← Book details Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 43

Sashe 17

Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya ta yi bayan ta ture kwanon yau kwanana uku, ina zuwa kai na fara tambaya ai Gwaggon ta ce baka nan" guri ya samu ya zauna gefen Hafsan bari kawai munje seminar ne yau ɗinma dakyar suka sallame mu."

Bari in zubo ma abinci ta faɗa tare da miƙewa Halima ya kalla, tare da cewa mutun sarkin ƙiwa yanzu da ke ce ko na roka da mita za'a zubo"

Dariya ta yi itama na ɗoki ne waye zai ɗauki hidimar ka, kullum kai dai kace ayi, harar ta ya yi kafin ya ce in kin gama rubutun ki sarrafa mana kifin nan.

Gwaggo ce ta ce ita da take rubutu Bebilon ta yi dafa mana, a hankali ya ce tab ina Hafsa ina girki kema kinsan Aunty Hadiza ba lallai tana bari Hafsa ta yi komai a gida ba.

Hafsa da ta ƙaraso ce dauke da kwanon abinci da kofin ruwa ta aje masa, tare da ɗaukan ledar kifin aikam naji ka wato ban iya komai ba kake nufi, ta fada da ɗan tsuke fuska.

Dariya ya yi ah haba "ni na isa ince baki iya ba, kawai banso ki wahala girki a kurfoti ba sauƙi, ki ajiye Halima ta dafa kinji Bebilon Malam," yar harar wasa ta watsa masa "ai fa ba zakamin wayo ba girki na yau dole zaka ci gidan nan"

Gwaggo ce ta sa dariya "Dan Allah ka barta gwamma ta girka yau ɗinnan Malam yaci ƙarni ya ishe shi ya canja shawara"

Yiri ri! Hafsa ta ɗanyi dariya gami da shewa aikam Gwaggo ki fara haɗa kayan ki dan cewa zai bai sanki ba sabida daɗin girki na" ta faɗa tana shafawa kifin lemon tsamin da ta yanka, yayin da takaici ya ishi Zahraddeen tunanin asarar kuɗin kifin sa kawai yake ji yake tam kar yaje ya make Halima wadda taƙi zuwa ta amshi kifin hannun Hafsa.

Kiran sallar la'asar da akayi yasa shi fita bayan ya yi alwala, tare suka shigo da uncle Mansur yaya ne ga Zahraddeen shi yake bin Umman su Hafsa tuni ya yi aure sai dai baya kwana uku bai zo gidan ba.

Tun daga zaure uncle Mansur ya ce a'ah yau girkin ƴan gayu ake haka a gidan kamshin da ya daki hancin su ya sa ya faɗi, Hafsa da ke juya miya ta saki murmushi, ai yau girkin nan ko ta fada tare da ɗan yin karamar kwafa.

Gwaggo ce tace ai dai abari aci tukunna ba ƙamshin ba ɗan ɗanon suks sa dariya, hira suke sosai kafin Uncle Mansur ya tashi zai tafi dakyar Hafsa ta roƙe shi yace zaije ya dawo ya ci.

Kamar yadda al'adar gidan take tabarma suka baje a madai daicin tsakar gidan can gefen taga fitilar ƴar sola irin wadda yara ke haɗawa suna siyarwa ce ta haske tsakar gidan ya yin da Hafsa ta ɗauko food flasks ɗin da ta juye abincin ta ajiye gaban Gwaggo.

Kallon ta Gwaggon ta yi "mai zan da shi?" Ta tambaya

Murmushi Hafsa ta yi "zubawa"

Halima ta kalla " ki aje wannan karatun kizo ki zuba, dan kin yi sa'a yau an ɗauke miki girkin shine wato komai sai dai ayi?"

"Anma Gwaggo nida bani na yi aikin ba ai ban san kan sa ba"

Zahraddeen ne cikin kufula ya ce "zaki zuba ko sai na make ki?"

Tana ƙunƙuni tana zubawa ta miƙawa kowa, tunda aka miƙawa Zahraddeen Hafsa ke kallon sa so take taji mai zaice, sam bai kula da yadda take kallon sa ba, ya nutsu yana cin abincin sosai ya masa daɗi bai ta ɓa tunanin yarinyar ta iya girka ba bare ts sarrafa kifi ya zama ba ƙarni.

Ganin bazai magana ba ta ce "Uncle baka ce komai ba?

Tsotse ƙayar hannun sa ya yi kafin ya ce " eh to abinci dai gashi nan kamar dusa dusa"

Dariya tasa "ai da dusar ne da farantin nan naka bai zama ba komai kai ba"

Kallon farantin ya yi sai kuma yasa dariya dan baima san ya cinye ba, Malam ne ya ce ai wannan abincin ko a otel albarka"

Gwaggo da take suɗe hannu ne tace "a'ah dai Malam kawai kana tsoron tane" suka sa dariya duka.

Kwanakin da Hafsah tayi a gidan Goggo ya saka ta ji daman irin rayuwar da suke yi kenan a gida. Rayuwa ce cikin aminci da kula da juna da bawa kowa muhimmanci. Duk da in aka saka mutum a gaba da fada akan wani abu sai yaji kamar ya gudu, ita dai gidan Goggon yafi mata dadi.

Zaune take tana taya Goggo linkin kaya ta lura Goggon tayi nisa a tunani. Ta kura mata ido sannan tace,

“Tsohuwa ana tunanin mutuwa ne?” Goggon ta murmusa ta kalle ta.

“Ba dole ba. Kowa matafiyi ne.” Sai Goggon ta goge hawayen da ya taho mata wanda yasa jikin Hafsah yayi sanyi. Shiru suka yi na dan lokaci kafin Hafsahn tayi magana.

“Goggo kin iya wainar gero?”

Goggon ta kalleta da mamaki. “Wainar gero kuma bebilo?”

Ta gyada kai. “Da ma wasu abincin gargajiyar. So nake na koya.”

Goggo taji dadi ganin jikarta ta ta soma wayo da sanin kanta. A iya sanin ta in dai ba so take ta burge mutane ba ko ta nuna ta iya, Hafsah bata kaunar girki. Kai, ko wanne aiki ma ba son shi take yi ba indai ba ra’ayin kanta bane.

“Sai mu fara ai. Dama na kwan biyu banyi ba. Yau sai muyi tuwon dawa amma ki shirya daukar mitar mutan gidan nan. Don ba ruwana.”

Hafsah ta saka dariyar da yasa Goggo tayi shiru tana kallonta cike da nazarurruka barkatai akanta. Duk da rabin su alan mahaifiyarta ne ba ita Hafsahn ba.

****

Tana kwance tana duba hotunan wasu dogayen riguna ne kiran Bilkisu ya shigo wayarta. Rabon da suyi waya ma ta manta kuma ita ma bata lura ba saboda yanayin zaman gidan Goggon. Ko yaushe da akwai abun yi ko kuma abokin hira.

“Hnmm.” Kawai tace da ta kara wayar a kunne.

“Ke an sa result.” Gaban Bilkisu ya fadi. Ta mike zaune.

“Innalillahi, yaushe?”

“Yau dinnan yanzu ake gaya min. Zaki iya zuwa ki dubo mana?” Hafsah ta daga labulen dakin ta leka taga yadda hadari ya hado sosai. Ajiyar zuciyar fargaba tayi sannan tace,

“Hadari ne a garin. Ki zauna kar asthma dinki ta tashi. Bari na kira Ya Usman.”

Da haka sukayi sallama Hafsah tana ta tunanin yadda zatayi. Dole sai dai suje su duba don ita bata so wani ya gano mata. Ta jima a zaune tana tunanin Yaya Usman zata fadawa ko Abba.

Shigowar Goggo ya sa ta daina zarya a dakin.

“Goggo an saka mana sakamakon jarrabawa. Don Allah ki min addua.” Ta fada idanunta cike da hawaye. Goggon ta kamo hannayenta suka zauna gefen gado sannan tace.

“Ki kwantar da hankalinki. Nasan kwanya ta kika yi. Zaki wuce dukka da sakamako me kyau. Oh jini ba abun wasa ba. Mamanku ma haka take yi duk sanda aka yi jarabawa.”

Hafsah ta lankwasa kai tace, “ke kam Goggo kun huta. Ba kuyi boko ba kuma ba wanda zai kalle ku ya muku gorin haka.”

Goggon ta yi murmushi me sauti. “Nayi firamare ai kafin a min aure. Lokacin ai mune manyan matan gari.”

Sukayi dariya kafin Hafsah ta mike ta kira Abba wanda ya tura mata dreba suje su dubo. Hankalinta yafi kwanciya ta kira shi don ko shi yace zai je ya duba mata yaga da matsala ba zaiyi mata fada ba sai dai ya bata shawarwari akan yadda zata maida hankali. Yaya Usman kuwa suna dawowa mummy zai gayawa wadda zata saka ta gaba tayi ta mata fada kan cewa babu abunda ta sani sai aikin bacci da fita yawo da kawaye. Sannan kuma har Yaya Farida ma sai ta san bata yi kokari ba.

****

Fitowar Mukhtar kenan daga wanka yaji maganganun mutane daga soro. Da sauri ya ajiye bokitin hannunsa ya shige daki sannan ya karo kofar. Baya son yadda mutane suka maida musu gida kamar titi. Ko wacce mace ta figo daga makota sai ta fado musu gida kanta tsaye saboda kusan kullum a bude take. Yasan hakan yana da alaka da sana’ar da Inna ta na yi. Zai
so ace ya bunkasa mata sana’ar ta yadda ba sai ana shigo musu gida kasafai ba. in Allah ya yarda da zarar kudi sun zauna masa shago zai kamawa Inna a bakin kasuwa sai ta dauki hayar yaran da zasu dinga zama suna sayar mata da abincin. Amma yawan yadda ake shigo musu gida yana bata masa rai.

Da sauri ya goge jikinsa sannan ya shafa mai saboda jin kiran Inna da yayi alamar tare suka shigo da bakuwar.

“Gani nan zuwa Inna.” Ya fada yana mikewa daga kan katifar shi sannan ya daga labule ya fito.

Idonsa alan Inna Ladi ya sauka saboda haka ya daure fuska sannan ya saka silifas dinsa yana karasowa inda suke. Sai da ya durkusa sannan ya gaishe ta.

“Muntari kenan, ashe ka samu aiki.” Ta fada, da alamar tana neman dalilin yin wata maganar. Mikewa tsaye yayi sannan yace, “eh alhamdulillah. Inna na fita, zan leka islamiyya.”

Da sauri ya fice ba tare da ya jira amsar su ba.

****

Ta dade bata ga nisan zuwa makarantar ba kamar yau. Tafiya suke yi amma kamar basa sauri take gani gashi kuma ko kuzarin ce masa ya kara sauri bata da shi. Sosai take tunanin makomarta har tana mamakin yadda akayi ta damu din. Sanda tana sakandire sam bata damuwa saboda yanayin karatun ya bambanta. Da ta shigo jami’a sai komai ya zamar mata sabo. Gashi dai duk karatu ne amma wani iri take jin shi. Ga yawan mutane a ajin.

Kallon bishiyu da gidajen hanyar take tayi tayi tagumi har suka isa cikin makarantar. Ko da suka dauki kwanar agriculture sai da gabanta ya sake faduwa, cikinta ya daure. Jikin ta sam babu wani kwari ta sauko daga motar sannan ta nufa inda ake saka notice board din.
Chapter 17 · 0% Book details