Sashe 38
Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Narai narai ya yi da ido, ya miƙe jiki ba kwari ya yi bakin ƙofa, tausayin yaron ne ya kamata ko mai ta tuna cikin sanyin murya tace "Abdallah " juyowa ya yi fuskar nan ta yi abin tausayi, buɗe abincin ta yi tare da ɗiba ta kai baki " ka gani zanci, ko banci da yawa ba, karka damu kaji" gyaɗa kai ya yi tace " yawwa to maza kane kuci naku"
Falon ya wuce yadda yaga aiman yayi jigum yasan da wani abu duban yaron ya yi " Aiman menene mai yasa baka cin abincin?"
Narai narai Aiman ya yi da idanu cikin muryar ɓacin rai irin ta yara yace "ba Mun bace ta zageni, kuma ba abinda na mata" shiru Abdallah ya yi kafin ya ce " bakai ta zaga ba, ranta ne a ɓace" murmushi Aiman ya yi " Au" sai kuma yasa dariya ya koma cin abincin sa.
*******
Zaune Bilkisu take ta rafka uban tagumi, tun ɗazu baccin ya kasa ɗaukan ta, ranta a cinkushe yaje, haushi da takaicin maza duk ya cika ta, kallon Tariq da ke kwance gefen ta yana bacci ta yi, ta kuma jin wani ƙululun takaici, haannu da yakai gefen ta yaji alamun bata nan ya sa shi miƙewa.
"Habibty lafiya mai ke damun ki?" Ya faɗa a rikice lokacin da ya tashi zaune a rikice banza ta masa tare da hararsa , rikicewa ya kuma tare da jawo ta jikin sa "haba habibty, mai na miki?, koma mene dan Allah kiyi haƙuri ki faɗa mun wallahi ba da sani nayi ba, kinji tawan" takaici ne ya kuma rife ta lokacin da ranta ke faɗa mata yanzu fa duk wannan abin zai iya mata abinda Muktar yama Hafsa.
A hankali ya matso ya kuma sata jikin sa, dan Allah Allah tawan kiyi haƙuri, kinji karki sa zuciyata yanzu ta buga, kinsan ko yaya damuwar ki take tawa nunkuwa take, abin mata da miji sai kuma jikin ta yayi sanyi duk taji tausayin mijin nata ya kama ta, murumushi ta yi " No bakai bane kawai raina ne ba daɗi" kamo hannun ta ya yi tare da yin ajiyar zuciya, na ɗauka nine though damuwar ki ko bani bane sila matsala ce tashi muyi salla ki faɗawa Allah ko mainene mu roƙeshi ya sauƙaƙa," numfashi mai nauyi ta aje haka ne komai girman matsala akwai Allah sam ɓacin rai yaso yasa ta manta da hakan.
A hankali suka sauko daga gadon zuwa toilet sukayo alwala tare da dawowa falon, shine ya shinfiɗa musu sallayar ya ɗauko mata hijabin ta a inda take ajewa ta sanya, cikin sujjadar ta roƙom ta shine Allah ya sauƙaƙawa aminiyar tata, ya ganar da Muktar ya mayar da ita, in ba mai ganewa bane kuma Allah ya cire ma Hafsa son sa.
Koda suka idar ma duka Addu'oin da a dai ɗaya ne, nemawa Hafsa Mafita. A wurin bacci ya ɗauketa Tariq ya shafa addu'a tare da zare mata hijabin ya ninke, a hankali ta ɗauki filo ya ɗaga kanta ya aje mata.
Ɗakin yaran su ya leƙa kamar yadda ɗabi'ar sa take indai ya farka sai ya duba su, ganin suna lafiya ya dawo bed room ɗin su gefen Bilkisu yaja ya kwanta.
Washe gari bayan ya dawo daga masallaci ya tarar ta yi sallah ta koma bacci murmushi ya yi tare da gyara mata zanin rufar sanyin asuba da ke ɗan kaɗawa yasa ya kuma rage air conditioner ɗin ɗakin kafin ya yi waje kai tsaye kitchen ya wuce ya hau tiri tirin haɗa musu abincin kari, walida Babbar ɗiyar su ce ta shigo, "Good morning Dad" murmushi ya yi " Good morning sweetheart"
Matsowa ta yi " Dad kaje ka taso Ummi, zan ƙarasa" murmushi ya yi " kun gana Tilawar ne?"
Gyaɗa kai ta yi " eh mun gama harma Jawahir ta koma bacci"
"Yayi kyau kema kije ki huta, nama gama ai" ya faɗa yana juye kwan dake cikin kwano cikin kaskon suya, murmushi kawai yarinyar ta yi ta fice daga kitchen ɗin.
Ganin yana fito da kayan yasa yaran zuwa suka amsa, miƙa musu yayi tare da yin bed room din su, tana kwance tana baccin ta alamun jiya bawani isasshen bacci ta yi ba, har ya sunkuya zai tashe ta sai kuma ya fasa sabida tunanin da yazo ransa na kar kanta ya yi ciwo, juyawa kawai ya yi ya koma falon.
Walida ce ta yi serving ɗin su, suna ci suna hira sai dariya suke yadda yake hira da su tamkar da wasu sa'oin sa yake, sun kusa gamawa ta fito hangar su da ta yi, da kuma ƙarasowa kusa yasa taɗan tsuke fuska tare da faɗin " eyye abinma ƴar son kai ce da wariya, wato kaida taran ka in kun ƙoshi ni ko oho ko"
Dariya ya yi tare da miƙewa yayo inda take " Habadai mu mun isa mu ce haka in kina so yanzu sai adawo da cin abincin farko, ai girmam ki ne" dariya ta yi " ah to gaskiya adawo da shi in ana so in yadda"
Jawahir ce ta miƙe tare da jan kujerar da Bilkisun ke zama " Hajiya Ummi ta fito cin abinci zai dawo farko," ta faɗa tare da yin alamun Bilkisun ta zauna, suka sa dariya duka.
*********
Yauma kamar kullum tun tafiyar Hafsa gidan ya zame masa tamkar kufai, rasa mai yake masa daɗi yayi, tayin da daren ya zame masa tamkar awanni dubu, sam bacci ya gaza ɗaukan idanun sa yayin da jiri da rashin karfin jiki yasa shi kasa yin sallar da ya yi niyar yi, a zaune ya yi nafilar rasa ma mai zai roƙa yayi, sassauci kan son Hafsa ko kuma sassauci bisa damuwar da ke damun sa, samun kansa ya yi da roƙawa Hafsan Haƙuri da juriya bisa rashin sa.
Bayan ya dawo daga Masallaci ya yi sa'a bacci mai nauyi ya ɗauke shi bai farka ba sai wurin goma, wanka ya shiga bayan ya fito ne ya haɗa ruwan zafi wanda yaji madara ko bread bai haɗa da shi ba ya kurɓe, kasancewar cikin sa ya naɗe yasa yana gama sha amar ya tawo masa, ya yi toilet da gudu.
Sai da ya wanke bakin sa sannan ya dawo ya yaɗa black tea ya sha kaɗan, can doguwar kujera ya koma ya kwanta, gizon da hayaniyar yaransu da kuma Hafsa a jikin sa ke masa yasa ya miƙe, dinning ya nufa ya ɗauki makullin motarsa tare da barin gidan.
Kamar wada tunanin sa ya guje, kawai ganin sa ya yi a ƙofar gidan su Hafsan yana horn, mai gadi da ya buɗe yagan shi ne ya washe baki "aa Alhaji Muktar kaine" wannan da mai gadi ya faɗa ne ya dawo da shi hayyacin sa a nutse suka gaisa kafin yace "Please kayi haƙuri na fasa shiga I will come back later" ya faɗa yana ƙoƙarin juya motar Mai gadi kawai ya bishi da ido cike da mamaki, shidai Muktar ɗin da ya sani baya shaye shaye bare yace wani abin yasha ya kasa gane ina zashi, taɓe baki yayi tare da gyaɗa kai lafin ya mayar da ƙofar ya rufe.
Jan motar Muktar ya yi da gudu ya bar wurin sai da ya yi nisa sannan ya faka bakin titi tare da dukan goshin sa.....
********”
Soyayyar Mukhtar a jinin ta take, a zuciyarta take. Duk yadda taso ta yakice son shi daga ranta ta kasa, dena kuka abun ya gagareta. Cike take da haushinsa amma duk da haka zuciyarta da shi take bugawa a ko wanne sakan da yake wucewa. Nisawa tayi tana sosa idanunta wanda yanzu sun gaji sun bushe. Ta kalli agogo taga biyun dare. Mikewa kawai tayi ta tafi daura alwala. Ko da ta dawo tayi raka'a biyu sai ta janyo wayarta ta buɗo messages dinsu da Mukhtar ta soma karantawa cike da kewar sa da ciwon rai.
Ke zan zaba a ko da yaushe. In an bani zaɓi tsakanin kaina da yaran mu da ke. Baki da mahadi a waje na.
Ta karanta message dinsu na karshe. Sakon ya bakanta mata rai, ya sosa mata zuciya. Ta rasa abun yi don hawayenta sun kare. Ko sati ba'ayi ba ya tura mata wannan. Ashe dama shima makaryaci ne kamar sauran maza? Duk tsahon rayuwarta dashi ta yarda da cewa shi din ya fita daban da kowa ashe duk kanwar ja ce.
Zuciyarta ta cigaba da harbawa cikin tsananin haushin kalaman nasa kamar a lokacin ya fade su.
Ta fara typing.
"Na tsane ka Mukhtar, makaryaci kawai."
Har zata tura sai ta goge. Shiru tayi ta ajiye wayar kafin ta sake ɗauka ta budo chat board dinsu again.
"Ko babu igiyar auren ka a kaina, ina kaunar ka. Ko ka tsane ni, bazan dena sonka ba, ƙaunar ka ta riga ta zame mun jini da tsoka."
Ta jima tana kallon message din da ta tura masa kafin barawon bacci ya sace ta.
****
Zaune yake yana juya shayin da ya hada wanda har ya huce bai fara sha ba. Babu abunda yake masa daɗi a zuciya da duniyar ma baki daya. Hafsah itace farin cikin rayuwarsa kuma da kansa ba tare da zugar kowa ba ya datse farin cikinsa. Har yanzu ya rasa inda zai dafa. Ji take gaba daya purpose dinsa a rayuwa ya gushe. Dama Hafsah ce alkiblar dukkan wani abu da ya shafe shi. Itace sila da dalilin komai. Sai dai yanzu da ya yanke alakarsu, bashi da wata madafa. Bashi da wani direction. In yaje aiki ya dawo sai ya rasa abunyi.
Sosai yake cike da kewarta amma in ya tuna dalilin da ya sanya shi yanke hukuncin nan tsakanin su sai yaji ba zai iya chanja ra'ayi ba, abu ɗaya ke ƙara ƙarfafa masa zuciya shine *ko da so* a zukata biyu dan ba'a tare ba'a fasa rayuwa, ya yadda Hafsa da shi a sannu a hankali zasu gudanar da rayuwar su tamkar ɗayan bai taɓa shiga rayuwar ɗayan ba. Rashin ta ba karamin horo bane a gareshi amma duk da haka ya zabi ya jure. Ba zai iya janye kalaman sa ba.