Sashe 41
Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kujerar da Mum ke zaune Khalil ya zauna tare da faɗin "Hajiya Mum wai yaushe kika canja hali?" Harar sa ta yi kai Ibrahim banson iskancin banza fa, kazo ka kori yaro muna nishaɗi shine zaka tsare ji da ido wato zaka ƙureni?"
"Opps Mum Iskanci fa naji kin anbata, ɗazu ma naji kina aibata Faruk anya kuwa Mum, mu yaran yanzu ba akiramu da sunan banza bama tarbiyar mu sai addu'a ina ga kuma kakarmu duk ta tsine mana". Shiru ta yi da alamu ta tuna bata kyauta ba.
"Yanzu dan Allah Mun dai dai kike fisabilillahi ki kalli yanda kika sa su Faruk duk suka rakaɓe, in basu sake a gidaj nan ba ina zasu sake, abinda kike fa zai iya ja musu psychological problem fa"
Taɓe baki tayi Uban su ya ja musu, wallahi duk na tsane su, dan tsabar rashin mutunci in bashi ɗiyar tawa ita kaɗai ya haɗota da gayya ince a mayar masa ace ni zan riƙe"
Dariya Khalil ya yi "a'a dai Mum Abba ne zai riƙe, sannan ita zatayi tarbiyyar ta, ke sai dai ki taya ta"
Tsaki taja "Ai walllahi Muktar ya cucen, yanzu da wannan uban gayyar waye ma zai tunanin auren ta fisabilillahi."
Shiru Kalil ya yi dan maganganun sun fara wuce tunanin shekarun sa kome ya tuna kuma sai ya ce " yo banda abin Mum ai matar mutun kabarin sa wanda zai aure ta ko yara nawa ne zai aure ta, kuma ba lokacin sai a mayar da su ɗin ba, ko a bawa Momin ta riƙe."
"Abawa me kace?, Ai mayar su zan tana samun miji suje can su ƙarata ganin su ma hawan ji ni zai samun wallahi" ta faɗa rai a cinkushe.
Shiru Khalil ya yi kafin ya ce " nidai dan Allah Mum ki gyara ko dan kar su taso da tsanar ki a ransu kefa kaka ce ta wurin uwa dan Allah"
Fuskar ta a ɗan ɓace tace shikenan dai in na kallesu banji haushi ba, I won't react anma indai na tuna da Azzalumin ubansu to.."
"Please Mum koma me kika tuna kawai ki daure kinji" Khalil ya roƙa.
Banza ta masa tare da rufe idanun ta, ya miƙe bari kiga kome na samu ya zama nawa, da sauri ta buɗe ido " karka sake ka ɗaukar mun komai"
*********
Kwanci tashi iddar Hafsa ta ƙare sam ta aje Muktar a rayuwar ta, ta yi kyau har ta ciko, duda can ƙasan ranta tana jin sa sai dai ta riga ta sa aranta takardar sakin auren da ta watsar shine ta watsar yadda ba abinda ya same ta lokacin da ta watsar tana jin zata rayu ko ba shi.
Tsaf ta shirya cikin doguwar rigar ta milk da ta sha adon Golden ta yo kyau sosai ga kitso da aka mata jiya ya ƙarawa fuskarta kyau, ba zaka kalle ta kace ta haifi Kursum ba, bare kuma Abdallah ko yayan sa Faruk.
Yaran basa nan suna farfajiya wurin Malamin da ke musu Lesson weekend, ɗakin Mum ta nufa, Mum ɗin na zaune tana hutawa ta shiga, "Mum sannu da gida," Hafsan tace.
Ba yabo ba Fallasa Mum tace "yawwa sannu" dan ta rage yi mata hayaniya yanzu da alamu zuciyar ta yanzu ta fara sanyi kan zafin da ta ɗauka.
"Yawwa zani gidan Bilkisu ne, kan batun admission ɗin da mukai Tariq zai nemo min," da yake Mum gwanar son yaran ta su ci gaba ce jin batin ci gaba da karatu wanda ada tayi tayi Hafsa ta yadda taƙi sai ta saki murmushi, "Tom sai kin dawo, duk a gaggaishe su"
Tana fita Harabar gidan Aiman ya taso da gudu shi sai bita, cikin dabara tace, "kasan dai kwanaki nayi rashin lafiya ko, to likita yace kar in dinga yawo da yara"
Kallon ta ya yi fuskar nan cike da disappointment, kafin yace " shikenan adawo lafiya in kin ji sauƙi sai in dinga binki ko?"
Gyaɗa kai ta yi alamr eh, ya koma salalo salalo zuwa inda suke karatun, yayin da Hafsa ta yi sauri ta fice kar ya canja shawara tasan halin sa da wayo da ya yi tunanin ba haka bane zai ce sai ya je, kamar kuwa yadda ta zata, har ya kusa sai ya tsaya cak da sauri ya juyo, ganin bata nan yasa shi yin kwafa ya koma ya zauna.
Kasancewar a ɗan sahu ta je yasa ta tsaya bakin ƙofar tana bugawa, tsayawar motar Tariq a ƙofar gidan yasa ta dena bugawa, fitowa ya yi yana murmushi "a'a Mamin yara kece da yamma haka, murmushi ta yi wanda ya ƙara mata kyau, da sauri Tariq ya ɗauke kansa sabida wani abu da ya jima da yaƙar sa da yaji ya taso masa, yayin da Hafsa tace kabari kawai ai wai nan so nake in same ka ne shi yasa.
Makullin gidan yasa ya buɗe, yana faɗin "inajin ko sun aiki Musan, tunsa kika buga bai buɗe ba,"
Bata ce komai ba ta shige ciki, yayin da ya koma dan shigo da motar sa, Yaran suna Falo malamar su na musu ƙari kasancewar yaran Bilkisu duk mata, suna ganin Hafsa suka fara murna, cike da murna suka gaidata, Chocolates ɗin da ta kawo musu ta rarraba musu, kafin ta wuce ɗakin Bilkisu, a kwance ta same ta tana bacci, haka kawai rayuwar yarinya ta dawo mata, hannu tasa ta ɗakawa Bilkisun duka tana dariya.
Firgigit Bilkisun ta farka ganin ta yasa ta miƙewa tana dariya, " kefa Mami wallahi bakya girma nasan burin ki in miƙe in biyo ki da gudu ko," dariya Hafaa tasa wallahi kamar kin san haka suka sa dariya duka...
*Muka ce ba, muma dai bari mubi trend ɗin paid book, mu samu mu mori arzikin duniyar ributu, dan Allah Allah ku bamu kunya*
Dariyar da sukayi ta saka su tuno da. Nan suka buɗo shafin yarintar su kafin suyi aure sukayi ta daarawa har sai da sukayi me isarsu. Kamar ba su ba sai shiru ya ratsa a tsakaninsu. Hafsah tayi ajiyar zuciyar da ya zame mata dabi'a duk da zahiri ta bar Mukhtar, ta kuma jingine shi gefe, duk sanda wani abun ya kawo zancen sa sai taji zuciyarta tayi nauyi.
Bilkisu ta zuba mata ido tana jiran abunda zata ce. Hafsah ta kauda kai gefe saboda bata san ta inda zata fara ba, karshe dai ta zabi abun cewa.
"Nazo neman alfarma ne..." ta faɗa cikin sigar tsokana wadda Bilkisun bata lura ba sai dai nutsuwar da ta karayi tana jin cewa ko me Hafsah zata nema a wajenta zata iya yi mata komai wahalar sa.
Hafsahn ta sunkunyar da kai, "dama na yanke shawarar komawa karatun shine nace dan Allah ko Tariq zai nemo min admission..."
Wani kallo da Bilkisu ta watsa mata sai da yasa Hafsahn ta saki dariyar da take riƙewa ita kuwa Bilkisun ta ƙule sosai ta tashi gami da yin tsaki.
"Wallahi kin mugun raina ni. Mtsww dallah matsa." Da haka ta fice a ɗakin Hafsah tabi bayanta sukai kitchen inda ta fara zuba musu abinci.
"Ba don halinki ba dai." Bilkisun ta faɗi yayin da suka zauna.
"Ko don halin nawa ma nasan zaki yi min alfarma..." harara Bilkisun ta sake yi mata saboda kalmar alfarma da Hafsah take ambato tana mugun bata mata rai.
"Allah ya baki haƙuri me gadon zinare!"
Murmushi sukayi.
Tariq da ya shigo da motar sane ya yo ɓangaren Bilkisun samun yaran suna karatu yasa shi yin ɗakin matar tasa, daga baki ƙofar kitchen ɗin ya tsaya, yana kallon su, yadda suke cikin nishaɗi sai suka birgeshi, zuciyar da ke ingiza shi ya yi abinda ba haka ba yasa shi yin saurin barin wurin.
*****
Juyi yake tayi akan gadon don tunda yayi asuba ya kasa komawa bacci, idanunsa suka kumbura. Haka ya wuni daga masallaci sai ɗaki. Ya rasa me yake masa dadi a duniya gaba ɗaya. A yan kwanakin nan duk ya rame ya yi duhu musamman ma in ya tuna cewar Hafsah ta gama idda. Tunanin yana saka shi jin kamar yayi ihu don yana tuna masa da cewa yanzu ba matar sa bace haka zalika kuma ko wanne namiji zai iya aurenta. Idan wannan ya faɗo masa a rai sai yaji kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu. Ba don imani ba sai yace duk sallah sai yayi addu'ar kar ta samu miji.
A gefe guda kuma kewar yaransa tana nuƙurƙusar mishi ƙasusuwa ga kunyar iyayen Hafsah tunda har yau bai waiwayi gidan ba kuma babu wanda ya nemi zuwansa. Ba Mummy ba Abba. Ya rasa ta inda zai bullowa lamarin ya samu sa'ida.
Ko da yajewa da Inna zancen ta je ta amso masa yaran sa cewa tayi babu ruwanta. Hajara kuma ta ce bata da lokaci. So yake ko yaya yaga yaran. A wani bangaren na zuciyarsa ma yana son ganin Hafsah yaga ya ta koma.
Ƙarshe dai yaga gara yaje ya sami Rashida ta bashi shawarar da ta dace. Duk da yasan yanayin tunaninta sai a hankali amma ko meye zata faɗa masa yasan zai bashi mafita in ya haɗa da nasa tunanin.
Haka ya tashi ya shirya ya nufi gidan. Cikin mintuna kaɗan ya isa gidan. Gidane ginin zamani, madaidaici. Kana ganin gidan kasan akwai rufin asiri. Ya jima a motar kafin ya fito.
Ko da ya shiga ya tsaya a kofar part ɗin Rashidan sai da ya shafe mintuna kafin ta fito da kasko a hannunsa. A take wani wari ya daki hancinsa ya kalle ta cike da mamaki.
"Wani irin turare ne wannan Rashida?" Mukhtar ya tambaya.
Rashidan ta taɓe baki. "Laaa yaya ban san kaine ba ai. Na dauka yan adawa ne..., Tsari ne na kaɓo a can wani kauye. Kasan yadda zamani ya chanja gashi ana nufar mutum da sharri shiyasa gara ya tsare kansa ko da an mishi barbade barbade ba zai kama shi ba."
Da kyar Mukhtar ya fahimci inda ta dosa da yaga tana magana tana leka ɗayan part din da abokiyar zaman ta take. Ya girgiza kai ya bi bayanta suka shiga falo. Rashida ta dena bashi mamaki sam sai dai kawai ya bita da addua. Murnar da yake yi ma da ya kasance yaranta kaf basui halinta ba.