Sashe 3
Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kaji dai shirin Muda likita nake son ji, ta yau ƴan siyasa sun siye filin shine nake saurara, ya aikin kuma fatan an dace.,?" Iska ya ɗan furzar "to gashi nan dai sunce zuwa dare zasu turo mana sako," ya faɗa jiki ba kwari.
"To Ai shikenan, ai mutun baya wuce ƙaddarar sa in ba'a dace ba sai mu cigaba da jarrabawa" Umman ta faɗa ga. Shiru kawai sukai kowa da abin da ke zarya a ransa yayin da sautin Radio ke ta shi a tsakar gidan.
***********
Sam Hafsa ta gaji da ajin na farko ba son Physics take ba sabida bata ganewa, na biyu malamin da ke koya musun yada ya wani haɗe rai yasa duk haushi ya cikata, ga kuma haushin kanta da take ji tun ɗazu da take tawowa idanun ta sun gaza goge mata hoton mutumin ɗazun ita a yanzu ba zata iya faɗin asalin mai take tunani akan sa ba.
Kamar jira take Malamin ya fi ce zumbur ta miƙe, riko tan da ta ji an yi yasa ta juyowa Bilki su ce, tare sukai secondry school yanzu kuma suke aji guda a Jami'a, "Hajiya ina zuwa haka cikin gaggawa Bilkisun ta tambaya tana kallon ta.?"
Ɗan wawwaigawa Hafsa ta yi taso mu tafi kar" yamma ta yi," dariya Bilkisun ta yi "wato da ace ban ruƙo ki ba kina nufin tafiya zakiyi ki barni ko me.?"
Dariya Hafsa ta yi "no da ba tafiya zan ba kawai zan ɗan fita ne in shaƙi fresh iska,"
"ok jeki ki shaƙa bari in nuna ma Ummi wannan abun"
"ok" kawai Hafsa ta ce har ta kusa bakin ƙofa ta ce "dan Allah karki barni ina ta jira waya ta babu caji nasan da Abba yaga biyar ta yi tunda na ce masa four ne zai ta kira in bai same ni ba hankalin sa zai ta shi."
Tana tsaye jikin karfen benen tana bin bishiyun gun da kallo tare da tsuntsayen da ke kai kawo daga wannan bishiya zuwa waccan ji take tamkar kar ta bar gun wannan ya sa ma bata kuma leƙawa ta dan cewa Bilkisun ta fito ba.
Kafaɗar ta Bilkisun ta taɓa "zo mu tafi" kamar jela ta bi bayan bilkisun, sai da suka fara zuwa Masallaci sukai sallah kafin su nufi wurin da zasu shiga mota.
Har ƙofar gida aka kai Hafsa in da ta sauka tana ɗagawa Bilkisu hannu kafin ta fara kwankwasa kofar gidan su, minti kaɗan Baba mai gadi ya ta so ya buɗe ganin ta ya saki washe baki "a'a Hajiya karama a dawo?" dariya ta yi "eh walllahi na dawo ya aiki?" ta tamtabaya.
"Aiki Alhamdulillah ai tun ɗazu da naga Alhaji ya dawo shi kaɗai na ce araina yau bani da abokiyar hira sai kim kai yamma,"
" ka bari kawai Baba ai Malaman nan basa kyautawa bamu san da aijin ba ɗazu aka sanya da nasan da shi ai da ban bi Abba ba duk na gaji."
"Assha sannu, Allah dai ya sawa karatun albarka," "amin" ta ce kafin ta yi gaba, gaban ta ne ya hau faɗuwa lokacin da ta ɗora idanun ta kan Momin su wadda ke saman bene tana faman watso mata harara, tasan ba komai bane fa ce dan kawai ta ga tana magana da Baba, a hankali jiki ba kwari ta nufi kofar da zata datar da kai asalin falon gidan.
Da sauri ta yi ƙoƙarin shigewa ɗaki dan karma Momin ta sassko ta mata faɗa, sai dai saurin nata bai idda ita ga shiga ɗakin ba ta ji Muryar Momin, "sannu issasshiya wato zaki iya cewa wancan mutumin kin dawo ni ban isa ki zo ki ce mun kin dawo ba?."
Ajiyar zuciya ta yi a hankali kafin ta jiyo, "No momy kawai ina san aje jakata ne sai in hauro saman," taɓe baki Momin ta yi, yanzu fisabilillahi Kalle ki, kin kyautawa mahaifin ki kenan?" kallon kanta Hafsa ta hau yi, tana son gano aibun ta gaza gano hakan yasa ta cewa Momy "mai nayi?"
"Eh kyace mai kikai zaku je makaranta inda mahaifin ki keda alfarma ace duk kayan ki ki rasa wanda zaka sa sai wannan jemammiyar rigar..?"
Dariya Hafsa ta yi "kai Momy wannan fa sabuwa ce last week na saya 17k fa" tsaki Momin ta ja, "ai walllahi lefin Abban naku ne ni ai bazan ta fi da ke a haka ba," dariya kawai Hafsa tace "shikenan Mum karki damu in zamu fita tare sai abinda kika zaɓar min zan sa but banda takalmi mai tudu."
"Ni in tafiya da ke a'a kawai kije ki bada ni cikin manyan mutane," dariya Hafsa ta yi "mai aka dafa? yunwa na ke ji" ta faɗa tana shiga ciki.
"in sai na faɗa miki zaki ci ki kwana da yunwa," Momin ta faɗa tana ƙokarin zama, Hafsan bata dena dariya ba ta nufi in da kwanunakan abin cin suke.
*******
Muktar na zaune cikin abokan sa kamar kullum bayan sun yi mangariba zuwa isha kafin ya wuce gida wayar sa ta yi ƙara alamar saƙo ya shigo, tun ɗazu yake duba wayar shiru ba kira ba saƙo wannan yasa har ya banzatar da wayar sai kuma ya ɗauko ya duba _"muna ta ya ka murnan samun aiki na koyar da Physics bisa gwajin da kazo ɗazu, zaka iya fara zuwa aiki daga gobe, gaza zuwa cikin wannan satin na nufin baka amshi aikin ba, Mun gode Hukumar Makaranta" _
Zumbur ya miƙe bayan kammala karatun saƙon Umman sa kawai ya tuna ita ya dace ta fara jin labarin nan, "ina zaka ne?, ai 8:30 batai ba" ɗaya cikin abokan sa ya faɗa cikin ɗaga murya.
Shima cikin ɗaga murya ya ce "mu haɗu gobe kawai, zan ma bayani," gudu gudu sauri- sauri yake har ya ƙarasa gida sallamar ma tare da kiran Umma ya haɗa ta, cikin sauri ta fito "kiran da yake mata yasa ta kasa amsa sallamar lafiya dai kake mun wannan kira?"
Wayar sa ya hau nuna mata kallon sa ta yi " yo banda abin Muntari ni me zan gane a waya mai ya faru?' sun ɗauke ni aikin ya faɗa cike da murna ɗo.
"Kai Alhamdulillah, Allah ya ƙarawa annabi daraja yasa a fara asa'a, ayiriri!" ta sa buɗa, daɗi ya kuma rufe Muktar a duniya yana son ganin farin cikin Innan sa, "yau she kuma zaku fara zuwa ta tambaye shi?."
"Go be in sha Allah" ya ce
"Allah ya sa muna da rai" ta faɗa
"amin Inna, bari in amso Omo gun Musa in zo in wanke kayan da zan sa gobe, gwanda in fara zuwa a mutunce," dariya ta yi "tom sai ka shigo" ya fice...
****************
"Wai dan Allah Hafsa ke wacce irin mutun ce?, kin kira mutun kince ya zo ya taimaka ya koya mana, kuma yazo kin ce yunwa kike ji" Bilkisu ta faɗa a fusace cikin faɗa fada.
Juyowa Hafsa ta yi cikin halin ko in kula "Please Hajiya dena mun ihu, kina ji fa ya ce zai je gun abokin sa ɗan level five ya jira mu ai ko addini ya bawa yunwa haƙƙin ta, in coke village ɗinne ba zaki ba ki je gun sa ku fara" ta faɗa gami da yin gaba ba tare da jiran amsar Bilkisu ba.
Ƙwafa kawai Bilkisu ta yi tare da bin bayan Hafsa rai ɓace.
Sai da suka sai lemo da cake sannan suka wuce gun ma su gurasa, Hafsa na son gurasar sosai tun randa ta fara ci shikenan kullum sai ta siya ada ƙyankyamin ta ma take anma tana jin ɗanɗanon ta ƙyankyamin ya bar ta. Suka wuce faculty of engineering ɗin dan can sukai zasu haɗu bilayi suka hau yi har Hafsa ta ɗauki wayar ta tana neman Number ɗin sata jiuryar sa na musu magana.
Shi kuwa zaune yake suna hira da Umar abokin sa lokaci-lokaci yana duba agogo sam baya son jira kawai dai dan yaran sun takura masa ne, kullum ya tuna yaddda suka haɗu sai ya yi dariya, yana zaune yana koyawa Umar Mechanics da yake carrying suka ji muryar ta, ta musu sallama," Ina wunin ku?" ta ce suka amsa da" lafiya ƙalau," ta ɗan sa hannu ta ɗauki takardar gaban su, mintina kaɗan da dubawa ta juya " lah Bilki zo kiga ya iya Physics wallahi" wadda aka kira da Bilkin ta matso "Allah Hafsa ki fita ido na bana son Bilkin nan"
Dariya Hafsa ta yi " sorry Bilkisu"
Kallon takardar Bilkisun ta yi "lah walllahi ya iya kuwa"
Ba tare da wani tunani ba, Hafsa ta ce " kawo wayar ka in sa ma Number ɗin mu dan Allah zaka dinga koya mana walllahi bamu iya ba," kasa magana ya yi ya miƙo mata wayar ta rubuta ta ce " na yi saving Suna Hafsa ita kuma Bilkisu me zan sa, dariya yasa "Bashir zaki sa but ni bance zan koya muku ba gaskiya."
"Dan Allah ka taimaka" ta ce
"Oktom ba yanzu ba kumin message ɗim sanda kuke da free time zan duba tamu time table in"
"To mun gode"kawai Hafsa ta ce taja Bilkisu sukai gaba suka bar Umar da Bashir da mamaki.
Umar ne ya taɓo Bashir wanda ke ta murmushi bayan tuna yadda suka haɗu "waɗancan ba yaran da kake jira bane?'" ta taga Bashir ya leƙo kun gann nan wayar ya Hafsa ta mayar suka haura saman.