← Book details Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 43

Sashe 1

Ko Da So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da so..

Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau

Bismillahir rahmanir raheem.

Idon ta cike da hawaye take kallon sa, fuskar ta ɗauke da mamaki gami da tsoron yadda lokaci guda ya birkice kamar ba masoyin ta abin alfaharinta ba.

Anya shi dinne kuwa?

Hannu tasa ta goge hawayen da ke famar zarya a kuncin ta, don tafi ganinsa da kyau, duk da tasan gogen su bawai shi zai sa zafafan hawayen nata su tsaya ba.

Warware manyan idanunwanta akan sa.

Shi dinne dai, Mukhtar. Mukhtar dinta. Mijinta, uban yayanta. Sanye yake da farar shadda kamar ko wacce ranar juma’a. Farin kaya ba karamin ƙara masa kwarjini da kyau da haiba yake ba.

Ta sake goge wasu hawayen dake zuba daga kwarmin idonta ta kalle shi.

“Kar kayi mana haka Abban Abdallah… dan Allah…” ta faɗa cikin karaya. Bata san me zata ce masa ba amma abunda yake bukata daga gareta yafi girman tunaninta. Ba zata iya ba.Shima yafi kowa sani.

Kamar ba zaice komai, kamar yanayin nata ya bashi tausayi sai dai ɗan guntun tunanin da ya yi yasa shi kauda kai daga kallon, saitin da ya juya ta matsa ta ko yi nasarar jefa kwayar idanun ta cikin nasa.

Ta sa ni Muktar ɗin ta na son ta domin tana iya ganin zallar tausayin ta gami da madarar son ta a idanun sa, ta sani soyayyar Muktar gare ta bata gushewa a zuciyar sa. Takan gane haka ne a Idaniyar sa da basa taɓa iya boye zallar ƙaunar ta, duk kuwa da tsananin bacin ran da yake ciki. Take taji hawayen idonta sun fara ƙafewa, saboda wani hope da taji ya ziyarci zuciyar ta.

Karkarwar da take yi tuni ta tsaya, hawayen ma kamar an ce su tsaya. Cike da kwarin gwiwa ta matsa kusa dashi, murmushin kwarin gwiwa tuni ya mamaye fuskar ta, kallon sa take tana neman irin nata murmushin a fuskarsa. A hankali ta kamo hannun sa tana tsara mai zata ce a ranta da zai sa ya sauko daga fushin nan, sai dai yadda ya juyo a fusace ya sata sakin sa da sauri kamar wadda ta taɓa wuta.

Cikin daƙiƙu idanunsa suka gauraye jajir kamar garwashi cikin kausasasshiyar murya mara amo yafara magana wadda inda ace Hafsa tasan abinda zai furta kenan da tuni ta toshe masa baki tahau magiyar kar ya furta.

“Na sake ki Hafsa. Na sake ki saki daya. Ki bar mun gida yanzun nan…”

Kalmomin da bata taɓa koda da wasa tsanmanin jin su daga bakin Muktar ba, kallmomin da suka saka dukkan wata gaba jikinta ta sage. Kalaman da ta jisu tamkar saukar dalma a zuciyarta.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un… Muktar ka sake ni fa kace?” Sam sam idaniyar ta sun dena gane komai yayin da ɗakin ya hau juyawa da ita tamkar fanka.

Yaraf ta zube a gurin, a ruɗe ya yi kanta yana Faɗin, “Ummu Abdallah...”

Yadda ya yi maganar yasa yaran su da basu san mai ke wakana ba suka yo falon da sauri, kamar wata ƙaramar ɗiyar sa haka ya ɗauke ta ya yi waje yaran suka bi shi yuuu...

A karo na farko kenan a rayuwarsu. Tun tasowar su da suka taɓa ganin Mamin ta su a irin wannan yanayin. Tuni jikin su yayi mugun sanyi. Mami mace ce mai kuzari gami da jarumtar ɓoye ciyo, duk runtsi tana daurewa ta farantawa yaranta sun shaƙu da ita ita ce koman su, kamar yadda suke koman ta. Ko kadan basu san menene rashinta ba a rayuwar su. Ko wannen su yana samun lokaci daga gareta dai-dai gwargwado. Wasu lokutan in suna hira takan ce musu su zama masu dogaro da kansu domin wataran zasu tashi babu ita a duniyar ma gaba daya.

Sai gashi yau rashin lafiya ta kwantar da ita ji suke tamkar duniyar ta tsaya musu. Ko da yake a wajensu duniyar ce ta tsaya domin Mami ita ce rayuwar su.

Tun jiya kawo ta ba wani bacci suka samu ba, Aiman ɗan ƙaramin cikin su ne ke ta faman zarya lokaci lokaci yana leƙa ƙofa da alamu mahaifin su yake tsanmanin gani wanda tun jiya da ya zo ya tabbatar an kwantar da ita bai dawo ba. Jiƙin yayan sa matsa, Yaya wai Yaushe Abie zai dawo.

Abdullahi ɗan kimanin shekaru goma sha biyu da kana kallon sa kasan idanuwan sa basu samu runtsawa ba, wanda har kuka sai da yayi. Shine dan ta na biyu kuma yafi kowa jinta a zuciyarsa kamar yadda uwar take dukkan kokarin ta ita ma ta boye yadda take jin sa daban a cikin yaranta. Ya dubi ƙanin nasa a hankali ya ce anjima kaɗan sam yaron bai cika som magana ba, bare yanzu ga tashin hankalin Umman su.

Juyawa Aiman ya yi ya cigaba da zaryar sa tamkar wani banban mutun, haka duk yaran Hafsa suke a nutse domin ita ɗim jajir tacciya ce wurin ganin yaran ta sun taso abin kwatance.

Kallonta suke yi dukkan su, alokacin da numfashin ta ke sama da kasa. Bacci take yi amma a baccin ma mutum in ya nutsu zaiga yadda take fusga da firgita kadan kadan. Sosai suka kura mata ido dukkan su suna jira suga kawai ta tashi.

Aiman ne ya matsa kusa da Babban wan su Faruk “Yaya wai Mami yau she zata tashi ne? Ni yunwa nake ji.” Ya faɗa yana tura baki. Kursum dake kusa dashi ta kwadeshi. Da gani itace a saman sa.

“Kai dallah malam waye yake ta abinci? baka ga Mami a kwance ba, Silly boy kawai.” Tayi tsaki tana sake mayar da taguminta kamar dazu.

Babban yana ta kallonsu bai ce komai ba kuma sai aka yi sa’a karamin baiyi kuka ba.

Suna zaune sunyi jugum jugum baban nasu ya fado dakin da gudu Aiman ya faɗa jikin sa, yawwa Abie tun jiya nake jira kazo ka tashi Mami. Kallo daya babban ya ma su yana shafa kan Aiman sannan ya dauke kan sa.

Tsai Abdallah yake kallon mahaifin na su babu wanda ya faɗa masa kuma babu ma alama a tattare da mahaifin nasu amma yasan shine silar kwanciyar mami. An yi kwana biyu yana lura da irin yadda suke mu’amala kamar makiyan junan su.

“Ya me jikin?” Abie ya sake tambaya bayan sun gaishe shi amma sai aka rasa wanda zai bashi amsa kamar sun haɗa baki gaba ɗaya.

“Mami will be fine. Kuzo in kai ku gida ku shirya ku yafi islamiyya…” ya faɗi yana so su tafi don baya son ta farfaɗo akan idansu domin bai san yadda zaiyi ba.

Kamar wanda ya faɗi wani abun tashin hankali Abdallah ya zuba masa ido kafin ya maida kallonsa zuwa ga Mamin yace, “hutu mukeyi ai Abba ka manta kuma in mun tafi waye zai zauna gun…” bai ƙarasa ba yaga kamar hannunta yana motsi. Ba shiri ya bar maganar tasa ya miƙe yayi kanta. Dukkan yaran suka mata rumfa suna kallon yadda take motsa yatsun ta a hankali gami da ƙoƙarin buɗe idanun ta.

A nata bangaren kuwa ji take kamar an ɗora mata dutsen Dala a kanta. Wani irin nauyi da ciwo ya mamaye gaba daya jikinta. A sannu a hankali take binsu da idanuwa.

Kamar a tare suka fara jero mata sannu sai dai babu wanda ta tanka.

“Alhamdulillah.” Mukhtar ɗin ya furta ganin ta farka, da dan damuwa a muryarsa sannan ya matsa kusa da ita. Daidai sanda idonta ya kama nasa, sannan ta fara zubar kwalla. Kamar wasa sai hawayen ɓakin ciki ya fara zirya akan kumatun ta.

“Mami, jikin ki ciwo?” Dan Aiman ya tambaya, su kuwa manyan sun ma rasa me zasuyi. Ba ma zasu iya tambayar ta mene matsalar ba musamman yadda suka ga ta kafe mahaifin su da ido.

“Mami please ki mana magana…”

“Mami sannu kinji, a kira miki doctor?”

“Mami sannu, dan Allah ki daina hawaye, yana min ciwo…”

Haka muryoyin yaran nata suke tashi a cikin ɗakin amma kamar ba da ita suke ba. Shi take so yayi magana. Har yanzu tana da kwarin gwiwa akan makomar su. Har yanzu tana son shi. Har yanzu shi din, shine farin cikinta. Kalamai uku kawai take so taji daga gare shi.

“Na maida ki.” Shi yasa ta zuba masa idanuwanta ba tare da kula da cewa yaran suna sane da su ba.

Sai dai Mukhtar ma ba tare da la’akari da yaran ba kawai ya juya ya fice daga dakin sam ci gaba da kallon masoyiyar tasa a haka zai iya sawa ya canja hukuncin da ya yanke, hukuncin da sam baya fatan janyewa.

Ko sannu bai ce mun ba.

Ko murmushin nan nasa kai sani farin ciki bai min ba, anya ba mafarki nake ba?

Hawayen da suka fi na ɗazu zafi suka ziraro zuwa kuncin ta lokacin da ta ɗora idanun ta bisa kofar da ya ja ya rufe.

A hankali ta rufe idanuwanta. Daga nesa nesa take jin yaran suna rokarta ta tashi sai dai tayi nisa daga duniyar da take yanzu. So take ta koma duniyar soyyayar su da Mukhtar don taga a ina ne ta kuskure. Ta san ko wanne labari yana da tushe, ko wanne labari yana da asali. Yana da mafari…

Nasu Mafarin ya fara ne a birnin Kano dake Najeriya.

****

Dala, Kano.

Sauri yake ya kammala cin tuwon dake gaban sa duk da yaji daɗin dumamen sosai zai so ace a hankali zai cinye shi sai dai baya so ya makara.

Daga gefe kuwa Inna ce ta ke ta faman jan ruwa daga rijiyar dake tsakar gidan tana cika bokitan dake gefenta. Mace ce ba zata haura shekara hamsin da biyar ba. Yar karamar mace ba tsawo babu kiba a tattare da ita. Fuskarta doguwa ce, hancinta madaidaici ne, leben ta ma mai tudu ne baka ce wuluk sai dai kaf yaranta babu wanda yayi bakinta. Gaba ɗaya su hasken mai gidanta suka ɗauko, farin bafulatani, Malam Adamu Mujeili. Duk da a Kano ya tashi amma yan asalin Yola ne. A nan Kanon suka hadu sukayi aure har suka haifi yara shida kafin Allah yayi masa rasuwa.
Chapter 1 · 0% Book details