adai yi shiru"

Shiru Mum ta yi tana haɗa maganar Usman da Sadik wanda ya mata jiya gaskiya suka faɗa, dole ta haƙura kawai a cigaba amma idanu zata sa musu ta faɗa a ranta, "kaje ka faɗa matan yazo ku tayani sa musu ido"

"Tom" kawai Usman yace tare da wucewa ɗakin Hafsa daga bakin ƙofa ya yi Sallama duda ƙofar a buɗe take yaja ya tsaya, "shigo mana yaya, kullun ina faɗa muku inna bar ƙofar a buɗe kowa zai iya shigowa"

Murmushi ya yi ya shiga zaune take tana kallo a system ɗinta gefen ta kuma danbun Nama ne tana ɗan tsakura, " kinga sauri nake, Malamin kine yazo mun magana da Mum tace zaki iya ci-gaba but make sure kun yi ƙoƙarin covering komai da sauri, kun fasa fitar ne?" ya faɗa.

Sai da ta daure wurin ɓoye murnar ta, bata son ya fara zargin batin mum gaskiya ne barema rannan ya mata batun ko ta fara soyayya ne, "Tom kace masa ina zuwa, eh mun fasa Hidayan ta ce sai gobe zata tafi, duk ma ta damu bata son komawa makarantar"

"Towo ai dama sai da na faɗa karatun naisa ba irin nasu bane, ita mai kwalafucin gida, ace daga shiga level 2 har ta sare, ai shikenan bari inje" ya faɗa

"Tom yaya adawo lafiya" ta faɗa lokacin da ta jawo system ɗin tana ƙoƙarin kashewa, yana fita ta rufe system ɗin ta zari mayafi, a nitse ta fito ji take tamkar ta zura a guje ta ɗora idanin ta kan sa, tuni zuciyarta ta isa harabar gidan tahau kewayon neman inda yake, tana barin falon ta fara duban sa can ɗan nesa da entrance ɗin falon ta hange shi zaune Kasan bishiya bisa kujerar da ke gun, tamkar yasan zumuɗi bai bari ta ɗauko abin zama ba.

Da mugun sauri ta ƙarasa sai dai tana zuwa daf dashi ta tsaya, cikin kala kalar shagwaɓa tace "nayi fushi shine zakayi rashin lafiya baka faɗan ba ko" ta faɗa idanun ta sun kawo ƙwalla.

Murmushi ya yi "banda abin Hafsa ita rashin lafiya ai bata sanarwa, anma amin afuwa"

Murmushi ta yi, " shikenan ya wuce ya jikin gashinan kuwa duk ka faɗa"
Hannu ya miƙa mata "ban wayar ki,"

Ba musu ya miƙa masa Number ɗin sa ya rubuta kafin ya danna kira tasa tayi ƙara, "Number ta kenan ko mun gama karatun wataran ma dinga gaisawa"

"Kaga zumuɗin ban ɗauko abin zama ba duk na ƙagu in ganka,"

"Ashe bani kaɗai ba, sosai na yi missing surutun ki fa"

Ɗan jan hancin ta tayi, fuskar ta ɗauke da murumushin jin daɗi.

Sai yanma lis suka gama karatun ta miƙe "bari in kawo ma kwanon rannan, kaga ko ruwa ban kawo ma bama"

"Karki damu ganin ki da nayi ma ya wadatar" maganar da yayi a zuciya ta faɗo labban sa sauti ya fita, bata ce komai ba ta yi ciki tana murmushi.

Tunda suke karatun yake tattara jarumtar, so yake ya faɗa mata irin son da yake mata ya kasa, ya rasa mai ke damun sa, ya rasa wanne irin kwarjini yarinyar take masa .

Hangar ta da yayi tayo wurin sa da kwano yasa shi faɗaɗa murmushin sa, ta ƙaro tare da miƙa masa, "gashi na gode sosai a gaisar mun da Inna amin godiya wurin ta"

Murmushi ya yi har ya juya, ya kuma juyo tare da cewa "Hafsa," ta juyo haka kurum suka samu kansu da faɗuwar gaba.

Matsowa ya yi kusa da ita gaban sa na ƙara faɗuwa, sam ya naimi abinda ya tsara zai ce mata ya rasa.

"Kinsan tunda nazo nake tsara irin yadda zan miki proposing Soyayya ta, anma kwarjinin ki yasa da na kalle ki sai in manta komai"

Har kanta taji batun nasa, daɗin da taji ya yi yawa, sai dai itama ɗin bata san mai zata ce ba, "kaga na manta ban faɗa ma ba kayan da kasa yau sunma kyau" kallon kansa ya yi tare da yin murmushi.

A gaishe da Inna tace tare da shigewa gida, ya kusa minti ɗaya atsaye kan ya fice yana fita ya durkushe yana haki Finally ya fidda abinda ke ransa, murmushi kawai yake, yana kuma kallon rigar dake jikin sa kalmomin Hafsa suka dawo masa "kayan da kasa yau sunma kyau" murmushi yayi kwarin gwiwa ya kama shi cas ya miƙe tare da nufar titi.

Hafsa na shiga ɗaki ta faɗa gado tana bubbuga kai, takaicin kanta duk ya cika ta, har dare in ta tuna ga dama ta samu ta watsar bata bashi amsa ba, sai ta hau tsaki da bugun kanta, da zarar zuciyar ta ce mata what if ya ɗauka rejecting ɗin sa kikai ba, sai taji kamar ta zane kanta, baccin da ya sace ta dakyar shima cike yake mafarkan Muktar ya dangana ya cire ta a ransa.

************

Tafe suke a mota zuwa filin jirgi inda Hidaya zata koma makaranta, a wurin faka motocin driver ya faka motar, Hidaya ta ɓata rai tare da yin narai narai da ido tamkar zata yi kuka, Hafsa ta ce " Hajiya ki fita mana kin takura mun rakoki kin san ina da abinyi sai ka ce akwai wanda ya miki dole sai kin je nesa karatun"

Hidaya turo baki ta yi cikin shagwaɓa ta ce " Maimakon ma kuyi kuka, haka ma fa Ammi tama ƙi rakono"

" zan fa tura ki waje, a'a to ya zata rakoki lokacin da tace kiyi BUK mai kika ce?" Hafsa ta faɗa.

Tsaki Hidaya ta yi " you are not helping matters " ta faɗa tare da barin motar, sai da ta ɗanyi nisa Hafsa ta fito da ɗan saurin ta, ta rungume ta ,"Zan missing ɗin ki, Allah ya kaiku lafiya."

sun ɗan jima a haka kafin su rabu, kuma sallama sukai kafin tayi ciki ita kuma Hafsa ta koma mota, Malam Musa ya ja su ka ɗau hanya. Wayar ta ɗauko daga aljihun jakar ta, Number ɗin Bilkisu ta hau kira sai dai taƙi shiga Number busy, tsaki ta yi, duban Baba Musa ta yi bata son takura masa sai dai kuma tana matuƙar son ji daga bakin Bilkin.

kai tsaye gidan su Bilkisu tasa ya kaita, a harabar gidan suka haɗu da yaya Ifti, wadda tana ganin Hafsan ta ɗan tsuke fuska, kusan tunda akai abin Bilkisu da Tariq Yaya Ifti ɗin ke jin hsushin Hafsan, Sam bata nuna ta gane tana jin haushin nata ba ta ce " Ya Ifti ina kwana?, tana nan kuwa"

" lafiya ƙalau, ni da ba ɗaki guda muke kwana sannan ba faɗan rayuwar ta take ba ina zan sani"

Hafsa bata ce komai ba ta yi shigewar ta ranta fal cike da jin Haushin Iftin, sam abin na bata haushi yadda Iftin ke wa Bilkisun bacin yadda Bilkisun ta damu da farin cikin ƴan uwan ta.

Falon ba kowa wannan yasa Hafsan yin sama nan ɗakunan ƴan matan gidan yake, kai tsaye ɗakin Bilkisun ta nufa, bugu ɗaya ta ce ta shigo. kwance ta same ta rib da ciki ƙafafun ta sun yi sama waya manne a kunnen ta tana zuba dariya. Murmushi Hafsa ta yi tare da samun wuri ta zauna.

"Hafsa ta zo muyi magana anjima, ok zata ji " Ta faɗa tare da aje wayar ta dubi Hafsa Tariq ne, yace a gaishe ki"

murmushi Hafsa ta yi "ai ba sai kin faɗa ba yadda farin cikin ki ya nuna, nasan shi ɗin ne, ina amsawa, walllahi ganin ki da nayi ya kuma tayar mun da abin da ya kawo ni"

Tashi zaune Bilkisu ta yi "towo mai ya kawo ki, kin san nayi mamakin ganin ki sabida nasan kina da lesson ko an gama?"

Kwafa Hafsa ta yi "uhumm! Wanne gamawa ai abinda ya kawo ni kenan, Bilkisu I am In love"

"Wow! What ke ɗin?" Bilkisu ta faɗa cike da mamaki.

"Eh nidai Hafsan da kika sai, ina son sa sosai walllahi, problem ɗin Mum bata son sa, that's not it only kamar shima bai sona, even though he confessed loving me"

Kallon ta Bilkisu ta yi duk ta faɗa, "Matar nan kin ɗauki soyayya da zafi, but batun Momy ke zaki sa ta so shi, shi mai yasa kika ce baya sonki?"

Numfashi Hafsa ta furzar "tunda ya zo yamin maganar yana sona bai kuma bi ta kaina ba, kuma fa ya fa amshi Number ta, amma ko da wasa bai kira ni ba, he should have chased me at least before given up, ba daga ya faɗa ban bashi amsa ba ya janye is that love?, ni da nake mace kullun sai naji ina son kiran sa, sai in daure at least I have some pride left"

"He might be busy fa, ko kuma wani abu ya samu wayar sa, ko kuma wani abun daban bawai dan baya sonki ba." Bilkisu ta faɗa.

Shiru Hafsa ta yi kafin ta ce "kin tabbata, abinda kika faɗa har ranki?" Hafsa ta fada tana Kallon Bilkisun.

Dariya Bilkisu ta yi "kedai Hafsa na fahinci zafin so ne da ke, ai ba zan faɗa miki what did I not mean."

" Bari kiga to in tafi kar yazo baya nan nassn tas Mum zata ce ace masa an dena lesson ɗin."

Girgiza kai Bilkisu ta yi "yanzu kinsan ba zama zakiyi ba kika wahalar da Driver maine anfanin wayar ki," Bilkisu ta yi complain.

"Wayar taki da bata da anfani na yi ta kiranki, baki ɗaga ba kina can kina soyayya, Hafsa ta faɗa lokacin da ta miƙe kinsan banga Mamin ku ba."

"Batanan tun safe taje Islamiyya sai uku zata dawo," inji Bilkisun.
Chapter 31 · 0% Book details