Sashe 28
Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai wurin Tara suka wuce gida, Usman ɗauke da sauran miyar yace "in yaje gida gobe sai ya tuƙa tuwo yaci" ita kuma Hafsa ɗauke da ledar kayan da ta ɗebo, Sadik sai faman tsokanar su yake sun zama masu fashi wa yar tsohuwa, yayin da Amira ke faman tsokanar.
*********
Kasancewar tun a makaranta jikin Muktar ya yi zafi yasa aka bashi hutun sati, duda bai naima ba, ba laifi hutun ya taimaka sosai, ya ji jiki kusan abubuwa suka haɗe masa ga zafin zazzaɓi ga ciwon son da ya rasa tadda zai dashi kullum tsoro cika masa zuciya yake, yasan shi jarumi ne, sai dai wannan Soyayyar tana ƙoƙarin sawa ya gaza yadda da jarumtar tasa, yana jin tsoro kamar ya taro wa kansa abin da yafi karfin sa ne, in ya tuna da Hafsa da asalin sa yana jin shi akaran kansa yaso kansa, bai kuma kyautawa kan sa ba da ya faɗa soyayyar Hafsa wadda bazai taɓa ganin laifin ta ba in har ta ce bata son sa.
Zaune yake a ƙofar gidan su cikin farar Jallabiyar sa ƙarfin jikin da ya ɗanji sabida Inna ta takura masa ya haɗiɗi tuwon masarar da ta tuka masa da zafin sa yasa ya iya fitowa, duk ya faɗa baka ganin komai a fuskar sa sai dogon hancin sa da dara daran idan sa dama shi ba gwanin ƙiba ba.
Salisu ne ya ƙaraso wurin riƙe da kwano, ganin sa a ƙofar gida yasa shi tsayawa tare sa sakin murmushi, hannu ya bashi suka gaisa bayan ya masa sallama, kwanon ya aje gaban Muktar kafin ya zauna, "Alhamdulillah jiki ya yi kyau walllahi jiya da kai na kwan raina sai da nayi danasanin mai yasa jiya ban zauna na kwana anan ba."
Murmushi Muktar ya yi "kana dai tsoron kar yau a aiko ma na cika," ɗan ƙaramin tsaki Salisu ya yi kaji ka ana zaune ƙalau zaka kawo mana batun mutuwa, kwanon da ya aje ya janyo "kunun kanwa ne, da zafin sa sosai your favorite, ina ganin yau shi Umma ta yi na ce ta zuban na tawo."
Girgiza kai Muktar ya yi "na ƙoshi komai naci Salisu ɗaci yake mun sam ban son cin komai dakyar naci tuwo ma wallahi."
"Ko ba ƙoshi ba?, to walllahi sai ka sha ko darbejiya kake ji, shiru kawai Muktar ya yi ya bude ya hau sha dan yana ɗaya daga ɗabi'ar su duk wanda ya rantse ɗayan kawai haƙura yake ya yi.
Sai da ya ɗan sha zafin kunun yasa ya iya sha da ɗan yawa, sannan ya aje yace kasan "ina ta so in same ka muyi magana kan Hajara da Garba yazo ya samen yace shi ya yadda ta yi karatun ta kawai yana so ya dinga zuwa zance."
Shiru Salisu ya yi kafin yace "ka barshi ya dinga zuwa ɗin, zaifi kan wuri wuri da suke bi dan su haɗu da juna, in a ƙofar gida ne da wuya shaiɗan ya raya musu wani abin fiye da in wuri wurin ne tun ana jin daɗin a haɗu a yi taɗin sai s koma tunanin ayi wani abun tunda ta nace sai ta yi zan ce, ai da sauƙi tunda tana son tayi karatun."
Shiru Muktar ya yi kafin ya ce "eh kuma haka ne, in kayi area ɗin gurin sana'ar tasa ka faɗa masa Please bana jin kwarin jiki na bazan iya zuwa ba."
Murmushi Salisu ya yi "karka ji komai Alhaji langai sarkin raki, ai kai dama badai cuta ta kama ba."
Hararar sa Muktar ya yi yana murmushi, shiru sukai na wasu mintina Muktar na ta faman tattauna a ransa, yana son faɗawa Salisu son da yake wa Hafsa yana son shawara da shi yayin da wata zuciyar ke faɗa masa kar ya ya fada ɗagowar da zai yi Salisu ya riga shi faɗin "bari in koma gida ko karyawa ban ba" ya faɗa tare miƙewa.
Aje tunane tunanen Muktar ya yi yace "ok tom na gode mutumina, sai mun haɗu," har ya ɗan yi taku mai tazara cikin rarraunar murya ta mara lafiya Muktar yace "kwanon shan fa?, daga inda yake Salisu yace in ka shanye na amsa anjima ya faɗa tare da karawa gaba, Muktar ya bishi da ido, kafin ya koma tunanin abar sonsa, salon tsokanar ta, salon murmushin ta komai nata da yake iya tunawa ƙara narkar masa da zuciya yake, kafin damuwa ta biyo baya in ya tuno da tazarar da ke tsakanin su, a hankali ya miƙe tare da ɗaukan kwanon shan ya shige gida, inna na tsakar gida ta ce "kwanon waye?."
Kallon hannun sa ya yi kafin ya ce "Salisu ya kawon kunu kuma na samu na ɗan sha."
Murmushi Inna ta yi "kai amma ya kyauta shine bai shigo mun gaisa ba?"
"Yace bai karya bane, nama ce ya faɗawa Garba ya dinga zuwa zance."
Murmushi Inna ta yi kawai, yasan halin ta ba abinda zata ce ga hukuncin da ya yanke kan ƙannen nasa, bai ce komai ba ya shige ɗaki tare da kwanciya a katifar sa, ya lumshe idanun sa wanda ke faman zayyano masa lokacin da suke zaune a lsnbun su Hafsa suna karatu.
Ganin shiru shirun da Hafsah ta dauka kwana biyu ya damu mommy sosai. Duk yadda ta kada ta raya kuma Hafsah ta nuna mata sam shirunta bai da alaqa da Mukhtar. A zuciyarta taji sanyi amma duk da haka bata jin zata iya barin sa ya cigaba da hulda da Hafsah saboda gudun bacin rana.
Mug din tea da take sha ta ajiye tana hamdala. Shirun gidan ya mata yawa yau saboda bata da niyyar fita ko ina. Hafsah ta kwalawa kira wadda ta fito tana hamma.
Mummy ta kalleta ta tabe baki kadan. Yau hira takeji shiyasa ma ba zatai mita game da yadda Hafsahn take ba.
“Mummy ina kwana.” Ta samu waje ta zauna. Ta kalli TV taga a kashe sannan ta kalli mummy wadda sanye take da wata doguwar riga mara ado sosai. Hannunta kamar ko yaushe dauke yake da zobunan gwal guda biyu da awarwaro uku wanda sai zata kwanta da daddare kawai take cire su.
Yanayin shigar mummyn ya tabbatar mata da yau ba inda zata je.
“Lafiya lau. Kin tashi lafiya?”
Hafsah tayi murmushi. Yau wace rana ba’a fara amsa gaisuwarta da mita ba. Ta gyara zama tana matsawa kusa da mummyn.
“Lafiya lau mummy.”
Suka danyi shiru cike da rashin abun fada don basu saba hira ba haka kawai sai dai in wani abun ne ya tashi.
“Yau ba zaki fita ba?”
Mummy ta gyada kai. “Hutu nake. Gyaran daki na zanyi daga nan inyi tsifa na wanke kai.”
Hafsah ta murmusa. “Toh mummy muje in taya ki gyaran dakin sai in miki tsifar ma.”
“A’a gara dai ki tayani gyaran dakin. Ba ruwanki da gashi na. Haka kawai a yanke min dan abun adon nawa?” Suka kwashe da dariya.
Abu ne da dukkan su basa mantawa. Akwai lokacin da mummy ta taba saka Hafsah da Hidaya suyi mata tsifa lokacin basu kai haka ba. Da yake tana da cika da tsawon gashi sai yasa suka dade sunayi har suka gaji. Hafsah ta kalli Hidaya tayi qasa da murya sosai don kar mummy taji,
“Dama akwai reza mu dan rage tsahon jelar.” Karaf kuwa sai a kunnen mummy wadda ba shiri ta kwace kanta ta hau su da fada. Tsifar da basu karasa ba kenan kuma basu sake ba.
“Mummy an fa dade. Kuma gajiya ce tasa na fada haka.”
Mummy ta girgiza kai. “Ba zan yi wannan gangancin ba. Tunda kika furta, zaki aikata. Ki ja min asara ki jawa babanku.” Suka sake yin dariya wanda tayi daidai da shigowar Sadiq.
Sallama yayi basu ji ba sai da ya sake yi. Ganin rahar da suke ciki ya faranta masa rai sosai har shima sai da ya murmusa.
“Ya Sadiq ina kwana.”
Hafsah ta gaishe shi.
“Ba wannan ba. Hado min shayi.” Mummy ta harare shi. Ya za’ayi mutum ya fito daga gida yazo neman abinci. Sai da Hafsah ta wuce sannan mummy ta amsa gaisuwarsa tana cewa,
“Ina Amirar take?”
Ya sosa keya. Kwana biyu abun nata kara gaba yakeyi don ko kwalliyar jikin ma da take bata lokaci tana yi masa bata yi yanzu. Bar ta dai tayi ta kwanciya tana ta gaji. Abun yaso ya dame shi musamman da yaga in zasu fita tana yin kwalliya iya kwalliya sannan ta ware sosai amma da sun dawo gidan sai ta sauya kamar ya kawo ta makabarta.
Boyayyiyar ajiyar zuciya yayi sannan ya niisa. “Bata jin dadi ne.” Da gaske kuma yau yaji alamar zazzabi a jikinta shiyasa ya danyi share sharen da zaiyi ya barta tayi bacci ta huta sannan ya fito.
Mummy bata wani gamsu ba tace, “Toh Allah ya kara sauki.”
Daidai sannan Hafsah ta shigo dauke da ruwan zafi a flask ta ajiye. Mummy ta kalle ta tace,
“Ki soya masa bread. In yaga dama kar yaci.”
Jin haka yasa ya fasa yin mitar da zaiyi na cewa jagwalgwalo ne Hafsah zata kawo masa kawai. Ganin kallon da mummy take masa ne ma yasa ya fara tunanin ko lefin me ya mata bai sani ba. Yaji kamar ya fasa zancan da ya kawo shi amma ba ya so ya rasa damar yau kasancewar tana raha.
“Mummy tana karatun kuwa?” Ya tambaya da alama yana nufin Hafsah.
“Hnmm gata nan dai ta bi tasa tsanar physics a ranta.” Ta tabe baki.
“Ai na dauka an yi solving wannan issue din.”
Mummy ta girgiza kai. “Yaron ne sam bai yi min ba. Shiyasa na dakatar da shi.”
Sadiq ya gyara murya, an zo wurin. “Me yayi mummy? Bai da kamun kai ne?”
Ta juya kai. “Kawai kasan talaka da jin kan sa. Sam kawai zuciyata bata aminta dashi ba.”
Ya murmusa a boye. “Amma Hafsah tana gane karatun sa?”
“Eh da alama. Shiyasa ma nake tsoron tasirin sa akanta.”
Sadiq yasan inda zancen yake. Yaga babu amfanin yiwa mummy kwana amma kuma don dai ya karkatar da tunanin ta zai gwada.