Sashe 42
Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mamakin yadda akayi Nura bai taɓa sakinta ba yake yi duk da kuwa halayenta marasa kyau ne. Nura yana son Rashida nesa ba kusa ba kuma yana kula da ita daidai iyawarsa tun bashi dashi. Duk sanda tayi yaji kuma da kanshi zai zo yayi biko har ma ya fadawa Mukhtar ya saka baki.
Shi gashi yana zaune da Hafsah lafiya kalau wani abun ya saka ya rabu da ita. Kenan shi ba son ta yake yi ba da gaske? Ko dai shi kawai rago ne? Ko jarumtakar kenan? Ya rasa amsar tambayarsa ya kalli Rashida da take shigowa da lemo a tray.
Ta ajiye sannan ta taɓe baki. "Sai haƙuri yaya. Tsiyar Nura ba zata bari ya saya mana lemon kwali ba sai na roba."
Mukhtar yace, "kamar yaya kenan. Wai ke Rashida yaushe zakiy hankali? Mijinki kike kiran sunansa gatsal haka?"
Tayi tafi harda shewa. "Hankali na nawa kuma? Don nace Nura? Ai Nawwara ya kamata na kira shi dashi. Namiji ne amma ba zuciyar maza! Kullum a babu. Ko da ya fara samu kuma aka makala masa waccan banzar me kama da biri. Ni abun kunya ne ma ace ina kishi da kamar ta."
Mukhtar ya rasa abun cewa sai kawai ya dauke kai. Ko yaushe a cikin kure shi take yi. In da sabo yaci ya saba.
Hakan ya tuna masa da Hafsahn sa. Mace me tarbiyya da iya kula da miji. Zata tsokane shi kamar kakanta amma kuma umarnin sa ko yaushe bata sabawa. Idan magana yake mata me muhimmanci tsayawa take ta saurara ta bashi amsar da ya dace. Idan lefi tayi cikin lumana zata gaya masa ba zata sake ba. Kusan komai nata ya cika goma amma da yake dan Adam ace sai ya zama bata cikan ba, tara take. Ko a zuciyar Mukhtar ma abu daya ne ya hanata cika goma a zuciyarsa.
Abun da ya zamo silar sakin ta.
Ko ita Hafsahn baya jin ta sani kuma ba zai iya sanar da ita ba. Ba zai iya sanar da kowa ba saboda ko shi kanshi in ya tuna dalilin sai yaga kamar sakin ba shine maslaha ba.
Mukhtar ya kai mintuna biyar yana tauna maganar da yazo da ita kafin ya kalli Rashida wadda take danna wayarta yace,
"Na saki Ummu Abdallah..."
Kalaman sa suka saka shi jin wani ɗaci a harshen sa saboda tamkar dafi suke. Zuciyarsa ta tsinke kamar ko yaushe idan ya tuna abunda yayi musu ɗin.
"Ban gane ba?" Abun yazo mata a bazata. Kuma ta kwana biyu bata leƙa gidan ba.
Ya rike kansa don ba zai iya maimaita wannan kalaman masu dafi ba.
"Ta gama idda ma." Sai yaji wannan din ma sunfi yi masa zafi.
Rashida ta fara salati tana sallalami cike da al'ajabi. Yanzu ashe Mukhtar zai iya rabuwa da Hafsah? A take kwakwalwarta ta ayyano mata cewar Nura zai iya rabuwa da ita kenan. Jikinta yayi sanyi duk da ba wani son Hafsahn take ba. Haka ta jingina da kujerar hadi da jefar da wayar hannunta. Ashe haka maza suke?
"Shawara nazo ki bani tsakani da Allah. Yaran suna wajen ta kuma tun da ta tafi ban je wajen su ba. Ya dace naje ganinsu?"
Bakin Rashida ya mutu murus. Da kyar ta haɗiyi yawu tace,
"Ikon Allah. Gaskiya baka kyauta ba. Kana nufin iyayenta ne zasu kular maka da su ko me? In ba zaka iya zuwa gidan ba ai kasan makarantar da suke. Kaje ka gansu salin alin kafin kayi tunanin mafita don ni kaina a kulle yake. Tabb..."
Aka dan jima bai ce komai ba.
"Tabb." Rashida ta sake maimaitawa sannan ta mike don gaba ɗaya ya jagula mata lisaafi. Dama kwana biyu taga Nura yana mata wani gani gani. Ai kuwa ba zata bari ya sake ta ta tashi a tutar babu ba. Dole ma tasan abun yi kafin ya shammace ta.
"Hnmm unmm..." ta faɗi sannan ta mike.
"Ka gaida gida." Ta shige ɗaki ta kullo kofar.
Ko kaɗan Mukhtar baiji komai ba ya tashi ya tafi.
*****
Sai yamma lis Hafsah tazo tafiya da yake bata zo da mota ba, ɗaki Bilkisu ta shige tana faɗin ina zuwa, Tariq na zaune yana taɓa waya ta shiga, yana ganin ta ya buɗe hannu alamun tazo ta shiga, ta maƙe kai, "kajika Hafsa na waje tana jira na kasan bata son jira" murmushi ya yi "nikam dai ba'a kyautamun ba, bakiji yadda nake missing ɗin ki ba walllahi" Dariya ta yi "nidai yanzu taimakawa zakai kazo ka kaita, bata zo da mota ba" miƙewa yayi an "gama tawan" sai da ya zo daf da ita ya jawo ta jikin sa, suka sa dariya duka, kaiko na faɗa ka jira take sai da ya manna mata Kiss a goshi sannan ya fice ta bi bayan sa. Hafsa da ya ɗora idanun sa kan Fuskar ta yada shi jin wani iri, rage dariyar yayi kafin yace "Madam munbar ki kina ta jira ko?"
Murmushi Hafsa ta yi, "ai indai kune na saba jira."
Duk yadda Hafsah tazo zillewa don kar ta shiga motarsa sai da Bilkisu ta kureta. Gudun ɓacin rai yasa ta yarda ya kaita din.
Sunyi sallama har ta shiga motar sun fito. Banda AC da takeyi baka jin sautin komai. Gaba ɗayan su ba wanda ya sake a motar. Ita Hafsah tana ganin rashin dacewar shiga motar wani daga shi sai ita shi kuwa yayi nisa a tunani yana yi yana satar kallonta wanda tunda ta shigo idonta yana ga window.
Tariq ya gyara murya sannan yace,
"Ya yaran?"
Idon Hafsah akan window ɗin ta murmusa. Indai kana son ganin farincikin ta ka tambayi lafiyar yaranta.
Murmushin nata ya taɓa shi, a hankali yace ya rabb, yayin da Hafsa ta ce "Lafiya ƙalau."
Suka sake yin shiru. Tariq ya rasa abun cewa, duda yadda yake son suyi magana ɗin, sai dai ya kasa wannan yasa kawai ya kunna rediyo. Waƙar indiya ta shigo wadda a take tasa Hafsah ɓata rai. Ta juyo da rauni a fuskarta. Karaf suka haɗa ido. Gaban Tariq ya faɗi, bai yi tubanin zata juyo ba, wannan yasa idanun sa duk sakanni in ya kalli Titi yake dawo da su kanta.
"Don Allah ka kashe?" Kamar ma tambayarsa take. Tariq ya kashe sannan yace "mai yasa, ba daɗi ne?" ya tambaye ta dalili.
"No It reminds me of him. Baya son waƙar indiya amma yana son wannan kuma yana rera min." Ta juya kanta tana tausasa zuciyar ta akan son Mukhtar da ya manne mata. Ta nemo dukkan dalilin da zaisa ta tsane shi ta sakawa ranta sannan hawayen suka koma. Ta bar shi har abada amma son shi? Bata jin zai barta.
Shiru Tariq ya yi kafin kuma ya ce "Kyanta kiyi taji har sai ta dena tuna miki dashi. Sometimes we have to help ourselves go over someone."
Ta gyaɗa kai. "Na sani nima so nake na manta shi a zuciya. I'm done with him amma zuciyata is obsessed. Karatu ma zan koma..."
Jin haka yasa Tariq yaji dadi sosai, yayin da tunani iri iri ya mamaye masa rai.
"An zo fa.." ta fada da dan dariya sannan ya faka motar shima yana dariya.
"Zan faɗawa Bilkisu tayi ma a hankali. Ta sace zuciyarka da yawa a waje ma tunaninta kake. Nagode." Bata jira amsar sa ba ta buɗe motar ta fice.
Ya bi bayanta da kallo, son ta yana sake sabunta a cikin ransa. Lokaci yayi da zai sanar da ita, ba zai iya yin kasadar barin taba kamar yadda ya yi abaya, dole tasa ce Hafsa, yanaji aransa sabida hakane ma ƙaddara ta rabota da gidan ta dan ta zama tasa, amma kafin nan yana bukatar amincewar Bilkisu. Zai yi istikhara sannan ya fada mata, duda bai san ta inda zai fara ba, anma tsananin son Hafsa aransa na bashi ƙwarin gwiwa, tsoron rasa ta a karo na biyu na sanya masa jarumta, dolema zai faɗawa Bilkisu da wannan tunanin yaja motar sa ya bar ƙofar gidan su Hafsa....
*********”
Lokaci wani halitta ne da tunda aka hallice shi yake gudu. Baya sauri dan wani, haka kuma baya jiran kowa. Dukkan wani numfashi da dan Adam yake shaqa tafiya yake da lokacin da aka dibar masa a duniya. Haka lokaci ya cigaba da tafiya, rayuwar Hafsah tana sake alkibila. Kamar wasa har ta samu gurbin karatu a jami'ar bayero ta cigaba da karatun da tace ta gama.
Sai dai ita duniya babu tabbas, zaka iya gama tsarin ka kuma ta sauya maka shi.
Zaune suke a ajin suna jiran shigowar malami wata yar ajinsu wadda suka fi jituwa da Hafsah ta kalle ta taga tayi nisa a tunani.
"Umm Abdallah lafiya kuwa?"
Hafsah tayi ajiyar zuciya. Babu abunda yake mata ciwo sama da yadda mummy tasa yaranta a gaba kuma tace kwana uku ta bawa Hafsah ta kira Mukhtar ya kwashi yaran. Tana kallo yadda duk auka takura musamman ma Abdallahn da duk yafi su hankali. Kullum in zata leka su zata ganshi idonsa biyu yana sallah. Da ta tambaye shi me yake nema a wajen Allah sai yace mata bakomai kawai yana mata addu'a ne. Tasan shi da zurfin ciki da son nuna kalau yake.
"Ciwon kai ne yake damuna yau. Kamar ma ba zan iya zaman lecture din nan ba, tafiya zanyi." Ta fara hada littafanta tana saka su a jaka. Zuciyarta cike fam da tunani tana neman mafita. Babu wanda zata yi shawara dashi sama da Yaya Sadiq ko aunty Ameera. A take ta yanke shawarar zuwa gidan nasu.
"Toh Allah ya sauwaqe." Amin Hafsah tace sannan suka yi sallama ta tafi.
Fitowarta daga ajin yayi daidai da lokacin da lecturer din ya iso tare da abokinsa. Dr Karaye. Ba tare da izininsa ba idanunsa suka sauka kan Hafsah. Da yake kuma daliban basu da yawa, lecturer din su Hafsah duk ya san su. Ganin yadda Karaye ya kalleta ya saka shi yin magana.
"Malama Hafsah ina zuwa?"